Trailer

118 4 5
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
                   FitattuBiyar

*ƊANƊANO*
      ****Dare yayi duhu ya mamaye gari hannunka baka gani saboda yadda garin yayi duhu matuk'a, yayi tsiitt baka jin motsin komai ko ba'a fad'a ba yanayin garin zai tabbatar maka da dare ya tsala. Mata ne guda biyu suke tafiya da sassarfa cikin siririyar hanya mai d'auke da ciyayi da shuke-shuke, sauri suke sosai babu kamar wacce take a gaba, ta bayan biye take da ita duk inda ta jefa k'afarta itama nan take saka tata.

Hasken aci balbal suka hango a gaba hakan ya saka ta k'ara ƙaimi wajan sassarfa har suka iso inda suke gano hasken, ta kalli wacce take bayanta tace, "Dakata a nan."

Cikin girmamawa tace, "An gama ranki ya dad'e, ki fito lafiya."
Gaba tayi zuwa inda hasken yake da sauri kamar zata kifa domin burinta ta isa wajan, dutse ne babba a wajan sai yadi kalar ja da aka yane dutsen da shi da kawunan rago a sak'ale anyi ado da su, wasu suna zubar da jini wasu sun fara bushewa wasu kuma sun zama k'ashi.

Zubewa tayi a k'asa tace,"Ta haihu! Ta haifi yara maza har guda uku a lokaci d'aya!"
Yadda take fad'ar maganar muryar ta rawa take yi kana ji kasan cikin tashin hankali da d'imauta take. Baza ka d'auka akwai halitta a wajan da take ba saboda yadda wajan yake da duhu sosai, aci balbal d'in a farkon wajan take kana shiga ciki babu haskenta.

"Ha!Ha! Bana fad'a miki daman zata haihu ba?. Mun riga mun ga haka zata haihu kuma y'ay'an za su girma."
Ya fad'a cikin murya mara dad'in sauraro mai bada tsoro da firgita wanda yake sauraronta. Abin mamakin bata tsorata ba sai sake gyara zama da tayi tace, "Ya zanyi? Bazan iya jurewa hakan ba ko kad'an, ka nema min mafita kaine k'arfin guiwata. In y'ay'an nan suka girma na shiga uku."

"Me kike so a yiwa yaran?, A kashe su? A haukata su?, A lalata rayuwar su ta gobe?, A juyar da tunanin su?, A sace su?. wanne kike so ayi musu a ciki? Ko wanne kike so zamu taimaka miki."

D'aure fuska tayi alamun rashin imani ya d'arsu a zuciyarta cikin kakkauasar murya tace, "Bana so a kashe su; ina so su rayu su d'and'ana irin kalar rayuwar da na tanadar musu, bana so su haukace saboda so nake da hankalin na su amma su kasa sarrafa shi, bana so a lalata rayuwarsu domin da nutsuwar su nake buk'atarsu, bana so a sace su; domin a gidansu nake so su tashi inda suna ji suna gani su da gidansu sai bare ya fisu daraja da mahimmaci a cikinsa. Ina so su rayu amma ko wannensu asan abin da za'a saka masa wanda dalilin hakan suna ji suna gani sarautar zata fi k'arfinsu nan gaba. Bana son jinin Rabi yayi wani ƙwaƙwƙwaran motsi sai na so, bana son jinin Rabi ya d'aukaka a duniya, yadda take jin tafi kowa ina so na nuna mata ita ba kowan komai bace face farcen susa a wajena."

Ya kuma sakin dariya mai munin sauraro yace,"ki d'auka wannan an gama, ki jira girmansu ko wanne a cikinsu zaki ga da kalar dabi'ar da zai tashi, ni ne nace zanyi in na fad'a bana fasawa sai na tabbatar. Amma da sharaɗi!."

Murya na rawa tace, "Meye sharaɗin?."
"Komai zai faru daga ba ya babu ruwanmu, aikinmu mun riga munyi in kika ga wani canji to ki tabbatar kin sab'a abin da zan fad'a miki nan gaba."

Farin ciki ya mamaye zuciyarta tace, Na amince da ko wanne irin sharaɗi, duk wahalarsa, duk qalubalensa, duk tashin hankalinsa na amince zanyi. Godiya nake, in da kai bazan zubar da hawaye ba ni na sani."

"Tashi kije, abin da kike so zai biyo baya!" ya fad'a a firgice ta mik'e da sauri ta juya ta bar wajan da sassarfa zuciyar ta cike da farin cikin ta samu cikar burinta.

*☆☆*
"Matuk'ar ina da rai, Matuk'ar ina raye babu wanda zai hau karagar sarautar garin nan sai Asad, zan iya sadaukar da kowa da komai akan cikar burina, zan iya aikata komai akan Asad ya mallaki sarautar nan ko meye, Ko da za'a rasa lafiya, ko da Za'a rasa rai, ko da za'a rasa dukiya, ko da za'a rasa komai da aka mallaka a duniya sai Asad ya mallaki kujerar sarautar nan ko da ba ya so. In har hakan bata kasance ba tabbas ba ya raye ne."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now