003

66 4 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
             FitattuBiyar 2023.

                   ©️ *Nana Haleema.*

*003.*

Asad da ya bar wajan mahaifin sa wajan mahaifiyar sa ya wuce duk da dare ya fara yi amma yasan bata yi bacci ba,kamar koda yaushe a hankali yake takawa ma'aikatan dare na ta kai gaisuwa wasu yayi murmushi wasu ya d'aga musu hannu wasu ma ya share dan baya son takura.  Lokacin da ya shiga ya tarar da Aliyu a zaune a kan kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa ga ma'aikata a zagaye dashi ya bar su a tsaye bai sallame su ba yana aikin danna wayar sa.

Sallamar da yayi suka amsa duk suka duk'a suka gaishe shi ya d'aga musu hannu bai kalli inda Aliyu yake ba kai tsaye d'akin mahaifiyar sa ya shiga, Jim kad'an ya fito samun da yayi tana wanka ya zauna shima a kan kujerar da ta kasance suna zama in bata wajan bai magana ba. "Dan girman Allah ranka ya dad'e kayi hak'uri bana jurewa tsayuwa kayi min wani hukuncin dan Allah" wani daga cikin ma'aikatan da suke zagaye dashi ya fad'a k'afar sa na rawa sosai.

Kallon sa Aliyu bai yi ba balle ya bashi amsa cigaba yake da abinda yake yi, gumi ne yake ketowa daga dukkan kafofin tsohon k'afafun sa sai rawa suke haka jikin sa idanun sa yayi ja sabida wahala, baya yayi zai fad'i Aliyu da yake danna waya yace, "in ka fad'i k'asa ka tabbata yau a tsaye zaka kwana." Dafa kujera yayi jikin sa na cigaba da rawa hawaye na zuba daga idanun sa.

          Dukka sauran ma'aikatan jikin su yayi sanyi dan ya fisu shekaru a cikin su kowa yasan bashi da lafiyar k'afa balle ya iya tsayawa,  Asad da ya ke jin komai yaso ya basar sabida ba shiri suke da Aliyu ba amma ganin abin yayi yawa ne sosai ya saka shi ya kalli tsohon yace, "Zauna!." A sama dukka suka ji maganar tasa Aliyu ya juyo ya kalle shi amma kamar ba shine yace na hankalin sa ma baya wajan su.

       Tsohon ya kalli Asad suka had'a ido da idanu yayi masa alama da ya zauna,  kallon Aliyu yayi yaga shi yake kallo ya kuma kallon Asad yaga shima shi yake kallo duk sai ya rud'e ya rasa abinda zaiyi, maganar wa zaibi a cikin su duk sai ya diririce. Aliyu yace, "ka sake ka zauna wallahi gobe sai na saka an zane k'afafun ka an ji musu ciwo yadda zaka jima baka taka ba."

         Asad ya mik'e tsam ya k'araso inda tsohon yake ya kama kafad'un sa ya zaunar dashi a k'asa kafin ya kalli Aliyu su had'a idanu ko wanne fuska a d'aure zaiyi magana Asad ya d'aga masa hannu yace, "Bana son hayaniya pls." Kallon ma'aikatan Asad yayi da hannu ya musu alamun me suke a wajan, d'aya daga ciki yace, "muna jiran ya bamu umarnin abinda zamuyi ne ranka ya dad'e" ya fad'a cikin girmamawa yana kallon Asad.

Da hannu yayi musu alamun duk su fita daman sun gaji babu b'ata lokaci suka fita tsohon da ya zaunar ya mik'e ya tafi kamar zai fad'i yayi saurin rik'o hannun sa ya tsaya cak sannan ya sake shi tsohon ya duk'a yace, "Allah ya kare ka a duk inda kake, ya baka kariya daga duk ka masu nufin ka da sharri, ya sanya ka zamo sarki a wannan gidan. Allah ya taimake ka ya biya maka dukkan buk'atun ka mai zuciyar alkhairi." Kai kawai ya d'aga masa ya fita da sha'awar rayuwar Asad duk da sarautar da izzar ta ratsa shi amma baya wulak'anta na k'asa dashi.

         Kamar jira Aliyu yake su fita ya mik'e yana nuna Asad yace, "Kaga Asad ka fita daga rayuwata tun kafin ka tunzura ni nayi maka abinda har ka mutu baza ka manta dashi ba, me kake ji dashi har da zan kira ma'aikata ka saka su fita?, kawai rainin hankali kake ji dashi ko kuma tsabar raini ne?" Ya fad'a a fusace yana kallon sa.
Bai ce komai ba sai ma waje da ya samu ya zauna ya cigaba da danna wayar sa dan shi baya son hargagin Aliyu ko kad'an.

        Hakan da yayi ba k'aramin sake harzuk'a Aliyu yayi ba ya koma gefe yana jan wuci yana k'arewa Asad kallo yana hasashen irin abinda ya kamata yayi masa wanda zai saka ya wuce takaicin da yake ji a zuciyar sa. Sallamar Hydar ta katse su Asad ne ya iya amsawa kawai banda Aliyu Hydar ya k'arasa ya xauna kusa da Asad kafin yace, "Our king how far."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now