SEASON_2 EPISODE_2

24 2 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
                          _The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
                           💀💀💀
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣2️⃣*

Shekara alub Dubu daya da dari Tara da tamanin da takwas,Akayi wani saurayi wadda burinsa shine ya zamo abin alfahari a idon duniya ta hanyar naimo abinda yayi shekaru da shudewa...
Da wannan muradi nasa ya hada hannu da wani kanfani wacce aikinsu shine wallafa ababen tarihi.

Sun shahara a fannin binciko kayayyakin tarihi haka wannan saurayi yayi aiki dasu harna shekaru biyu ba tare da ya samo wani abin daya danganci kayakin tarihin ba,duk zancen daya kawo a matsayin shiririta suke dauka domin kuwa sun kwashe shekaru Yana ambata musu Abu guda daya wato wata kofar al'ajabi da yake gani a kowace mafarkin sa.

Maiko zai faru idan ka daura yaddarka akan Abu guda, mutane ko suka mansheshi abin dariya... So sad
Aiko a Tsakiyar party na samun takoban jaruman Daa ne suka Bata Masa Rai ya wuce ba tare da yayiwa kowa sallama ba haka ya koma gida inda ya shige gidan fuskar da Babu annashuwa.

"Son kamar naji dazu kace zaka dawo gida late,but what happened?."
Haka Mahaifiyar sa ta tambaya shiko ansa Mata yayi da "Nothing." Ya shige dakinsa inda ya aje ID nashi akan wata table dake 'Bari guda na wannan dakin,hayewa yayi kan katifarsa ya kwanta da ruwan cikin sa.

Kwatsam sai ga Kira ta shigo wayarsa Babu Bata lokaci ya ansa hade da sallama.

"Wa'alaikassalam Al-Hussien,Ya hakan? Tafiya Babu sallama."

"Eh wallahi an naimi na dawo gida ne shiyasa."
Haka ya Bata ansa inda ta mayar masa da tambaya kamar haka.

"Amma lafiya dai Kam?."

"Eh lafiya."

"Okay toh shikenan,Dama na kirane na sanar dakai cewar Hajara ta sauya *patner* "Abokina Aiki",tanajin nauyin sanar dakai hakan shiyasa ta sanar dani na Gaya maka Dan haka gobe saika naimi wani abokin aikin kaji."

Shiru yayi baice Komi ba ya sauke wayar...kansa ko ta daure domin dokar aikin wannan kanfani idan baka da partner kana gab da samun Kora daga kanfanin.

Nanfa ya kasa cewa komi,ya tsaya sai nazari yake hade da tunanin Abubuwan da suka faru tsakanin sa da shugaban kanfanin Nan ya Mike ya ciro wata jaka dake karkashin gadon sa,ya aza a saman katifar ya Kuma bude..
Nanfa sai zanen kofar ta baiyana a jikin wata farar pepa wacce nake kyautata zaton shi yayi hakan.

Sai yace...
"I'm very sure,idan kaga wannan zanen zakasa gabadaya ma'aikatan ka bincike akan wannan kofa."

Da haka yake tunanin yasamu mafita,ya Kuma sa aransa gobe zai gabatar da wannan gaban ma'aikan gurin.
Amma saidai kas baisan kaddara takan ruga fata ba.. danko da yasan halin da zai kasance ciki da bazai Rintsa ba,Amma tunda baisanda Wannan ba tuni ya lulluka cikin duniyar bacci wacce take cike da mafarkai.

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now