EPISODE 11

47 5 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 1️⃣1️⃣*
*THE CONFUSION*

#Tina da Mufydah ko suka hadakai guri guda cikin rad'a Tina tace da mufy..
"Ko meye dalilinsa nayin hakane oho"

Atif,mu'azz duk sunyi sanyi da sukajiyo wannan magana ta Samra....

*"Meye Al-Hussien ke Shirin boyewa gaskiya da lauje cikin nad'i,"*
Haka Atif ya furta cikin kasar zuciyar sa.....

Zuciyoyinsu Bugun uku uku take yayinda suka kasance a Ankare domin kuwa saura kiris wannan Garkuwa ta Rezar wuta ta kafe.
yadda suka kasance a ankaren hakama Scopions din suka kasance... Domin kuwa har sun soma matsowa wajen garkuwar.

Aiko daukewar wannan Garkuwa ta Rezar wuta tazo daidai da Tsinkewar wata siririyar murya Mai fasa dokin kunne...
Wannan Kara na bada sautin "Aaaaaaaaaaaaaaaaaaa!!" Cikin firgici da naiman kare kunnuwa su daga fashewar yasa suka toshe da hannayensu biyu..
Wannan Kara dai ya dauki lokaci kafin ya tsaya,bayan tsayawarta sai suka tsinci kansu cikin wani yanayi Mai wuyar sha'ani.

Kallon Abubuwa uku uku suke ta sanadiyar mugun jiri data kamasu dukka,ga kuma rashin jiyo sauti ta dalilin jini dake zubowa daga kunnuwan su...
Dukkan ninsu sun kasance cikin wannan yanayi illa Al-Hussien da ko daya daga cikin hakan bai samesa ba...

*ATIF*
Sai faramar Rintsa Idanu yake yanata Girgiza Kai da niyar ya samu waraka daga jirin dayake ji da Kuma rashin jiyo sauti.
Haka yayita fama Amma Babu alamar kaiga ci,hala bai daina wannan aba tasa ba daga karshe ya dago hannun sa ya daidaita setin kunnuwansa ya soma tafi dan yajiyo sautin Amma shiru kake ji....

*Noor*
Zaune take ta mansher da hannunta tamkar laita tana ta kunna wuta tana kashewa yayinda Forzy ke zaune gefe guda

"Noor! Zamafa bai same muba ya kamata mu Kara gaba ko Allah yasa mu dace...."
Fadar #Forzy kenan inda #Noor din ta Bata ansar cewa.

"Ni Kuma Ina ganin Nanne daidai gurin da ya dace mu yada zango,Ya kamata muhuta Domin Duk jiki na Rad'adi."

"Alright na amince Miki bawai Dan inaso ba dan ya zaman mini dole ne,Amma bayan Nan karki sake naiman agaji irin wannan"
Haka Forzy ta ce da ita...inda tayi Gajeriyar murmushi Hadi da cewa
"Cikin sauri haka kin amince da bukata ta kamar yadda Y'an Kungiya guda keyi, gaskiya kedin ta Daban ce"
Forzy ko tayi Gyaran Murya sa'annan tace da ita...

"Kina nufin Dangan taka kenan irin ta mutanen Team daya,Hm banason mu hada Dangan taka ta wannan sigar nafison mu zauna tare a matsayin Two sister Har izuwa karshen Rayuwan mu Dukda bansan goben mu ya zata kasance ba,ko mutuwa ko Kuma Rai Amma inason mu kasance sister Har ranar da daya daga cikin wayen Nan abubuwan Dana lissafa zata riske mu."
Haka tayi ta zazzaga bayani yayinda ta sauke idanun ta kasa...bayan ta karashe bayanin nata ko ta dago Idanu da niyar da kalli fuskar Noor ta Kuma cigaba da bayanin...Amma sai tayi kicabus da #Noor na sheka bacci hade da mishari..

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now