015

47 4 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

                ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*015*

Fuska a had'e Rauda ta shiga cikin gidan su Khairi na bayan ta tana gurshek'en kuka sai Khalil da yake biye dasu a baya. Ganin su haka ya saka Umma ta kalli Rauda tace, "Tun d'azu Rauda sai yanzu?." Zama Rauda tayi kafin tace, "Sai da naje titi." Umma tace, "Ke kuma Ummin ce ta dake ki kike kuka?."
Khairi tace, "Anty Rauda ce, dan kawai naga wanda ya siya mata fruits a asibiti na yi masa magana shine ta mare ni" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da kuka.

Umma ta kalli Rauda tace, "Akan me zaki mare ta Rauda bayan abin arzuk'i tayi? Ai ba laifi bane da taga wanda yayi mata alkhairi ta nuna ta san shi. Inda arzuk'i kema gaisawa ya kamata kuyi dan taimakon ki yayi." Rauda tace, "Umma bai cancanci a kula shi ba, bai san darajar d'an adam ba kwata-kwata." Da mamaki Umma tace, "Ke ya akayi kika sani?."
"Umma ina wannan d'an sarkin da muka had'u dashi a gidan sarki..? Wanda muka sake had'uwa dashi har Khalil yake cewa yace na shiga mota nak'i...?. dashi muka kuma had'uwa yau, shine fa wanda take cewa ya siyi kayan marmari dan tsabar k'arya."

"Wallahi ba k'arya nake ba shine Umma" Khairi ta fad'a tana kuka. Umma ta kalle ta zatayi magana Rauda tace, "Sai sake marin fuskar ki sannan zakiyi mana shiru naga alama. Bashi da kirki fa ko kad'an Umma yau ma baki ga kalar rashin mutuncin da yayi min ba."

Umma tace, "Kuma dai?." Rauda tace, "Kin san Khairi da shegen surutu ta dinga zuba a gaban sa maganar da ba'a tambaye ta ita take furtawa shiyasa na mare ta, wannan ai ba wanda za'a kula bane ba. Habiba tace min har neman mata yake yi garin haka in yayi mata wani abun fa tunda yasan babu abinda zamu iya?." Umma ta rik'e baki tana nuna Rauda da yatsa tace, "Ina raba ki Rauda da irin wad'annan zantuttukan wallahi, kinga ki kiyayi bakin ki kar ki jawo abinda zaki zo kina dana sani. Ina ruwan ki da sabgar sane wai? Ba abinda ya had'a ku ki dinga k'okarin gefa rayuwar ki a hatsari sabida tsiwa. Kuma kar na k'ara ji kince yana neman mata tunda kedai bai neme ki ba bai kuma nema a gaban idanun ki ba, ki kiyayi tsayuwa gaban Allah."

"Wallahi Allah na tsane shi tsana mai muni Umma, ban tab'a jin tsanar wata halitta a duniya kamar sa ba, bana son ganin koda fuskar sa ce." Umma bata ce komai ba ta wuce tana d'aura alawar magriba dan bata ga amfanin yi mata magana ba.

         Bayan an idar da sallah suna zaune cikin k'aramin hasken fitilar tsakar gidan Baba ya shigo kamar an cillo shi har tuntub'e yake yi, "Ke Rauda maza jeki ga Anas can yana jiran ki." Abincin hannun ta ajjiye dan tasan ko bata ajjiye ba tunda yace ta tashi sai fa ta tashj tana k'okarin mik'ewa cikin fad'a yace, "ki k'arfafa jikin ki malama ki tashi." Babu wanda ya tanka ta tashi ta saka hijjabi ya d'auki kujerar da take zama da kansa yayi gaba tana bin sa baya.

        Sanyin khamshi taji tunda ta shigo soron gidan nasu Baba ya ajjiye mata kujerarya kalli Anas da yake tsaye yace, "Gata ta fito maka da ita da kaina, zauna mana" ya fad'a yana kallon Rauda. Ba musu ta zauna Anas ya duk'a har k'asa yace, "Allah ya saka da alkhairi Baba." Baba ya amsa da amin ya fita.
Zama yayi kan irin tata kujerar yana kallon ta cikin hasken fitilar da aka ajjiye a soron ga hasken wayar sa da ya kunna gana waje wanda yake shigowa, bata d'ago ba shi kuma baiyi magana ba.

        Jin shirun yayi yawa ya saka ta d'ago sai suka had'a ido karon farko tayi murmushi mai kyau tace, "Ina wuni." Jinjina da kujerar Anas yayi ji yayi in bai jingina ba iskar soyayya da take kad'a zata iya d'auke shi ta kai shi wani wajan shiyasa ya nemi mafita tun da wuri. Bai jima sosai ba ya kalle ta yace, "Dan Allah ki sake min murmushi da kika yi yanzu." Bata san lokacin da murmushin ya sub'uce mata ba ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na gode my love, Allah ya biya ki da aljanna."

"Baka amsa ba na gaishe ka" ta furta a hankali.
"I'm sorry My love, murmushin da kika yi min a karon farko a rayuwa ta ya saka na manta duk abinda kika ce. Lafiya lau ya jikin ki?."
"Da sauk'i."
"Allah ya k'ara lafiya. Kiyi hak'uri na nemi wayar Baba lokacin da abin ya faru ban same shi ba, ina can hankali na yana kan ki Rauda duk da tarin aiyukan da suka min yawa."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now