012

55 5 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
      FitattuBiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*012.*

"Na'am Yaya Asad" ta bashi amsa tana kallon sa shima kuma ita yake kallo da mamaki shinfid'e a kan fuskar sa. kallon k'ofar falon yayi ya dawo da kallon sa gare ta sai tace, "Mama ce ta bani fresh milk tace na saka maka a fridge shine nake waya nace na saka." Kai ya jinjina kafin yayi gaba sai kuma ya tsaya ya juyo ya kalle ta yace, "bayan yau ta tab'a aiko ki?." Kai ta girgiza alamun A'a tace, "bata tab'a ba, yau d'in ma dan bata fito bane ba ya saka ta bani, ni kuma bazai koma ciki ba shiyasa nake sanar da ita a waya."

         Baice komai ba ya shiga d'akin wajan fridge ya nufa ya bud'e yaga madarar a ciki ya kulle ya shiga d'akin sa yana k'are masa kallo kamar wanda yake neman wani abun kafin ya sauke ajiyar zuciya ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa. Wani abu ya gani ya gifta ta bayan sa bai juya ba ya cigaba da kallon mudubin ya sake ganin giftarwa abu hakan ya saka shi ya juya da sauri amma bai ga komai ba.
Wajan da yake ganin abun yake nufa amma baya ganin komai hakan ya saka shi kulle idanu ya bud'e tunda ya fara mafarkan nan sai ya dinga ganin abun kamar a zahiri ne yake faruwa.

        Bai jima sosai ba ya kuma fita yaje masallaci ya dawo suka had'u da Hafiz a k'ofar shiga falon suka shiga tare, suna zama Suhail ya shigo da sallama Asad ne kawai ya amsa banda Hafiz ya samu waje ya zauna yana fad'in, "kwana biyu kowa ya b'uya." Asad girgiza kai kawai yayi Hafiz ya kalli Suhail yace, "ko zaka iya bamu waje magana zamuyi." Suhail ya kalli Asad ya kalli Hafiz ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "okay babu damuwa."
"Noo zauna" Asad ya fad'a yana danna wayar sa jin hakan Suhail ya koma ya zauna Hafiz takaici ya sake kama shi ya girgiza kai amma baicr komai ba

      Shiru wajan ya sake d'auka dan shi dai Hafiz bazai yiwa Asad magana Suhail yana nan ba shi kuma Asad bazai yi maganar ba, Suhail ya mik'e yace, "Sai da safe" yana fad'a ya fita Hafiz kamar jira yake ya kalli Asad  yace, "Abinda kake yi fa sam ba mai kyau bane ba, kasan manufar Suhail a kanka amma ka dinga zak'ewa kana barin sa kusa dakai bayan nida kai mun san dama kad'an yake nema a kan ka ya halaka ka amma kake bashi fuska har haka."

       Shiru yayi kamar bazai amsa ba jikin sa wani iri yake ji cikin kwanakin gabad'aya baya son zaman gidan yana jurewa ne kawai sabida Mama amma da tuni ya bar k'asar, "Ka nunawa wanda yake neman ka da sharri baka san yanayi ba yafi riba" ya bashi amsa yana kallon sa shima yana kallon sa.
"Amma kasan....." dakatar dashi Asad yayi yace, "Bana son magana a kan hakan. Muyi abinda nace."
"Okay better" ya bashi amsa shima kafin ya mik'e ya fita dan bazai yi maganar ba shima ya fasa.

       Murmushi Asad yayi bayan ya fita cikin su biyun shi dai ya rasa wanda yafi sonsa ko wanne burin sa ya bashi kariya shiyasa yake ji dasu baya so yaga an tozarta wani a gaban sa. Duk da shi ba wani sakewa yake da abokai ba amma babu laifi su kan danyi hira sama-sama.

        Tashi yayi ya fita daga apartment d'in gabad'aya yana takawa a hankali kamar ko yaushe ana zubewa ana kwasar gaisuwa yana amsawa a ciki, zaga gidan kawai yake badan akwai abinda zaiyi ba sai dan haka zuciyar sa take bashi umarni, har yazo b'angaren da yake da duhu sosai har ya gota sai kuma ya dawo da baya jin abinda ake cewa, "ku bari kawai shima Asad d'in maganin sa zamuyi yadda muka kwantar da Hydar shima haka zamu kwantar dashi, ko muyi masa kurciya ya bar k'asar gabad'aya bazai sake dawowa ba har abada." Dariya yaji anyi kafin yaji ance, "Allah yaja zamanin Master planer, Asad bazai tab'a mulkar garin nan ba in sha Allah, jinin Rabi'atu baza suyi sarauta ba in Allah ya amince."

       Motsi yaji alamun za'a fito ya tsaya a wajan cak yana jiran yaga wacce zata fito, rad'ad'in da ya kawo masa ziyara a idanun sa ya saka shi kulle su ba tare da yayi niya ba yana juya kansa yana so ya bud'e amma ya kasa idanun nasa ruwa suke yi, hannu ya saka a aljihu ya d'auko tissue yana goge idanun nasa hankalin sa na wajan da yake jin maganar amma baya gani sosai, sai da ya d'an samu sauk'in idon ya d'auko wayar sa ya kunna haske ya sake haska wajan amma babu kowa alamun da gangan aka saka masa abu mai yaji a idanun sa.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now