EPISODE_8

63 8 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣8️⃣*

Tsastsaye suke sun rasa tayi.....
Mufyda ko tuni ta kigice Tana ta rawar jiki.....hade kuma da waige waige  ta hakan ne ta hango musu wani Bala'in na daban.....Meye wannan Kuma??
*Kunamu* Tagan su Zagaye dasu ta ko'ina ma'ana sunyi musu zobe....kuma ko wacce daya daga Cikin kunamun Girman ta takai Girman Akuya..... 🦂🦂
Cikin zafin Nama suka yiyo kansu Ganin Haka Yasa Duk suka Rikice, *Atif da Mu'azz* ko suka kalli idanun juna,kamar hadin baki sukayi tsalle suka dira da kafafun su Kan Wannan shunfudeddiyar kankarar da suke.. nan da nan suka tsunduma Cikin wannan makeken Rijiya......Ta sanadiyar tsastsagewa da wannan Kankara tayi,Ihu suke Ahhhh!! Yayinda suke fadawa cikin wannan Guri,A tunanin Atif da Mu'azz ko yin hakan zaisa Kunamun su koma inda suka fito but hakan Kara musu hazaka tayi Domin Kara sauri sukayi suna Kuma shiga Rijiyar yadda kasan taron kud'an Zuma.

▪️▪️▪️▪️▪️

"Gaskiya Nayi matukar mamaki, Domin banyi Zaton zanga hakan da idanuna ba.....Gaskiya Nayi mamaki sosai da sosai"

*Reply*

"Ah kina nufin bakya Jin tsoro na??,Nifa Gaskiya Jikina bai dauka ba"...

"Hmm Maizai saka naji Tsoron ki,Aiko Babu Abin tsoro a tattare dake Noor"

Haka Forzy ke jiyo Wannan Tattaunawa Nasu Nina Yayinda ta kasance kwance take gefe duga suko zaune Guri daya wato Nina da Noor....sun Kuma kasance sun Bawa Forzyn Baya.
Haka *Forzy* ta tashi Cikin Sand'a ta Dauki jakar ta ba tare da sun sani ba ta Ruga A Guje,Nina Da Aljanan Nan Kuwa Ko iyya juyo sawun Kafrnta Basu yiba har ta bar gurin..

Cikin Sauri hade da kuma Gudu Forzy ke Tafiya yadda kasan biyo ta akayi baya,Tana Wannan Sauri hade da Nishi Yayinda Take tunkarar Kofar wannan Daki data kasance a ciki Wanda a Halin Yanzu Bata wuci Taku Talatin Bane kacel tsakanin ta da Kofar....

Tuni Takai ga wannan kofa tasa hannu da Karfin tsiya ta bude....shiga ciki tayi sa'annan ta mayar da Kofar ta Rufe.

Al'amarin Nina da wannan Aljanar ko Fira Tayi Fira suka Soma Sako Forzy Ciki inda Nina Tace Da ita..... "Kawa tace ita,Kuma Ina......"
Bata karashe maganar nata ba ta sanadiyar ta juyo da niyar nuna inda Forzy ke kwance Amma Sai ta tarar da gurin Babu kowa...
Cikin mamaki ta Furta cewar "Ina Kuma Gangar Jikin Forzyn Ta shiga"...

Aljanan ko Tayi saurin cewa da ita "what are you talking about" Amma Bayan tayi Arba da shunfudar Forzy sai Ta cika da mamaki ta Kuma kasa cewa komi....

Nina kuwa ta ce da ita......

"Anan Take Kwance fa,Amma Ina ta shige"

"Kodai maiya dauke ta ba,Ina ko zataje Bayan Tuntuni anan take kwance Kuna ma a tsorace"
Cewar Aljanan Kenan wacce Nina keyi Mata lakani da *Noor*

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now