014

51 1 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
       FitattuBiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1
*014.*

      A sanyaye ta shiga gida hannun ta rik'e da leda ta zauna a inda ta saba zama Umma ta kalle ta tace, "Lafiya yake neman ki?." Ledar hannun ta ta nuna mata kana tace, "Wai cewa yayi nayi hak'uri da abinda ya faru jiya ga maganin wani ya siya min kuma ya biya bashin baya ya kuma bada kud'in wanda zan karb'a nan gaba."  Da mamaki Umma ta rik'e baki tace, "ikon Allah! Waye kuma ya biya?."

"Ban sani ba Umma, na tambaye shi yace shima turo wani aka yi amma wanda ya siya d'in bai zo da kansa ba."
"Wanne d'an albarkan ne da wannan aikin?."
"Nima kaina ya kulle Umma."
Umma ta nisa kafin tace, "to wama zai miki haka in ba Anas ba? Shi kad'ai ne saurayin da yake zuwa wajan ki yanzu shine zai shiga lamarin ki, Jikina yana bani shine ya siya miki."

Rauda tace, "Amma kuma Umma Anas baya garin nan tun ranar da muka had'u had'uwar k'arshe ya cewa Baba zaiyi tafiya ban kuma ganin sa ba,  bai ma san halin da nake ciki ba a yanzu." Umma tace, "Ke kamar ba y'ar zamani ba Rauda? Kin manta yanzu waya tana isar da ko wanne irin sak'o a kuma duk inda kake a duniya?."
"Haka ne Umma, amma ina tantama gaskiya."
"To in ba shi ba waye Rauda?."
"Babu kowa" ta fad'a a sanyaye Umma tace, "to kin gani, amma Allah ya yi masa albarka ya raba shi da iyayen sa lafiya."

Rauda ta murmusa har cikin zuciyar ta take jin farin ciki tace, "Amin Umma Karon farko kenan a rayuwar ta da naji ya burge ni" ta fad'a farin ciki na shiga zuciyar ta sosai. Umma tace, "kin ga bara na kawo miki ruwa ki sha maganin nan jiya kin sha wahala" ta fad'a tana mik'ewa ta kawo mata ruwa a kofi ta sha maganin ta shafa na shafawa ta ajjiye ragowar.

        Inna da take d'aki taji komai ta fito fuskar ba yabo babu fallasa ta wuce su bata ce komai ba daman Umma tasan baza ta ce ba dan idan magana ce akan Anas k'arara zata nuna miki tana bak'in ciki da ba Rahma yake so ba. Baba ne ya shigo a gigice fuskar sa taf fara'ar da basu tab'a ganin irin ta ba yana fad'in, "mutanen gidan nan kuna ina! Kuzo kuji abin arzuk'i da farin ciki" ya fad'a yana shigowa yana kallon su. Umma tace, "Malam lafiya?."
"Bari kedai, ai babar ki ta iya haihuwa da ta haifo ki na aura kika haifo min Rauda. Bawan Allah shigo mana" ya fad'a yana kallon k'ofa.

Mutumin ya shigo sanye da k'ananu kaya hannun sa rik'e da leda ya durk'usa har k'asa ya gaishe su kafin yace, "An turo ni akan na kawowa Baba keke napep guda biyu, sannan ance na bawa mahaifiyar Rauda wannan kud'in" ya fad'a yana d'auko kud'in daga leda.  Da hanzari Baba ya kaiwa kud'in cafka mutumin ya hana shi ya kalle shi yace, "Ita aka ce na bawa Baba." 

Yak'e Baba yayi yace, "Daman zan mik'a mata ne ai."
Mutumin ya k'arasa wajan Umma  ya ajjiye kud'in a gaban ta yace, "sannan yace a gaida wacce bata da lafiya shima baya jin dad'i ne da ya zarar ya samu lafiya zai baro inda yake yazo in sha Allah. Gashi yace a bata" ya fad'a yana sake d'auko kud'i a rufe a takarda ya sake ajjiyewa Umma.

"Sannan akwai kayan abinci da yace a tawo dasu gasu can za'a shigo dasu yanzu." Umma da ta saki baki tana kallon mutumin tace, "bawan Allah waye ya turo ka da wad'an nan abubuwan haka?."
Kafin yayi magana Baba yace, "Anas mana, da shi mukayi maganar zai siya min abin hawan da zan dinga samun kud'i dashi, gashi kuma ya cika alqawari." Umma ta jinjina kai tana kallon mutumin tace, "Amma hidimar tayi yawa bai kamata mu karb'i abin hannun sa ba tunda babu wata magana mai k'arfi tsakanin sa da Rauda, gaskiya a mayar masa."

Baba yace, "ai na riga na ba shi auren ta, ko bana raye shine mijin Rauda tun ba yau ba na mallaka masa ita" ya fad'a hakora a bud'e dan kar ma a mayar da kud'in. Mutumin ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "Za'a shigo da kayan yanzu" ya fad'a yana fita jim kad'an aka fara shigo da kayan abinci babu abinda babu harda yankakkun kaji da d'anyen nama. Bayan an gama shigowa da su yace, "To Baba zan wuce ni." Umma tace, "Bawan Allah da gaske Anas d'in ne ya turo ka?." Zaiyi magana Baba yace, "Kina da matsala Binta, in ba shi ba waye zai aiko mana da wannan abin arzuk'in? Shine an fad'a miki sai faman maimaita magana d'aya kike yi."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now