SEASON_2 EPISODE_5

25 9 1
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
                          _The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
                           💀💀💀
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣5️⃣*
*_Ina Mai bada hakuri game da Hutu dana tafi na 1month ba tare da na sanar da mabiya littafina ba ina mai bada hakuri kwarai da gaske,bayan wannan ina kuma da Bad news tare da Good news the Good news is that Kofar ajali zata fara zuwa muku sau biyu a sati kuma an kara yawan typing and the bad news is that Dayan littafina mai suna kunfa Yakun zata daina zuwa muku a both WhatsApp da Kuma Facebook dalilin kuwa shine na shiga gasar marubuta na Arewabooks da wannan littafi Mai suna #kunfa Yakun wacce dokar shiga gasar shine banda posting a wasu guraren illa Arewabooks dan haka reads Ina Mai gaiyar ku izuwa chakwalkwalin Marubuta Hausa wato #Arewabooks domin karaya littafin Kunfa Yakun a kan farashi mai Rahusa wato ₦100 Only ga wayenda Kuma bazasu iyya bi ta Arewabooks ba zasu iyya jira izuwa karshen wannan wata ta march wacce bayan gasar farashin littafin zata koma kamar yadda take Da wato ₦300 dan haka kada ayi babu ku,ku gaggauta wajen garzayowa Arewabooks domin karantawa tare da manyan marubuta. Fans I need Your support ta yadda zamu lashe gasar Lets win wannan tare Fans_*


_*LABARIN*_
"Hm dakace basira sai nayi mamaki,to ina basira zatayi aiki anan,duba kaga cikin dakin koda tsinke babu a ciki toh taya zamu naimo hanyar fita?."

*Atif* juya Idanu yayi izuwa kusun ruwa huɗu na wannan ɗaki kafin nan ya saki kakkaurar nunfashi hadi da naiman guri jikin kofar ya zauna,haka Mu'azz shima zama yayi a gefen sa inda kafaɗar su ke hade da na juya...

Nan Atif ya lumshe Idanu inda Mu'azz shi kuma ya kura masa Ido ko kibtawa bayayi,a wannan lokaci kuwa da zaka umurce sa da yayi maka bayani yadda fuskar Atif yake ka zana dako zai fada maka komi ba tare da ya canza komi ba... Yana kan hakan kuwa sai Atif ya buɗe Idanu inda suka hada nan da nan Mu'azz ya murmusa hadi da ɗauke Idanu..

"What?."
Haka Atif ya tambaya inda Mu'azz yayi sauri mayar masa da cewar.

"Babu."

"Ehyee wato ana murmushi Babu dalili Kenan?,Toh bari kaga yanda zan saka ka fadi dalilin yin hakan."
Haka Atif din ya furta yayinda yayi kamar zaiyi masa cakulkuli,aiko Ganin haka yasakashi cewa...

"Wait! wait! wait!,zan fada maka."

"Okay muje ina sauraran ka."

Gajeriyar murmushi ya sake saki kafin nan ya sake cewa...

"Nothing oo."
Aiko juyo hakan yasa Atif ya Soma yi Masa cakulkuli, Mu'azz ko Idan da Abinda ya tsana a duniya to cakulkuli ne,Haka ya bada Gari inda yayi gaggawar cewa zan fada..

Kwanciya da gadon bayansa yayi gefen Mu'azz domin kuwa lokacin da yake yimasa cakulkuli tuni ya baje a kasa yana birgima, Soma cewa yayi...

"Kawai ina mamaki ne."

"Mamaki,akan me?."
Haka Atif ya sake mayar masa da tambaya inda ya soma da cewa..

"Ina mamakin yadda yanzu nake iyya tsayawa na kalli fuskar ka, sa'annan na saurari muryarka yayinda kake nuna kulawa ga ƴan tawaga ta,back then Babu wa'yanda muka tsana a duniya sama da ku amma gashi yanzu mune muka kasance killace a daki daya muna fira hade da wasannin... Gaskiya ko wannan ne kaɗai ya issa ya sakani murmushi kuma koda yanzu na daina numfashi bani da kaico sabida nasan Zaka kula da tawagar kamar yadda ya kamata."
Haka Mu'azz yayi ta suburbudo bayani babu kakkautawa yayinda idonsa na saman rufi na wannan daki...
Batare da  Atif ya ce dashi komi ba amma hakan bata saka ya daina zuba ba haka yayi ta tunowa Atif ire iren mugunta da kuma nuna tsaya a fili da kungiyar sa sukayi ta musu hada yazo karashe labarin saiya yunkura ya zaunu inda ya soma kame kame da kaga yanayinsa ko kasan yana sone ya bada hakuri amma mai zai faru bayan ya juya Idanu ya kalli Atif yayinda ya soma cewa...

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now