008

57 4 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
        FitattuBiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*008.*

         Washe gari ta kama ranar Asabar kamar jiya da wuri Hydar ya d'auki mota ya tafi asibitin da Rauda take duk da ciwon kan da yake fama dashi haka ya jure dan da ita ya kwana a ransa.  Dak'yar ya iya k'arasawa yayi parking motar ya shiga cikin asibitin kansa na sara masa sosai. D'akin da take ya fara shiga da sallama a bakin sa cikin takun nutsuwa da izzar sarauta da k'asaita da take yawo a cikin jijiyoyin jikin sa.

        Yana shiga idanun sa ya sauka a cikin na Rauda da take kallon wanda ya shigo, bai d'auke idanun sa daga cikin nata ba ganin yadda idanun ta sukayi ja duk da bai san su a yadda suke a baya ba amma yadda ya gan su ya san sun canja.  Kwarjini da fad'uwar gaban da ta ziyarci k'irjin ta ya saka ta janye idanun ta ta saukar k'asa duk da tsananin azabar da take ciki.

Babu kowa a d'akin sai ita kad'ai ya k'araso yana yatsine fuska sabida kansa ba k'aramin sarawa yake yi ba, ko takawa yayi sai yaji takun har kwakwalwa sa. Kallon ta yake yi ganin yadda take juya kanta kana gani kasan tana cikin azaba jikin ta har rawa yake ga k'afar tata a d'aure goshin ta manne da flasta, k'arewa fuskar ta kallo yake a karon farko k'irjin sa ya cigaba da bugawa yayi saurin d'auke fuskar sa yana kallon gefe guda.

Bud'e k'ofar akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo yaga Dr ne da kuma mahaifin ta ganin sa ya saka Dr k'araso yace, "barka da zuwa." Idanun sa ya lumshe ya bud'e kafin ya kalli Baba kafin yayi magana Baba yace, "Barka da safiya, da fatan an tashi lafiya."
"Ya mai jiki?" Ya furta a nutse yana kallon Baba.

"Mai jiki da sauk'i" Baba ya bashi amsa jikin sa har rawa yake yi.  Hydar ya kalli Dr baiyi magana ba hakan ya sake yace, "Komai zai tafi dai-dai in sha Allah." Kai kawai ya girgiza ya juya zai fita cikin takun isa sai kuma ya tsaya cak ya juyo yana kallon Baba kafin yace, "ba wani damuwa?."
Sai kuwa Baba ya gyara tsayuwa yace, "To Alhaji kasan lamarin abubuwan sai a hankali, ga gida ba abinci ga kud'in motar zuwa asibiti ga kuma......." hannu Hydar ya d'aga kawai baice komai ba ya saka hannun a aljihu ya d'auko d'aurin dari biyar guda biyu ya mik'awa Baba ya k'araso jikin sa har yana rawa ya karb'a baice komai ba bai kuma bari Baban yace komai ba ya fita.

Baba yabi kud'in da kallo yayi murmushi yana shafa fuskar sa yace, "To ke Rauda ai sai ayi fatan ki ta zama a asibiti wannan abin arzuk'i haka?, tunda nake na d'auka zan rik'e kud'i manya haka nawa na kaina ni kad'ai? Ai ban tab'a ba sai silar kwanciyar nan taki. Yo ba sai nayi ta addu'a kita zama ba indai irin wannan zasu zo hannu."

Rauda kallon Baba take yi duk da ciwon da take ciki hakan bai hana jin takaici da bak'in ciki a zuciyar ta ba, ji ta kud'i ma yake bata lafiyar ta ba gashi da ya shigo ko ya jiki bai mata ba dan ta fahimci shine ya buge ta.
Hydar dak'yar ya iya zuwa office d'in Dr ya zauna kansa yana juyawa a ya saka duka hannayen sa biyun ya dafe kansa, ganin hakan hankalin Dr ya tashi dan masomin tashin ciwon Hydar kenan hakan ya saka shi ya rud'e yace, "Prince lafiya? Me yake damun ka?."

        Kansa yake nuna masa jikin sa har rawa yake hankalin Dr ya tashi ya kalle shi yace, "Prince kana buk'atar drip." Kai ya girgiza alamun a'a kafin kuma ya ja dogon numfashi jin yadda kansa yayi mugun sarawa daga nan idanun sa duhu ya mamaye su amma duk da haka yak'i kulle idanun nasa.
"Prince! Prince!! Kana jina?, Prince!!!" Dr ya fad'a hankali a tashe amma lokacin idanun Hydar ya rufe ruf yana zaune idanun sa a kulle jikin sa ya saki duka.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" abinda Dr yake maimaitawa kenan jikin sa na mugun rawa ya bud'e k'ofar Office d'in sa yana fad'in, "Nurse!, Ashiir kana ina?!" Ya fad'a da k'arfin gaske wanda yake kira ya tawo a guje. "Zo ka taimaka min" ya fad'a yana komawa ciki suka shiga tare suka d'aga Hydar da jikin sa yake a sake kamar gawa  suka d'ora shi akan gado Dr hankalin sa tashe suka tura gadon Hydar zuwa babban d'aki na musamman.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now