EPISODE_2

108 11 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣2⃣*

Atif tafe yake cikin jerin dogayen bishiyoyin nan,yayinda yake waige waige alamar baigane inda suka nufaba kuma babu alamar takun kafafunsu ta ko'ina,nan saiya fara kokonto anya bashi bane yabi sababbiyar hanya......amma duk da haka bai koma bayaba duk da wasiwasin dayake haka yayi ta tsusa kai cikin dajin.

Al'amarin su mu'azz ko tafiye suke cikin nishadi yayinda suke dauke dauken pics(hoto) na duk abinda ya burgesu a wannan guri...
Haka sumadai sukayi ta tafiya mai nisa,yayinda suka kuma manta da abinda suka bari a baya wato mota da kuma dalilinsu na tsayuwa anan guri.

Cikin wannan tafiyar da suke dai,suka ci karo da wata hanya mai matukar burkewa yayinda aka kayatar da hanyan da furanni iri daban daban,sa'annan aka jera wasu kananun duwasu masu launin pink da blue. Abin donin ban sa'awa Kai hatta iskar dake kadawa a wannan gurin ta dabance haka suka shige wannan hanya suka fara taku kowannin su zuciyar sa cike fal da burin ganin inda wannan hanya zata kaisu.......
*[Hmm Masu iyya magana kance kaddara takan riga fata,dako sunsan bala'in da suke tunkara da kuwa sunyi gaggawar yiwa kansu fatar mutuwa domin tafi sauki.]*

Tafiye suke yayinda suka daga kawunan su sama suna ta kalle kalle kai kace dan kauye a *London*

"Wow gaskiya duniya na dauke da abubuwan mamaki iri daban daban....."
Haka Mufyda ta furta cikin muryar mamaki,inda samra tace da ita

"Gaskiya ni tausayawa Atif nake wallahi,gaskiya yayi mummunar choices,danko yayi missing na wannan nishadi"
Fashewa sukayi da dariya bayan ta furta hakan...
Wannan firar da suke sun kasance suna yintane yayinda suke wannan tafiya.

"Wow" Haka Samra ta furta yayinda ta hango wata kyakkyawar bishiya mai launin golden color,kai kace ko da ruwan gold din aka halince ta,danko itatuwan wannan bishiyar launin gold ne,furannin tako fararene gayayenta ko kore......cikin sauri ta karasa hade da ciro wayarta ta soma dauka da hoto..sauran abokan tafiyan natako cen ta barosu a baya danko, hango bishiyar da tayi ta ruga izuwa ga wannan bishiyar,haka dai tayi ta daukar hoton wannan bishiyar. Bayan ta dakata dayin haka sai taga jikin bishiyar na tsastsagewa abin mamakin data gani kuwa shine wannan tsagewar da bishiyar keyi wasu harrufan rubutune ke bayyan ajiki....

Itako ta Kame guri guda ko motsi bata iyayi,sa'annan ta wani zura idanu har saida taga karshen rubutun... Abinda aka rubuta jikin wannan bishiyar ko shine.

      *This is a warning*
Karku kuskura kushiga wannan hanyar idan har kunason kanku da arziki.....

Sai kuma alamar kan korangwal☠️☠️☠️dake nuna had'arin gurin.


Bayan ta karanci hakar sai jini ta soma kwararowa ta jikin rubutun a hankali yadda hawaye ke zubowa a fuskar d'an adam.

"Samra........ Samra.... Samra!!"
Haka mu'azz ya furta har sau uku kafin ya dan duki kafadarta....
Firgicewa tayi hade da juyawa cikin sauri tayi ido hudu da mu'azz,tsaye bayanta

KOFAR AJALI 2021On viuen les histories. Descobreix ara