021

61 2 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*021.*

           Hankalin Mama in ya kai miliyan ya tashi jikinta har rawa yake sabida tashin hankali ta tashi ta bar wajan da sauri ta nufi ciki hankalin a tashe sosai. Bata tab'a jin abu mai munin abinda Aliyu ya fad'a mata ba gabad'aya ya gigitata ta rud'e jikin ta har rawa yake yi sabida rud'ani. Kallon agogo tayi taga k'arshe sha d'aya na safe ya kusa ta saka takalmi da sauri ta fita zuwa b'angaren y'ay'an nata dan tana so ta tabbatar da abinda akace mata. Gab da zata shiga falon taji sautin muryar Hydar yana cewa, "Deaf in love, ban tab'a amincewa zaka fara soyayya da wata mace ba duba da yanayin ka da yanayin maganar, sai gashi ka fad'a ba tare da ka shiryawa hakan ba, wannan soyayyar taku itace silar accident."

Asad dai baice komai ba Mama jin abinda ta jiyo ta sake firgicewa ta kuma tabbatar Aliyu bai mata k'arya ba abinda ya fad'a gaskiya ne tunda gashi har Hydar ya sani yana kuma kiran soyayyar da silar accident, har zata shiga falon sai kuma ta koma da baya da sauri ta koma b'angaren ta ta shiga cikin d'akin ta hannu na rawa ta d'auki waya ta kira Mum. Buga biyu Mum ta d'auki wayar kafin tayi magana tace, "Sadiya in kina da time ki shigo yanzun nan." Daga can b'angaren Mum tace, "An gama ranki ya dad'e, bani mintina goma zan iso." Mama bata kuma jin me tace ba ta yanke wayar ta cillar kan gado tana zaga d'akin hankalin ta yayi mugun tashi.

        Zagaye take daga nan zuwa nan ta kasa zama abinda bata tab'a tunanin zai faru ba shine yake k'okarin faruwa jinin ta wanda ya fito daga jikin ta shine da son y'ar talaka, jinin talakawa kuma nakasashshiya. Jinin nata ma kuma Asad da ta k'wallafa rai a kansa ace shine yake son y'ar talaka gurguwa mummuna wannan ba k'aramin abun kunya bane a wajan ta. Shigowar Mum ya saka Mama ta juya Mum ta k'araso da sauri tana fad'in, "Ranki ya dad'e lafiya kuwa?."
"Ina fa lafiya; zauna mu tattara" Mama ta fad'a tana zama itama Mum d'in ta zauna.

"Me ya faru?."
"Meye ma bai faru ba Sadiya. Wani abu naji wanda yayi bazanar tarwatsa min zuciya ya jefa ni cikin wani hali wanda ban shirya tsintar kaina a cikin sa ba." Mum tace, "Ranki ya dad'e meye wannan d'in haka?."

Mama tace, "Ace wai jinina wanda na haifa da kaina ne zai so jinin talakawa, y'ar talakawar ma y'ar tallah a titi bak'a kuma gurguwa? Ta yaya hankali na bazai tashi ba?." Mum ta dafe k'irji ciki da firgici tace, "mun shiga uku, gaskiya dole hankalin ki ya tashi domin kuwa wannan babban cin mutunci ne da cin fuska a gare mu duka ba ke kad'ai ba."
"Bari kawai, yanzun nan naji maganar yanzun nan na tabbatar da ita amma zafi nake ji a k'irjina kamar ana tafasa min zuciya."

Mum tace, "Amma waye da wannan d'anyen aikin? Nadai san Aliyu bazai aikata hakan ba sai dai Hydar dan nasan shine zai iya b'allo mana wannan ruwan." Mama tayi murmushin takaici zuciyar ta na sake cika taf da k'una da b'acin rai tace, "Wanne Hydar ana zaune qalau...? inda Hydar ne ai hankali na bazai tashi haka ba. Babbar giwar fa Asad; wanda yake jiran kujerar masarautar nan wai shine yake soyayya da yarinya irin wannan." Gaban Mum yayi mugun fad'uwa jin wanda aka ambata ta dafe k'irji cikin tashin hankalin da ya bayyana akan fuskar ta itama ta zaro idanu tace, "Asad! Mun shiga uku."  Mama ta girgiza kai bata ce komai ba Mum tace, "Kuma kin tabbatar da maganar? In kika duba yanayin sa ranki ya dad'e sai naga kamar ba zai saurari irin su ba, Anya maganar nan daga majiya mai tushe take?."

         "Da Aliyu ya fad'a min ban amince sosai ba amma da naje na riska suna magana da abokin sirrin sa Hydar a sannan na tabbatar da Aliyu baiyi min k'arya ba. Sadiya jinina tafasa yake yi bazan lamunci wannan lamarin ba gabad'aya." Mum tace, "ni kaina jinin nawa tafasa yake ranki ya dad'e balle ke. Amma fa abinda mamaki anya kuwa ba asiri tayi masa ba? In ba asiri ba a yadda kika lissafo ta meye abin so a wajan ta har da yarima mai jiran gado guda zai d'aga kai ya kalle ta?."
"Babban tashin hankalina kenan Sadiya."
"To shi kin ji ta bakin sa?, ina nufin kun tattauna dashi akan lamarin?."
"Bai san ma na sani ba."
"Amma yana da kyau shima a tsawatar masa a kanta tunda yana jin maganar ki."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now