018

56 3 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*018.*

         Cizo ya kawo mata karen shine ya saka ta yin k'ara ta kulle idanun ta tana jiran taji sukar hakoran sa a a naman ta amma sai taji shiru, ta bud'e idanun ta a hankali taga karen baya gaban ta kamar d'azu ta juya gefen ta ta ganshi a tsaye ya juyo yana kallon ta kusa da wanda bata tantance waye ba. A hankali yake takowa yazo kusa da ita suka had'a ido sai jikin ta ya cigaba da tsuma ya had'e hannayen ta waje guda tana kuka amma ta kasa magana.

      D'auke kai yayi daga kanta ya kalli wad'anda suka sato ta sai suka zube a k'asa cikin girmamawa hannun su na jinjina d'aya yace, "Tuba muke ranka ya dad'e, zamu aikata abinda ka umarce mu yanzu, ka yafe mana zamu yi."
"Aliyu ya saka ku kawo ta nan?" Ya fad'a a tausashe cikin muryar sa mara hayaniya wacce bata fita sosai yana kallon su.

       Sai a sannan suka gane bafa Aliyu ne a gaban su ba babar giwa ce da kanta sai jikin su ya k'ara kaimi wajan tsuma d'aya yace, "Kayi mana aikin gafara ranka ya dad'e. Yarima Aliyu ne ya umarce mu da mu kawo ta nan mu sakar mata Bobby ya cize ta sannan muyi abinda muke so da ita. Mun tuba wallahi baza mu sake aikata hakan ba." Kai Asad yake girgizawa kaf yasan plan d'in nasu sune da Aliyun basu san ya sani bane amma tunda yasa a fara tracking d'inta yasan da haka.

Kallon da yayi musu ya saka jiki su rawa suka fara fad'in, "Kiyi hak'uri yarinya muma ba san ran mu bane ba wallahi saka mu akayi babu yadda zamu yi, kiyi hak'uri ki yafe mu." Kanzil Rauda bata ce ba sai kuka da take mai tsuma zuciya ya sake kallon su duk sai suka sake diriricewa dan basu fahimcin kallon na meye ba.

D'aya ne ya mik'e da sauri ya kawo mata sandinan ta guda biyu yace, "kiyi hak'uri." Da hannu yayi musu alamun da su wuce su tafi a da sauri suka hau mota suka ja da gudu. Dawo da kallon sa yayi kanta yadda jikin ta yake tsuma tana kuka hakan ya tabbatar masa da ba k'aramin tsoro take ji ba sai ta sake bashi tausayi yana so yayi mata magana amma bai san me zaice ba.

Yana tsaye tana kuka sai da ta gaji dan kanta sannan ta fara k'ok'arin tashi tsaye, bata iya tsayuwa da k'afafun ta hakan ya saka tashi yake gagarar ta ganin sai juyi take kamar wancan lokacin ya saka shi mik'ar da ita tsaye ya bata sandar ta rik'e sai kuma ta dafe kai da hannayen ta guda biyu jin yadda yake sarawa. Bata daina kuka bai kuma ce komai ya juya wajan motar sa ya shiga karen shiga mazaunin baya ya dawo da motar daidai kusa da ita amma har lokacin bai ce k'ala ba.

Wajan take kallo babu alamun abin hawa in tak'i shiga motar ta cuci kanta dan bata san a inda take ba balle tabi hanyar da zata sami mota, tana so ta shiga amma rashin yi mata magana da baiyi ba ya saka take shakka kar ta shiga ya wulaqanta ta.

      Sauke glass d'in gefen ta yayi da hannu yayi mata alama da ta shiga a sanyaye ta ja handle d'in motar ya bud'e, so take ta fara saka sanda guda d'aya sannan ta shiga sai ta shigo da d'ayar amma ta kasa ta rasa yadda zatayi. Babu tsammani taga ya fito daga motar ya dawo inda take ya karb'o guda d'aya ya saka a ciki ta saka k'afar ta mai lafiyar ta shiga cikin motar, saka mata d'aya sandar yayi kana ya kulle k'ofar ya zaga ya shiga.

Ganin ta yayi duk a tsorace tana kallon baya ya juya yaga Bobby ya san shi take jin tsoro bai ce komai ba yaja motar. kuka take cigaba da yi tana goge idanun ta har lokacin jikin ta bai daina rawa ba shi kuma bai ce mata ci kan ki ba tuk'i yi a nutse. Kukan ya dame shi har tsakiyar kansa yake jin kuka amma bai san me zaice mata ba shiyasa yayi shiru ya jure abinda yake ji ya cigaba da tafiya.

Ba tare da tayi zato ba taji sun tsaya tana d'ago kai ta gan su a k'ofar gidan su d'an hasken kwan solar da ya haske wajan gidan nasu duk da babu wani haske sosai amma dai yafi babu ya haska wajan, kallon sa tayi ta kalli gidan nasu ta tabbatar fa nan ne mamaki da tsoro suka yi mata yawa tunanin ta a ina ya san gidan su?.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now