EPISODE_5

82 11 0
                                    

💀💀💀
*KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣5⃣*

Rike *Ahmad* yake da Hannun forzy,yayinda suke sheka gudu na fitar hankali.
Bayansu kuma wayannan halittu masu kama da kadangarune ke biye dasu,wayannan Halittun kuwa sunyi matukar kusanci dasu, danko acikin idan da wani yayi missing step to fa sai wanin shi Bade shi ba,danko Loma daya zasuyi dashi.

Cikin wannan Yanayin suka kasance Nayen wasu dakiku,Har saida suka kaiga Mabilla kamar yadda su Harun suma suka sami tasu mabillar.

Kofa suka hango daga cen nesa babu Bata lokaci suka dad'a himma sai da suka tsinci kansu cikin wannan daki kafin suka taka biriki,ta sanadiyar sun kai bangon karshe na wannan daki.

Abin Da yayi matukar Dagula lissafin Forzy tare da Ahmad ko shine,a guje suka shigo wannan daki yayinda tsoro ta hanasu tsayawa surufe wannan kofa bayan sun shige cikin. amma kuma sai suka tsinci kansu a wani faffadar guri kuma babu abinda ya kasance a bayansu yayinda suka kai bangon wannan daki.

Cikin mamaki suka Dubi juna yayinda zuciyoyin su ke cike da tambayoyi amma babu wanda ya furta hakan ga d'an uwansa dan kuwa ko sunyi babu mai ansawa a cikinsu.

*Al'amarin* Wannan aljana kuwa tafe take cikin duhu,yayinda take wannan tafiyar ko sai tajiyo sautin takun kafan mutum ya wuce ta bayanta cikin sauri.. Sa'anan kuma a razane ta waige baya..
Amma meye kuwa kuke Tunanin zata tarar abayan nata?

meye kuwa zata gani daya wuce empty place sai kuma shiru da gurin yakeda ga kuma dan karen duhu......

Batare datace komi ba ta jujjuya idanu zuwa kowani lungu da sako amma still babu wanda ke wannan guri.....
Ajiyar zuci tayi sa'annan ta waiga da niyar tafiya,amma kuwa koda taku guda batayi ba, ta sake jiyo wannan sauti a karo na biyu,amma kuma wannan karan akwai dan banbanci,dankuwa hade da dariya cikin siririyar murya tajiyo....muryar kaman na karamin yaro ko kuma yarinya.

Cikin sauri ta sake waigawa ta karewa wannan guri kallo ba tare data ga komi ba,hakanne ya sake tunzura ta,ta juyawa ta kuma soma tafiya cikin sauri but sai tasake jiyo hakan wanda wannan karon harji tayi karamin yaro ya ta'ba mata kayan jikin ta.

"Da wani anan gurine?"
Abinda wannan yarinya ta furta kenan,jin babu ansan data samu ne yasa tajuya.... kwarma bagidajiyar ihu tayi dan kuwa ba karamar razana tayi ba.

Abinda ya tsoratar da itan ko shine juyawar da zatayi sai wutan dace wannan guri suka kunna kansu yayi da suka bada wani sautin a yayin kunnuwar mai razana mutum wani *buUuu* yadda kasan Tukunyar gas ce ta kama da uta.

*TIRKASHI WAI ALJANI DA TSORON DUHU*

Aiko bata sake 'bata lokaci anan gurin ba,cikin sauri ta kara gaba....
Cikin wannan siririyar hanya mai kama da cikin kogon dutse take wannan tafiya....

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now