009

61 3 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
         FitattuBiyar 2023

               ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*009.*

            Tunda Mama tazo inda yake hankalin ta yake a tashe tana zaune kusa dashi tana fad'in, "Asad me kake ji a cikin naka? Kayi min magana dan Allah. Yaushe ya fara yi maka ciwo? Me kake ji?, zafi yake kome?." Bud'e idanu yayi ya zauna sosai yace, "Mama, I'm okay fa."
"Ban amince ba Asad, kalli face d'in ka fa yadda ya koma, tashi muje asibiti da sauri daman nasan babu ta yadda za'ayi kaci abincin Hajiya ba tare da ka samu wani abun ba."

Hannun ta ya rik'e duk da ciwon da cikin sa yake masa yace, "Mama kar ki tayar da hankalin ki."
"Ta yaya bazan tayar da hankali ba Asad? Abincin fa ta baka kaci gashi har kana ciwon ciki wanda baka tab'a yi ba, hankalina kake so na kwantar ko me?." Shiru yayi bai amsa na kafin ya lumshe idanun sa yace, "bacci zanyi."
"Baza kayi bacci ba Asad sai munje asibiti, kar ka kulle idanun ka ka bud'e mu tafi." Suhaima ce suka shigo tare da Dr Yasir Mama na ganin sa tace, "Zo da sauri ka duba shi." Da saurin kuwa ya k'arasa yana yanayin jikin nasa yana tambayar sa abinda yake ji duk da yasan babu lallai ya basa amsa.

        Allurar ciwon ciki yayi masa kafin ya d'ago ya kalli Mama yace, "Ranki ya dad'e ba wani abin tayar da hankali bane nayi masa allura zai daina ciwom." Jidda tace, "are you sure zai daina?."
"I'm very sure." Mama tace, "in akwai damuwa muje asibiti ko scanning ne ayi masa."
"A'a ranki ya dad'e zai ji sauk'i." Kai ta d'aga shi kuma ya fita da sauri baya so tayi masa maganar Rauda da take asibiti.
Aliyu da ya shigo a lokacin ta kalls tace, "Ka rik'e shi ku shiga d'aki ya kwanta, please Aliyu take care of him bana so wani abun ya same shi."

        Mik'ewa Asad yayi ya tafi d'akin da kansa Aliyu ya kalli Mama yace, "basai na taimaka masa ba kin gani" yana fad'a ya shiga d'akin da yake kusa da na Asad d'in ya kullo k'ofa. Fita Mama tayi suma su Suhaima suka fito suka ga ta mik'e alamun b'angaren mai martaba zata je su suka kuma koma ciki.
Mai martaba yana zaune shi kad'ai kamar ko yaushe aka mata izinin shiga ta shiga da sallama ta nemi k'asa ta zauna tana kallon wani wajan daban.

        Ganin hakan sai ya murmusa yace, "Rabi'atul adawiya ya akayi ne?."
"Allah yaja da ran mijina burin mutanen gidan nan suga bayan y'ay'ana me suka tare musu? Hydar gashi can ciwo ya tashi, ga Asad ma Hajiya ta bashi zogale yaci gashi can a kwance yana ciwon ciki. Ya suke so nayi ne me na tare musu?." Mai martaba ya mik'e daga kashingidar da yayi yace, "Ciwon Hydar ya tashi baki sanar dani ba?." Ta kalle shi tace, "Na rud'e ne gabad'aya ana kira na naje asibitin da je duba wata yarinyar da ya buge a can ciwon ya same shi na dawo dashi nan, ga Asad ma a kwance ya suke so nayi ne?" Ta fad'a kamar zatayi hawaye.

Mai martaba yace, "kar ki zubar da hawaye ban sanki da raguwar zuciya ba ki daure kamar yadda kike daurewa a koda yaushe. Yanzu ya jikin Asad d'in?." Idanunta ta goge tace, "yayi bacci. zogale yaci wanda Hajiya ta bashi daman na tabbatar ba da zuciya d'aya ta bashi ba, yanzu gashi can a kwance babu lafiya, burin su suga Asad ya mutu sai sun kashe sa hankalin su zai kwanta."

       Mai martaba ya kalle ta sosai yace, "bana son zargin da kike saurin yi ki fara tabbatar da abinda kika ga gani kafin ki yanke hukunci."
Bata ce komai ba hakan ya saka ce sake cewa, "kar ki damu duka zasu samu lafiya babu wanda ya isa yayi musu abinda Allah bai nufa ba, Asad yana da ibada sosai k'aramin abu ko babba bazai kama shi ba sai wanda Allah ya nufa. Hydar zai samu sauk'i nan kusa ki daina tayat da hankalin ki."

       Bata ce komai ba a nan ma amma ta d'an ji sanyi a zuciyar ta yace, "muje na duba jikin su da kaina" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ita kuma bata mik'e ba. Ganin hakan ya saka hannayen sa da kansa ya mik'ar da ita tsaye yana kallon fuskar ta da murmushi yace, "kar ki bada ni mana, ko yaushe ina fad'in ke jaruma ce samu mace mai irin tsayayyiyar zuciyar ki abu ne mai wahala ya zaki bani kunya kum?. Come on ban san ki da haka ba, muje."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now