007

48 4 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
        FitattuBiyar 2023.

              ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*007.*

        Bayan sallar juma'a aka samu kiran gaggawa daga mai martaba duka iyalan gidan hatta matan da suke gidan mazajen su sai da aka kira su aka taru a fadar cikin gida duk wani da ya kasan jini a gidan sai da aka kira shi. Dukkan su suna zaune ana sauraren abinda mai martaba zaice kowa yayi mamakin kiran.

          A kamalance da k'asaita da zallar nutsuwa da hikima ya fara fad'in, "kamar yarda na saka a kira ku nasan da yawan ku kuna tunanin lafiya akayi kiran gaggawa haka kasancewar bai tab'a faruwa ba. Ba wani abun bane an kira ku ne akan murabus da nace zanyi a d'ora Asad." Kallon kallo aka shiga yi dukka mutanen wajan gaban su na fad'uwa matuk'a burin kowa yaji k'arshen maganar.

           "Babu batun ta a yanzu mu janye, amma nan da wasu kwanaki maganar zata dawo matuk'ar ina raye kuma abinda nace baza'a canja shi ba, in kunga abinda na fad'a bai faru ba ku tabbatar k'asa ta rufe fuska ta." Shiru fadar take ko masu kirari babu kasancewar magana ce ta cikin gida su kad'ai babu damar magana kuma sai ya bada dama. Fuskokin mutanen dake wajan zaka kalla zaka hango zallan farin ciki akan abinda yace, fuskar Mama ce kawai a d'aure cikin akasin farin ciki amma bata ce komai ba.

"Bana son na sake jin wata magana akan wannan na yiwa tufkar hanci, in lokaci yayi komai zai bayyana amma banda yanzu."  Nan ma shiru suka kuma yi kafin yace, "Akwai wanda yake da magana a cikin kuz?." Shiru akayi babu wanda yace komai sai daga baya babar y'a kaf gidan mai Maimuna wacce taci sunan mahaifiyar mai martaba ake kiran ta da Mummy tace, "Allah yaja da zamanin mahaifin mu, Allah ya kare mahaifin mu a duk inda yake. Hukuncin mai martaba shine hukunci a ko wanne lokaci, babu mai magana a cikin mu."

Kai ya girgiza kafin yace, "Kowa zai iya tafiya." Kai k'asa sukayi da kansu a tare dukkan su suka furta, "A tashi lafiya." Dukkan su suka fita kowa ya nufi b'angaren sa zuciyar kowa fari kar sab'anin Mama da take cikin mayuwacin hali.

            Tunda ta shiga b'angaren ta take zagaye hankalin ta a tashe ta matuk'a ta kasa zama sai kai kawo take, ta  d'auki waya hannu na rawa ta kira Sadiya tana d'auka tace, "Sadiya akwai matsala babba."
Daga can b'angaren tace, "Ranki ya dad'e me ya faru?."
"Mai martaba ya janye batun murabus d'in sa haka kawai babu wani dalili."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Ranki ya dad'e munyi sake gaskiya, duk yadda akayi wani abun aka yiwa mai martaba kuma ya shiga jikin sa. In fulani zata tuna akwai wanda zasu shiga su fita wajan ganin an tarwatsa mana abinda muka saka a gaba."
"Shiyasa nace miki ina buk'atar zuwa Kano, dole ne na shiga garin Kano a kwanakin nan, babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da mulkin Asad, babu shi ko waye" tana fad'a ta yanke wayar hannun ta na rawa ta kira Asad.

            Yana zaune yaga kiran ta daman yasan sai Mama ta neme shi ya d'auki wayar baiyi magana ba ya sauke daga kunnen sa ya tashi ya tafi b'angaren nata, can ciki ya shiga inda ya kasance babu mai shiga sai su yana shiga kafin ma yayi magana tace, "a tafiyar da kuka yi dashi me kuka tattauna har ya canja shawara lokaci guda?." Ya d'ago ido kamar zaiyi magana sai ya fasa ganin hakan sai ranta ya sake ya b'aci tace, "bazan lamunci wannan shirun naka ba Asad! Ka fad'a min kaine kace masa baka ra'ayi?."

         Kai ya girgiza alamun a'a kafin yace, "wallahil azim Mama bamuyi magana irin wannan dashi ba, ki amince dani bazan yi k'arya dan na kare kaina ba" ya fad'a a sanyaye yana kallon k'asa. remote ta d'auka tayi jifa dashi ya tarwatse a wajan tana wuci tace, "koma dai meye Asad baka isa kak'i karb'ar mulkin nan ba indai ina da rai, Asad kaine zaka mulki garin nan babu wanda ya isa ya shiga tsakanin ku da mulkin nan, dole ka cika min burin."  tana fad'in hakan ta wuce zuwa d'akin ta tana fad'in, "A shirya min tafiya gobe zan wuce Kano." Kai ya girgiza sai da ta shiga ciki sannan ya juya ya fita zuciyar sa gabad'aya babu dad'i ko kad'an.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now