002

95 3 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
                 FitattuBiyar 2023.

                     ©️ *Nana Haleema.*

*002.*

             Bayan fitar Rauda Umma ta kalli Baba ta girgiza kai tace, "Dan Allah Malam ka daina d'orawa y'ay'an ka talla ka bar mu mu matan ka mu dinga siyar maka kome kake so a gida, tura yaran nan tallah babu abinda zai haifar sai d'a mara ido."
"Kedai kiyi masa amma ni kam gwara a d'ora musu tallan, yadda za'ayi rububin siya a wajan su mu baza'a yi a wajan mu ba. sune y'an mata wani saurayin ko dan su kula shi ma ya siya a wajan su" wacce take fitowa daga d'aya d'akin ta fad'a tana kallon Umma.

Baba yace, "bar ta Asabe ita ai baza ta tab'a ganewa ba shiyasa, indai akace an tab'a mata Rauda shikenan babu zaman lafiya, ko da yake tun lokacin yayyen Raudan ake fama da ita y'ar bak'in ciki ce bata so taga nayi arzuk'i." Murmushi Umma tayi ta kalle su cikin takaici tace, "Amma bakwa gudun wani abun ya faru dasu ta silar tallan da ake basu?, kun manta y'ay'a mata ne dukkan su sun kai munzalin aure?."
Baba ya nuna ta da yatsa yace, "Kinga Binta bana son mugun fata a kan yarana, ina yi musu addu'a ba dare babu rana Allah zai kare min su duk inda suke,  kar na sake jin kin furta wata magana mara dad'i a kan su in ba so kike ranki ha b'aci ba." Umma bata kuma cewa komai ba ta koma d'akin ta.

Tana jiyo shi yana fad'in, "kuma wallahi kika cigaba da hure mata kunne akan yaron nan Anas da yake son ta take k'in sauraron sa ki kiyayi hukuncin da zan miki, ban tab'a ganin uwa y'ar bak'in ciki kamar ki ba. Ace y'ar ki ta samu mai kud'i amma ki dinga bari tana wulaƙanta shi....? ita ba y'ar kowa ba ba kuma jikar kowa ba, gata ita ba kyau ba balle ace shi ya gano ya nace amma ki dinga hure mata kunne."

Tana jin sa tayi shiru ta zauna a kan ledar da take shinfid'e a d'akin tana girgiza kai. Lamarin sa kullum sake gaba yake duk da girman da yake cimma masa, indai akan kud'i ne ba sani ba sabo, ko meye zaiyi indai akace kud'i zance ya k'are, tun lokacin baya haka yake gashi shekaru har sunyi nisa halayyar sa tana nan.

Malam Adam haifaffan garin azare ne mazaunin unguwar Katsalle, y'an uwan sa da kowa nasan y'an Azare ne a nan aka haife su a nan kuma suka tashi suke kuma zaune. Yana da mata guda biyu Asabe da Binta y'ay'a kuma yana da goma takwas mata biyu maza, Asabe tana da guda shida biyar mata namiji d'aya, Umma kuma uku mata d'aya namiji shine auta a gidan gabad'aya. Suna zaman lafiya babu laifi wata ran ka gansu kamar y'an uwa wata rana kuma da kaga yanayin su kasan kishiyoyin juna ne. An aurar da mata biyar uku suka rage a gidan, Rauda wacce ta kasance itace babba wanda suka rage a d'akin su sai k'anwar ta Ummulkhairi sai k'anin ta Khalil. D'aya d'akin kuma sa'ar Rauda mai suna Rahma sai k'anin ta Garzali.

          Talakawa ne gidan wani lokacin abincin da zasu ci gagarar su yake sai dai kowa ya san abinda zai ci shida y'ay'an sa, mai gidan Allah ya d'ora masa san abin duniya baya jin kunyar rok'o haka baya jin kunyar cewa a bashi, koda sirikan sa ne mazajen y'ay'an sa indai Allah ya had'a su koda a hanya ne da wahala su rabu bai tambayi wani abun ba duk da suma ba masu kud'i bane ba. Tun y'ay'an nasa mata suna nuna rashin jin dad'in hakan da yake yiwa mazajen su har suka gaji domin ba zai daina ba.

         Tunda su Rauda suka kammala secondary school suka sauke a islmaiyya ya ajjiye batun karatu daman dak'yar aka k'arasa shi, dak'yar da sid'in goshi da ya hana su cigaba da karatu yace bashi hali suka koma islmaiyya suna hadda shima dan kyauta ce wani d'an siyaya ya d'auki nayi. Shekarar farko aka kori Rahma ita kuma Rauda ta cigaba da yin haddar ta tana sake sanin littafan addini dan Allah ya bata kaifin basira.

Bayan ta kammala hadda a cikin shekara d'aya ta dawo gida sosai ta samu ilimi ta k'aru ta kuma san abubuwa da yawa a fanin addini,  burin ta ta zama y'ar jarida amma kuma Baba ya daqile wannan burin nata domin yace bashi da halin da zai kaita jami'a dole ta jinginar da burin ta badan taso ba. Daga nan ya fara dafa musu abinci yana d'ora musu talla su shiga kasuwa su siyar su kawo masa kud'in ya d'aga pillow ya ajjiye dan babu wanda zai ci kud'in koda abinci ne babu a gidan sai dai a hak'ura.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now