022

49 5 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*022.*

          A hankali suke takawa zuwa cikin gidan suka shiga da sallama idanun sa ya fad'a na Rauda da take zaune cikin ranar da bud'e har taje inda suke fuskar ta duk taji ciwo musamman bakinta da ya fashe. Runtse idanu Asad yayi ya kawar da kansa gefe daga kallon ta kafin Baba yace, "Kunga irin abinda aka yi mana. kalli mahaifiyar Rauda har targad'e aka yi mata, ga ita kanta Rauda da ta kasa tashi tsaye tun da akayi abun bamu sani ba ko an sake karya mata k'afa ne; kalli saman d'akin babar Raudan sun cire kwanon bayan sun dake ta. Me muka yi muku haka?."

        Hydar ya gyara tsayuwa yace, "Kuyi hak'uri Baba bamu san abinda ya faru ba kenan sai yanzu muke jin labari shine muka tawo nan d'in kai tsaye dan muyu maganin abun, Mama kiyi hak'uri bamu san abinda ya faru ba kenan" ya fad'a yana kallon Umma. Rauda ta kalle shi ta zaro idanu waje cikin zallar b'acin rai da tashin hankali tace, "Ba tun yau ba daman in aka cuci mutum sai ace yayi hak'uri, in aka zalumci talaka sai ace yayi hak'uri ya yafe sabida bashi da gata da wanda zai shige masa gaba ya karb'i hakkin sa. dan an fimu kud'i da mulki ba hakan yana nufin an mufi daraja a duniya bane, muma mutane ne baza mu lamunci azo har cikin gidan mu a ci mana mutunci sannan a dake mu ba kuma ace muyi hak'uri; bazai yu ba wallahi. Meye ya had'a mu daku da za'a dake mu a kanku? Tsautsayi ne ya ratsa tsakani fa akwai shikenan sai ya zama abin tashin hankali?, naga tun kafin bayyanar ku cikin matsayin wanda suka bige mu ai rayuwar mu muke yi babu abinda muka nema muka rasa, daga shigowar ku rayuwar mu har an fara neman raywuar mu?" Ta fad'a cikin fusata da masifa tana kallon su dukkan ranta a b'ace ba.

         Hydar yazo wuya ba'a tab'a yi masa irin wannan fad'an ba a duniya sai yau nan take ransa ya b'aci amma babu yadda ya iya yayi k'okarin b'oye fushin sa kana yace, "Na fad'a miki ko meye ya faru babu sanin deaf babu sani na, inda mun sani hakan ai baza mu bari ta faru ba. Yanzu ake sanar damu muka tawo dan muga su waye amma bamu same su ba, meyasa baza ki fahimta ba?."
"Zuwan ku d'in banza da wofi dashi gwara ku zauna a gida ku sha a.c yafi min wallahi. Sai da aka gama ci maa mutunci sannan zaku d'auko k'afa kuce wai kunzo to kuyi mana me? Ku bamu hak'uri kenan ko?. Ni abinda nake so naji ma akan wanne dalili zasu dake mu har su yiwa Ummana wannan rashin mutuncin?, suna zancen wani Asad ni meye had'ina da wani Asad?, su ya dama bani ba wallahi in ma wani sharrin aka je aka min can ta matse muku amma wallahi sai maganar nan taje gaba in ba haka ba na shiga radio na yayata abinda aka mana ko babu komai k'imar gidan ku zata ragu."

       Hydar ya kalli Asad da ya zuba mata idanu kawai yana kallon ta ya girgiza kai yana cize bakin sa cikin zallan b'acin ran da yake ji a zuciyar sa, in badan Asad ba ta isa ta dinga fad'a masa wannan kalmai marasa dad'in jin ya tsaya yana kallon ta bai hukunta ta ba?. Ya daure yace, "Ni da kaina nace kuyi hak'uri muje a fara yi muku magani kafin komai." Kafin Baba yayi magana ta kuma cewa, "Bama so ku rik'e kayan ku talakawan da ake rainawa sun yiwa kansu magani kuma zasu karb'arwa kansu hakkin kansu."

"Wai ke meye haka ne? Ina baki hak'uri kina sake d'aga min murya kina fad'ar duk abinda yazo bakin ki?, wani dalili kawai ya saka nake tsaye a gaban ki ina baki hak'uri amma badan shi ba bazan zo inda kuke bama balle ki samu bakin fad'a min abinda kike so. Na fad'a miki kuyi hak'uri zaku ji abinda ya jawo hakan wanda ban sani ba shima wanda akayi dukan dan shi bai sani ba, meyasa kike haka ne?" Ya fad'a cikin fad'a yana kallon ta ransa a b'ace. Zata kuma magana Baba yace, "Muna so muji dalilin dan gaskiya sai maganar nan taje kunnen mahaifin ku sai naji dalilin dukan da aka yiwa iyalai na har cikin gida."

        "Firstly ku fara ganin likita a duba lafiyar ku, please Baba kuzo muje" Hydar ya sake fad'a yana kallon Baba. Rauda ta kalli Asad da idanun sa yake yawo a kanta amma in baka fahimta ba baza kace ita yake kallo ba taja dogon tsaki tace, "Wanda akayi dan shi d'in yana tsaye k'ikam shi bazai bada hak'uri ba sabida bamu kai ya bamu hak'uri ba an dake mu an daki banza kenan, to wallahi sai na d'auki mataki ina k'yale komai banda a tab'a min iyayena." D'auke kai yayi daga kanta Baba ya kalle ta yace, "Ya isa haka Rauda bana son sake jin bakin ki, ke Rahma tashi mu taimaka mata ta tashi aje asibitin."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now