001

389 13 4
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
           October/FitattuBiyar 2023.

           ©️ *Nana Haleema.*

_*Da Sunan Allah mai rahma mai jinqai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad S.A.W. Godiya ga Allah mad'aukakin sarki da ya bani iko da damar sake d'ora alqalami na akan sabon labarina mai take KWANTAN B'AUNA, ba dabarata bace, ba wayona bane,ikon sane shine ya nufa da bai nufa ba da bamu zo nan ba. Ina rok'on Allah yadda ka bani damar farawa lafiya ka bani ikon gamawa lafiya.*_

_Masoyana gani na sake dawowa a cikin wani sabon salon ina fatan zaku bani had'in kai fiye da wanda kuka bani a baya wajan ganin mun isar da sak'on da yake cikin labarin nan yadda ya kamata. Wannan tafiyar daban take da ko wacce, kuma doguwa ce sai kun shirya, salon daban yake ina tabbatar muku da hakan. Kunce kunyi kewata ko? To gani na dawo zan gani da gaske anyi kewar ko kuwa dai dad'in baki ne.😅 Gabad'aya labarin fiction bai faru a gaske ba, in yayi kama da naka ko naki to ayi hak'uri rashin sani ne._

_Warning: Ban amince a canja min labari zuwa wata siga daban ba, documents, audio ko a d'ora akan wani blog ba batare da izini na ba, a kiyaye dan Allah._

*001.*

*BAUCHI STATE,*
*MASARAUTAR AZARE KATAGUM.*

*Mafari.*
*1994.*

        Dare yayi duhu ya mamaye gari hannun ka baka gani sabida yadda garin yayi duhu matuk'a yayi tsiitt baka jin motsin komai ko ba'a fad'a ba yanayin garin zai tabbatar maka da dare ya tsala. Mata ne guda biyu suke tafiya da sassarfa cikin siririyar hanya mai d'auke da ciyayi da shuke-shuke, sauri suke sosai babu kamar wacce take a gaba ta bayan biye take da ita duk inda ta jefa k'afar ta itama nan take saka ta ta.

Hasken aci balbal suke hango a gaba hakan ya saka ta k'ara kaimi wajan sassarfa har suka iso inda suke gano hasken ta kalli wacce take bayan ta tace, "Dakata a nan." Cikin girmamawa tace, "An gama ranki ya dad'e, ki fito lafiya." Gaba tayi zuwa inda hasken yake da sauri kamar zata kifa domin burin ta ta isa wajan, dutse ne babba a wajan sai yadi kalar ja da aka yane dutsen dashi da kawunan rago a sak'ale anyi ado dasu wasu suna zubar da jini wasu sun fara bushewa wasu kuma sun zama k'ashi.

Zubewa tayi a k'asa tace, "Ta haihu! Ta haifi yara maza har guda uku a lokaci d'aya!" Yadda take fad'ar maganar muryar ta rawa take yi kana ji kasan cikin tashin hankali da d'imauta take. Baza ka d'auka akwai halitta a wajan da take ba sabida yadda wajan yake da duhu sosai aci balbal d'in a farkon wajan take kana shiga ciki babu hasken ta.

"Ha!Ha! Bana fad'a miki daman zata haihu ba?. Mun riga mun ga haka zata haihu kuma y'ay'an zasu girma." Ya fad'a cikin murya mara dad'in sauraro mai bada tsoro da firgita wanda yake sauraron ta. Abin mamakin bata tsorata ba sai sake gyara zaman ta da tayi tace, "Ya zanyi? Bazan iya jurewa hakan ba ko kad'an, ka nema min mafita kaine k'arfin guiwata. In y'ay'an nan suka girma na shiga uku."
"Me kike so a yiwa yaran?, A kashe su? A haukata su? A lalata rayuwar su ta gobe? A juyar da tunanin su? A sace su?. wanne kike so ayi musu a ciki? Ko wanne kike so zamu taimaka miki."

D'aure fuska tayi alamun rashin imani ya d'arsu a zuciyar ta cikin kaukasar murya tace, "Bana so a kashe su; ina so su rayu su d'and'ana irin kalar rayuwar dana tanadar musu, bana so su haukace sabida so nake da hankalin nasu amma su kasa sarrafa shi, bana so a lalata rayuwar su domin da nutsuwar su nake buk'atar su, bana so a sace su; domin a gidan su nake so su tashi inda suna ji suna gani su da gidan su zai bare ya fisu daraja da mahimmaci a cikin sa.  Ina so su rayu amma ko wanne su asan abinda za'a saka masa wanda dalilin hakan suna ji suna gani sarautar zata fi k'arfin su nan gaba. Bana son jinin Rabi yayi wani kwakwkwaran motsi sai naso, bana son jinin Rabi ya d'aukaka a duniya, yadda take jin tafi kowa ina so na nuna mata ita ba kowan komai bace face farcen susa a wajena."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now