SEASON_2 EPISODE_1

31 8 4
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
                          _The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
                           💀💀💀
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣1️⃣*

*_NEW BEGGING_*

*Amrita!* *Amrita!*
Haka ake Kiran wannan suna cikin sauri kamar ana son dakatar da Mai wannan sunan aikata wata gagarumar abar...

Aiko wacce nake kyautata zaton itace Mai wannan sunan ta kasance tana tafe cikin zafin nama yayinda fuskar ta Babu annashuwa ko kadan,Shigar ta ofishin ta jibge wasu decoment dake rike hannun ta hade da cewa.

"What the heck,Mai kuke nufi da Kun sauke wannan bincike?."

Aiko fadar hakan keda wuya sai ga Mai Kiran sunan nata a baya ya shigo ofishin.

"Amritah Ya kamata ki dakatar da wannan shiriritar."

"Shiririta fa ka Kira abinda nake yi,Hm shin kasan Rayuka nawane a cen cikin had'ari?".

Haka Amritah da wannan santalele saurayi suka fara cacan baki kamar zasu doki junan but at the end juyawa tayi ta kyale sa Hadi da dawowa kan Jami'in dake zaune gaban ta.

"Ka iyya bude baki kace an sauke bincike Amma baka iyya d'aga katon tumbin Nan naka kaje binciken ba..."
Fadar hakan da tayi sai Wannan santalelen saurayin da suka shiko tare ya Kirawo sunan ta *Amritah* alamar ta tsayar da abinda take kokarin yi but sai hassalata Kiran sunan keyi haka tayi ta jifan sa da bakaken maganganu Hadi da cewar Babu ankin da suka iyya illa karban cin hanci,Kuma tayi takaici da gomnati tasa ragamar binciken a hannun su.

Wannan Dan sanda dai Yana da Damar daure ta but yayi shirune Dan mutuncin mahaifin ta da yake gani...
Amma dayaga abin ta soma wuce gona da iri sai ya Mike yayinda suka fara kaiwa junan su.... Kowa na fadar abinda tazo Masa a bakin,kamar Shirin film Yau dai ga rikici a ofishin Y'an sanda.

Wannan santalelen saurayin Hadi da Tarun ma'aikar gurin bude baki sukayi suna kallon su domin kuwa abin yafi karfin su.

"Amritah 2years fa ba kwanaki kadan bane."
Abinda ya fito daga bakin Wannan santalelen saurayin kenan yayinda sukayi shiru inda Amritah ta juyo ganinta izuwa kansa.

"bance Yayanki baya Raye ba,but Y'an sandan Suma suna iyyakan kokarin su wajen ganin sun shawon kan Komi damo sunsan idan suke da tuni sun naimo su but they don't that's why zasu sauke binciken domin duniyar da akawai matsaloli da Dama bazasu iyya tsayawa akan Abu daya har su kare ba."

Jiyo hakan yasa tayi sanyi,sauke kanta kasa tayi cen sai ta yunkura ta fice a fusace,Aiko fitar ta taja mota ta wuce...

Wannan santalelen saurayin ko ya fito cikin sauri inda ya tarar taja mota ta wuce...

"What's wrong with her?."
Abinda ya fito daga bakinsa kenan...

#Sunan ta Amrita,And Dalilinta na fada da wacen Dan sandar ko shine sun sauke bincike akan Yayar ta Wanda suka 'bata shekaru biyu da suka wuce tare da abokan aikin sa....Duk da cewar wannan batan nasu ta dauki lokaci Mai tsawo but sai take ji ajikinta har Yanzu Yana Raye...
Haka tayi driving babu inda ta tsaya sai Tsakiyar gidan su,inda ta sauka cikin sauri ta karasa inda ta tarar da Wannan santalele saurayin data Baro a police station a zaune zaman jiranta..

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now