010

57 6 2
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
       FitattuBiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*010.*

          Asad lokacin da ya koma d'akin sa gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa fassarar mafarkin da mahaifin yayi masa yana dawo masa cikin kansa tiryan-tiryan, kenan akwai mace da zata shigo rayuwar sa matsayin mata? Wacece ita?, a ina take Allah ya had'a su tun a mafarki?. Shin ita tana mafarkin sane ko batayi?. Sam baya so wata mace ta shigo rayuwar sa ko kad'an sabida shi kad'ai yasan illar dake tattare da hakan.

          Lumshe idanun sa yayi tuno Jidda ce zab'in Mama ya bud'e idanun a zuciyar sa yana tambayar kansa kodai Jiddan itace yarinyar mafarkin...? Numfashi ya sauke a hankali kammanin ta suke bayyana a idanun sa kamar lokacin yake mafarkin.

        Wara idanun sa yayi yana hango zubin ta da kammanin ta amma basa fita tarrr amma yana iya hango ta a idanun sa kamar almara, agogo ya kalla yaga yamma tayi sosai bazai yu yaje Abuja ya dawo a ranar ba da babu abinda zai hana shi zuwa Abuja wajan abokin sa Zaid ya zana masa fuskar da yake gani a mafarki ko zai iya gane ta in ya ganta, da ace yana kano ma a lokacin zai tafi amma yasan yana Abuja.. Haka yayi ta zaune da wannan tunanin kafin ya tashi ya d'auki makullin mota ya fita.

*☆☆☆*

       "Dan Allah Malam ka bani koda duba d'aya ne a kud'in na siyo mata kayan marmari ta sha bata iya cin abinci, koda tana ci ma ba'a son mai karaya tana cin abu mai nauyi sabida zagawa band'aki" Umma ta fad'a tana kallon Baba da yake tsaye a cikin d'akin.
Baba ya gyara zaman hula yace, "Kinga ni babu komai a jikina kud'in ma da aka bani na adana su sai auren ta yazo sai ayi amfani dasu, ga shinkafa da manja nan ai nasan tana san cin abinci da manja shiyasa na saka aka dafa mata."
"Yanzu Malam mai karayar ce zata ci shinkafa da manja? Kazar gida fa ita ake so masu karaya suci sabida tabi jikin su."
"To ba'a haifo ta inda zata ci kazar ba in baza ta ci shinkafar ba ta hak'ura."
"Amma Malam kud'in da aka bayar fa duk nata ne tunda itace take jinya."

          A fusace yace, "Amma ji kikayi nace ai na adana mata sai lokacin bikin ta ko? Ko saka su a gaba nayi naci banza da wofi dasu?." Jin yadda yake magana Rauda dake kwance tace, "Umma a bar shi zanci shinkafar." Umma tace, "ta ina zaki ci shinkafa Rauda?, baki san ba'a san mai karaya ya dinga cin abu mai nauyi ba sabida yawon band'aki?. Dan Allah malam ka bani koda naira d'ari biyar ce."

Tsaki yayi ya saka hannu a aljihu ya d'auko naira d'ari biyu yace, "gashi nan a siyo mata." Ba yadda Umma ta iya haka ta karb'a ta kalli Khairi da Khalil da suke gefe tace, "Khairi ina za'a samo mata kankana da lemon zak'i tasha?." Khairi tace, "Umma wajan asibitin nan akwai amma da gani zaiyi tsada tunda kinga asibitin manya ne."
"Jeki dai ki duba mana ko za'a samu" ta fad'a tana bata kud'in ba musu ta karb'a ta tafi.

         Tana fitowa wajan asibitin kuwa suna nan masu kayan zak'in ta tsallako ta nufo su tunda ta tawo kowa ya tashi dan daman an san siyayya za'ayi ta k'arasa wajan d'aya tace, "Sannu Baba." Yayi murmushi yace, "yauwa y'ata me za'a baki?."
"Kankana nake so ta naira d'ari lemo ma na d'ari" ta fad'a tana mik'a masa kud'in. Kallon ta yayi ya kalli kud'in ya kalli asibitin da ta fito sai ta girgiza kai yace, "yarinya babu na kud'in sai dai na baki lemo guda biyu ko wanne naira dari."

Wara idanu tayi tace,  "a unguwar mu naira ashriin-ashirin ne, bar shi bara na tambayi na gaba." Koda taje na gaban ma shima haka sukayi ta je na kusa dashi shi ce mata ma yayi babu ta tsaya cak kawai tana kallon su cikin rashin sanin abin yi.

           Mota ce ta faka a kusa da ita aka sauke glass dai-dai lokacin da take cewa, "Yayata aka kwantar a nan kuma bata iya cin abinci dan Allah ku taimaka min ku bani kankana da lemo na d'ari biyu ita kad'ai ce damu itama dak'yar Baba ya bayar."
"Dallah malama bamu dana kud'in ki ki wuce ki bawa mutane waje, y'ar aiki kawai" daya daga cikin su ya fad'a ta juyo idanun ta ya fad'a kan Asad da yake kallon su mai siyar da Apple yana masa magana ma amma baiji ba.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now