024

56 3 3
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
           Fitattubiyar 2023

           ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*024.*

         Asad baiga Baba ba da ya fita a mota ya tarar da Hydar kawai ya shiga ganin hakan Hydar yaja motar ya tafi yana satar kallon Asad da yake murmushi mai kyau kana gani kasan zuciyar sa fari tas take a wannan lokacin. Shima murmushi Hydar ya mayar da hankalin sa kan tuk'in kana yace, "in aka ce min deaf zai so wata mace lokaci d'aya haka bazan amince ba, amma sai gashi na gani na kuma tabbatar kana cikin soyayyar da baka san iyakar ta ba." Hannu Asad ya saka ya shafa kansa yana kallon titi shi kansa mamakin kansa yake yi domin bai tab'a d'auka akwai soyayyar wacce zata yi masa kamu lokaci guda kamar ta ba, bai kuma d'auka akwai macen da zai yiwa wannan son na farar d'aya haka ba sai gashi ya tabbata yana kuma kan faruwa a lokacin.

"Ka fad'a mata kana sonta face to face dai ko?." Asad ya girgiza kansa alamun a'a Hydar yace, "to meyesa baka ce mata ba? Meye amfanin zuwan da mukayi?, dan fa ka sanar da ita kana sonta ya saka na d'auko ka muka zo nan."
"Oho" ya furta ya shafa fuskar sa yana lumshe idanun sa. Hydar yace, "gashi ai yanayin ka ya dawo daidai da kazo ka ganta, kana cikin damuwa amma gashi daka ganta ka dawo normal. But da ka sani kayi mata bayanin yadda kake sonta, ina so ka sani Asad lokaci yayi da zaka ajjiye wannan rashin maganar taka, ka san ita soyayya ba ruwan ta da mulkin ka ko nasabar ka ko kud'in ka, a iya kwanakin da ka fada tarkon sonta nasan ka tabbatar. Ka fuskanci abinda zuciyar ka take so in ba haka ba zaka iya rasa ta, soyayya tana son kulawa sosai."

Kallon sa yayi idanun sa a bud'e sosai yace, "babu maganar rasata" ya fad'a yana cize bakin sa cikin jin zafin kalmar rasa ta da yace zaiyi. Hydar yayi y'ar dariya kana yace, "na sani shiyasa nace ka dage Asad, a kan idon ka aka nuna mana wanda yake sonta zai iya kwace ta in ya fika iya kula da ita, na farko kai ga yanayin nature d'in ka ga kuma yadda abin yazo in ba mayar da hankali kafi ba zaka zama looser, kuma sun saba da wancan kai kuma kalma mai tsaho bata tab'a had'a ku ba." Murmushi kawai Asad yayi bai kuma cewa komai ba ya mayar da hankalin sa kan in ya tuna Mama gaban sa sai ya fad'i yaji komai ya fice masa a rai.

             Washe gari.

           K'arfe tara na safe Mum tazo ta d'auki Mama a mota suka fita su biyu kacal ko hadiman Mama bata bari sun biyo ta ba babu wanda yasan inda zasu je sai su kad'ai.  Tunda ta shiga motar take k'wafa Mum da take tuk'i dai bata ce komai ba domin itama nata ran a b'ace yake sosai sai daga baya Mama tace, "Wai ni Takawa zai yiwa fad'a kamar zai dake ni akan wata banza y'ar matsiyata bayan hak'urin da ya saka na basu?, kamar ni ace na bawa wad'annan k'ask'antun hak'uri....? Me suke dashi a duniya da zan kalle su nace suyi hak'uri....? an cuce ni wallahi" ta fad'a tana dukan jikin motar ranta a b'ace.


Mum dai bata tanka ba tafiya suke yi lokaci kad'an suka shiga wata unguwa da babu jama'a ko kad'an sai gidaje kad'an-kad'an kamar rugar fulani suka faka motar suka fito dukkan su suka shiga cikin gidan.

       Wani k'aramin d'aki suka shiga wanda yake baje da magunguna na itace dana gari da turarruka kana dosar d'akin kasan d'akin maganin gargajiya ne, wanda yake zaune a gaban faranti da aka zuba masa yashi da k'aton mudubi a kusa dashi yana ganin shigowar su ya murmusa yace, "Barka da zuwa Fulani." Waje suka samu suka zauna kafin Mum tace, "Malam mun same ka lafiya."
"Lafiya lau Sadiya, ya yara suke?."
"Lafiya lau. Matsala ta taso dole muka zo da kanmu shiyasa nace basai kazo ba zamu shigo nida Fulani."

Mama ta kalle shi bayan ta d'age nikaq d'in fuskar ta tace, "kamar yadda ta maka bayani a waya Sunan yarinyar Rauda inaso a duba min aga kodai asiri ta yiwa Asad har ya furta yana sonta duk da tarin nak'asun dake tare da ita da kuma tarin y'an matan da suke so ya kula su ya tsallake su yaje wajan ta." Jin abinda Mama tace ya jawo farantin gaban sa ya fara dubawa kusan minti d'aya da wani abun kafin ya karkad'e hannun sa yace, "a abinda muka gani bata yi masa asiri ba had'uwar jini ce kawai."
"Ka dai sake dubawa ko wani ne daban yayi masa asiri dan ya sota" Mum ta fad'a tana kallon sa.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now