016

63 4 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*016*

        Yarda take jin gaban ta yana fad'uwa shima haka yake ji bai mata magana ba kuma bai d'aga glass d'in motar sama ba balle ya bar wajan yana tsaye har lokacin ko motsi bayayi. kanta ta sunkuyar k'irjin ta na bugawa duf, duf, duf, kamar wacce tayi gudu mai nisan zango tana raba idanu a k'asa tana ji kamar ta tashi ta gudu daga wajan. Ya bud'e baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya d'aga glass d'in motar ya ja motar ya bar wajan a guje.

          Nannauyar ajiyar zuciya tayi har da dafe k'irji jin ya tafi ta bi motar da kallo har lokacin k'irjin ta bugawa yake yi tace, "Ni Rauda na shiga uku, na d'auko abinda yafi k'arfi na" ta fad'a tana haki har lokacin tana kallon inda motar ta bi.
"Ke kuma zaman me kike a nan?" Aka fad'a daga gefen ta ta kalli inda taji maganart aga Habiba da Walida sai taji dad'i a ranta tana k'okarin mik'ewa suka zo suka kama ta ta mik'e tsaye.

      "Bari kawai gidan gaiswar can zan je fa har na shiga layin naga maza shine zan koma gida an jima Khairi ta rako ni." Habiba tace, "Mu ma can zamu je ai yanzu, muje to." Ba musu suka jera suna tafiya a hankali sabida yanayin tafiyar ta. Waiwaye suka ga tana yi suka juya suma suka babu abinda take kallo Walida tace, "Wai me kike nema ne?."
Bata amsa ba suka cigaba da tafiya har suka shiga cikin gidan rasuwar.

Ba jima suka fito bayan sun yi mata gaisuwa sunyi nisa da gidan Walida tace, "Oh yanzu in kin ga an cika a rasuwa to gidan mai kud'i ne an san za'a ci a sha, in iyayen mu suka rasu ko wani namu babu wanda zaki gani amma nan da yake akwai kud'i kalli motoci da maza dan Allah."
Habiba tace, "Ai yanzu daman in kin ga gidan rasuwa ya cika to tabbas akwai wani babban mai kud'i a gidan, ki duba irin abincin dake fitowa dashi fa kamar gidan biki ga kaji ga naman rago ga kuma ruwa da lemo kamar bikin gidan gwamna. Har da gwamna fa akayi jana'iza d'azu."

Walida tace, "An ce sarkin garin nan ma dashi akayi." Habiba tace, "A'a yanzu fa daga gidan sarkin nake bai zo ba baya jin dad'in amma ya turo wakilan sa Asad da Aliyu. Kuma shi ai yana da k'okari wallahi ko ba masu kud'i ba yana zuwa jana'iza, ki tuna ta gidan su Salima da baban su ya rasu shine ma ya ja sallar gawar, yanzu ne ance baya jin dad'i shiyasa ya turo wakilan sa kuma na jiki."

Jin hakan sai gaban Rauda yayi mugun fad'uwa ta kalli Habiba tace, "Waye Asad a y'ay'an nasa waye kuma Aliyu?." Habiba ta kalle ta tace, "ke dai kina son labarin gidan sarkin nan. Aliyu shine babba shine baya ji bashi da mutunci ko kad'an bai d'auki talaka a bakin komai ba, shine ya mare ki ranar nan badan nayi masa wannan kirari ba wallahi sai yace a kai ki ki share turken dokunan da kike jin tsoro kuma wallahi sai kin yi in ba haka ba a zane ki" ta fad'a tana kallon Rauda ta cigaba da fad'in,

"Bashi da mutunci ko kad'an ya raina talaka ganin talaka yake kamar ba mutum ba, in fa ya tawo bayi ko dogarai suka tawo wallahi sai kin koma can baya duk nisan wajan ya wuce sannan zaki wuce, ga shi kowa ya shaida a gidan shaye-shaye yake da neman mata shiyasa basa shiri da mai martaba. Naji ance a da yafi son Aliyun amma rashin jin sa ya saka ya fita a ransa tunda yayi yayi Aliyu ya shiryu yak'i kullum sake wastewa yake yi, gashi baya yafiya ko kad'an. akwai wani labari da naji y'ar sarkin Zamfara tayi masa rashin kunya ya saka aka d'auko masa ita yayi mata fyad'e na wulak'anci ya azabtar da  k'arshe yarinyar rasa ranta tayi, amma da yake babar sa ba kanwar lasa bace wallahi tuni an manta da maganar."

Habiba bata kula da halin da Rauda ta shiga ba tace, "Asad kuma shine Kamili mai kirki duk da baya fara'a amma kowa ya shaida a gidan nan shine ya fita zakka kamar ba jinin sarauta ba in yayi miki wani abun, bazai ga ana wulak'anta d'an adam a gaban sa ya k'yale ba, bazai ga ana cin zarafin wani a kyale ba, shiyasa ko hukunci Aliyu ya saka a yiwa wani da sun ga Asad zasu daina domin tasu tukunyar ce zatayi zafi a wajan sa. Ga taimako ko a hanya yaga tsoho zai tsallaka titi Asad yana iya parking mota ya fito ya tsallakar dashi ya bashi kud'i sannan ya koma mota yaje inda za shi, labari in yaji na gidan ku baku dashi ko kuna neman wani taimako sai ya taimaka muku wallahi, wani lokacin baza ma kusan shine yayi ba. Kuma kaf gidan nan babu mai kud'in sa hatta mai martaba bashi da kud'in da Asad yake dashI, sai dai mai martaba ya nunawa Asad kadarori amma zunzurutun kud'i Asad ne yake dashi tunda shi bada Nigeria yake aiki ba. Kullum fa sai ya bawa su Gwaggona dubu d'aya sadaka, sama da mata d'ari a gidan nan kowa sai ya samu yara da manya, in kana da buk'ata ma in Allah ya had'a ku ka nemi taimakon sa an gama shiyasa kullum yake gaba baya b'ata yin baya a rayuwar sa."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now