019

52 5 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*019.*

         Irin kallon da yake yi masa jikin Waziri yayi sanyi qalau kuzarin sa ya ragu amma duk da hakan bai nuna ba ya daure ya cije baya so ya bayyanar da raunin sa kar Aliyu ya gano shi, Aliyu wani irin murmushi yake yi ya sauke k'afar daga kan d'aya ya kalle shi ta k'asan idanu yace, "kana ganin hakan zai yu kuma?."
Jin abinda yace sai ya sauke ajiyar zuciya yace, "Mai zai hana ya yu ranka ya dad'e?, indai zaka bada goyan baya abu ne mai sauk'i faruwar hakan."

Ya juya manyan idanun sa ya sauke su akan Waziri kana ya mik'e tsaye yana kallon sa yace, "Zan yi tunani a kan hakan" yana gama fad'ar hakan ya fita daga falon bai sake kallon waziri ba. Waziri ya dafe k'irji gaban sa yana fad'uwa sosai ya d'auko waya da sauri jikin sa har rawa yake, kiran yake ba'a d'auka ba ya cillar da wayar akan kujera ya mik'e yana zaga d'akin.
"Me yaron nan yake nufi dani? Yaji sirrina a banza ya tashi ya tafi ya barni....? kenan yana nufin na jira shi?, in bai amince bafa?." Naushin iska yayi ya koma ya zauna jikin sa har b'ari yake sabida tashin hankalin da yake ciki.

Kamar kuma anyi masa allura ya mik'e da sauri ya shiga d'aki dan bai ga ta zama ba.

Aliyu lokacin da ya fita mota ya shiga ya zauna yana tuno abinda Waziri ya fad'a masa sai yayi murmushi yaja tsaki yace, "Wai ni zai yiwa wayo, an fad'a masa ni d'in shashasha irin sa?, ko kuma ya d'auka zuciya ta irin ta Asad ce?." Sai kuma ya tsaya da dariyar ya d'auki waya da sauri ya kira Waziri, kamar jira yake yaji an d'auka ya gyara murya yace, "Na amince da tayin ka." Yana jin ajiyar Wazirin a waya baice komai ba ya yanke wayar ya ajjiye wayar wayar yana kallon glass d'in gaban motar.

      Asad bai koma gida ba sai da ya gama yawon sa har dare yaci abinci sannan ya koma, ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga apartment d'in su ya tarar da Aliyu a zaune ya kunna sigari yana sha, har ya wuce ya dawo yana kallon sa har ga Allah baya son warin ta ko kad'an ya masa magana sau babu adadi amma yak'i.
"Aliyu ko a lafiyar ka abinda kake yi ba daidai bane" ya furta yana kallon sa. D'ago idanun sa yayi ya kalle shi ya murmusa ya sake zukar sugarin ya fesar kana yace, "lafiya ta kace ba taka ba, a gani na ai hakan ba damuwar ka bace ba."

Asad bai kuma cewa komai ba ya d'aga kafa zai wuce yaji yace, "kabi a hankali ka kuma taka tsan-tsan akwai lokaci Asad." Baice komai ba ya wuce ya k'yale shi ya shiga d'akin sa. Can k'arshen d'akin ya wuce ya janye labule sai ga k'ofa ta bayyana a wajan wacce in ba kasan da ita ba baza ka tab'a cewa tana wajan ba ya shiga ciki ya kulle k'ofar. K'aton wajan karstu ne mai d'auke da drawer na littafai manya-manya na addini dana karatun zamani, littafai ne sama da guda dari uku a wajan ko wanne rukuni da cover sa da sunan su a k'asa ga table da kujera mai guda d'aya a wajan da k'aramar lamp a kai.

Kujerar yaja ya zauna ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu kansa na juyawa ya rasa dalilin da ya saka yake jin hakan da zarar ya shigo d'akin sa, daurewa yayi ya tashi ya k'arasa jikin cover ya d'auki littafai guda biyu ya k'araso ya zauna a kan kujerar ya fara dubawa. Karantawa yake a nutse yana bin rubutun daki-daki yana Nazariin abinda yake yi.
Rufe na farko yayi ya bud'e na biyun yana sake bi a hankali har ya kammala karanta inda yake da buk'ata ya kulle ya kifa kansa a kan littafin kamar mai bacci.

Juma'a ce gobe kuma shine zai gabatar da hud'uba shiyasa yake ta dube-duben littafai amma zuciyar sa ta kasa bashi topic guda d'aya da zaiyi hud'ubar a kansa, d'ago kai yayi ya saka hannu biyu ya d'an daki kansa a hankali ya furzar da iska waje yana kallon d'akin gabad'ayan sa. Zuciyar sa yaji yana bugawa da sauri har yana jin sautin ta a kunnen sa ya runtse idanun fuskar Rauda ta bayyana a gare shi.
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a hankali yana dafe da kansa har lokacin bai kuma daina jin bugun zuciyar ba.

      Cize bakin sa yayi ya runtse idanu kafin ya koma ya jingina da kujerar, sautin muryar ta yake tunowa a hankali tana shiga ilarin jikin sa, tasirin muryar da dad'in ta ya saka shi kulle idon sa yana sauke numfashi gashin jikin sa na tashi. sautin muryar yarinyar mafarkin sa yaji sai ya bud'e idanun sa; ya kasa banbance shin itace yake gani a mafarki ko kuma ba ita bace?, bai tab'a ganin waccan fuskar ta completely ba amma idanun ta da goshin ta irin na Rauda ne, akwai banbanci a maganar su waccan muryar ta tafi zak'i a kan ta Rauda, ita kuma ta Rauda tafi sanyi da taushi kamar mai mura in tana magana.
Tashi yayi ya kashe hasken d'akin ya fita daga cikin da ya dawo d'akin sa ya zauna a gefen gado ya rasa tunanin ma mai zaiyi.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now