EPISODE 10

51 5 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 1️⃣0️⃣*
*THE DEATH*

Ihun Aljana Noor ce ta ratsa cikin wannan katafaren ginin inda karan ta ratsa ko'ina a fadin gurin ta Kuma kaiga riske *Forzy*, a firgice ta take biriki bayan ta duba ko'ina batare da taga komiba sai ta soma sauri danta hango wata hanya wacce take kyautata zaton Mai billewace.....

Cikin sauri ta Soma tafiya tana kokarin kaiwa ga kofar,Amma Kuma sai ta Soma jiyo wata murya Mai kama da nata sak nayi mata dariya..abaya,Aikuwa cikin razana ta juyo inda ta tarar da bayan nata Babu alamar kowa,nanfa kirjinta ya soma bugun uku uku...ta Kuma soma magana a kasar zuciyar ta.

"Shin kodai kunnuwa na ba daidai suka jiyo bane....? Kamar naji anayimin dariya"
Aiko Bata kammala fadar haka ba taji tafin hannun mutane sunkai goma a kan kafadar ta....

*#Samrah*

"Hakan bazai taba yuwa ba,bazamu sake barin Nina abaya ba..."
Haka tayi ta furtawa yayinda Atif da sauran mutanen ke kokarin shawo kanta Amma daga karshe ta kwace kanta daga hannun su ta ruga tana Mai dotsawa izuwa wannan Ramin daya fashe aikuwa sai daya saura taku talatin ta kaiga Ramin kawai sai taga wannan macijiya Mai girman bishiyar dafino ta billo ta wannan Rami....

Bayan tayi ido hudu da wannan macijiya ko tayi furucin "Oh no" cikin siririyar murya.

Aikuwa macijiyar batayi Wasa da damar taba,dankuwa ta wani shure ta kaikace Shirin film....
Haka ta tashi sama kamar kwad'o Kuma Babu abunda ya tokare ta illa kofan ga dake bayansu domin kuwa sun bawa kofar baya....

Aiko Sumewa #Samrah tayi Atif, mu'azz da sauran mutanen suko zura idanu sukayi Dan mamaki...

Macijiyar ko ta Soma wani jujjuyawa cikin salo Mai matukar tsoratar tana ta bubbude wuya kamar wata jegariya nanfa ta kurama taron nasu ido....
Can tayi kansu sulululu ta yadda idan ta kaiga su wub daya zatayi musu ta hadesu Dan kuwa a tsaye suke guri guda sunki motsawa sai ihun tsiya da suke....

Kamar walkiya sai ga wani santalelen saurayi ya diro gaban wannan macijiyar, saurayi Mai cikar Kamala da Kuma kwar jini,ga faffadar kirji irin ta jaruman kwarai.

Bayyanarsa a wannan guri yayi daidai da budewar bakin macijiyar da niyar hade taron su Atif... Amma Allah bai Bata damar haka ba ta sanadiyar bayyanar wannan saurayi,kabbara yayi hade da dafe saman kan wannan macijiya aiko cikin kankanin lokaci ta koma baya da karfin tsiya Danko karfin kabbaran yafi karfin ta ba kusa ba.

Zuru zuru mu'azz,Atif da sauran mutanen gurin sukayi domin kuwa abin yayi matukar Basu mamaki,ko kibta ido basuyi...
Wannan saurayin ko tsaye yake yayin da wannan macijiyar ke kururuwa tana komawa baya.... Fadiwa kasa wannan macijiyar tayi cikin sauri da Kuma zafin nama ta Mike hade da yunkurin sake farmakar su...

Aiko wannan saurayin bai Bata damar yin haka ba Dan kuwa soma karanta *Suratul Jin* yayi bayan ya karanta Aya goma na wannan Sura sai wannan macijiyar ta Soma ihu cikin kankanin lokaci ta rikide ta dawo Suffan mutum... Atif da mabiyansa ko mamaki takai makura domin kuwa sun rasa ta cewa sai kallon ikon Allah.

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now