ZAZZAFAR KAUNA 01-10

726 15 2
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Page na kune masoyana a duk inda kuke ku sani nima Ina sonku kamar yanda kuke sona🥰*

*1-10*

*CIGABAN LABARIN*

Kuka kawai Beauter take ta daura kanta a saman cinyar Ammie tana kuka,komai ya dawo mata sabo fal kamar yanzun komai ya faru haka take ji..tunda Haidar ya fasa aurenta bata taba jin tsanarshi irin yanzun ba tabbas Ahmad ne silar faruwar komai...Amman Haidar shine *SANADI* shine yayi sanadin shigowarta duniya...Da ace bai fasa aurenta ba da yanzun tana gidanshi a kwalkwashin inuwar aurenshi,Amman ya rushe komai yayi sanadin komai ya ruguza komai.

Dago kanta Ammie tayi tana cewa.."kukan ya isa haka Daughter karda kanki yayi ciwo." Share mata hawayen tayi tana cigaba da cewa.."touching heart story! and kuma haka Allah ya qaddara daman haka kika rubuto Daughter in Sha Allah komai yazo karshe ya zama labari...sai dai ba zan matsa maki ba akan aure sai dai inason ki zauna kiyi tunani Daughter ki sani darajar y'a mace dakin mijinta."

Daga kai Beauter tayi bata ce komai ba sai sauke ajiyar zuciya da take..Dad ne ya sauke ajiyar zuciya yana cewa.."Hauwa tashi kije ki kwanta dare yana yi."..To tace tana tashi ta shige room din Ammie tana fadawa wanka,bayan tashin Beauter Dad ya kalli  A Kadir  yana cewa.

"Kaji dai abunda ya faru da Hauwa'u nasan waye Kai nasan abunda zaka iya da wanda ba zaka iya ba, duk da ba'a yabon d'an yau amman ni nasan waye Kai ka rike wannan yarinyar amana ka sata farinciki ka mantar da ita kuncin da Ahmad da Haidar suka sata nasan zaka iya, abu d'aya zaka yi yanzun ka samu ta anshi soyayyarka shine gaba."

"In Sha Allah Dad,zanyi iyakar kokarina da yardar Allah."

"Allah yasa."

*Nigeria 🥀*

Koda yazo bakin gate danna horn yayi mai gadi ya wangale masu gate yana tura hancin motarshi a cikin babban compound din gidan...da yake babban compound ne wanda zai iya daukar mota saman da goma banda idan kaje dai dai apartment dinka nan ma mota sama da hudu ko biyar za'a parka ta...dai dai apartment dinsu yayi parking din motar yana kashe mota ko kallonta baiyi ba ya balle marfin motar ya ficewarshi ko inda take bai kalla ba.

Da harara ta rakashi tana goge guntayen hawayenta ta fito itama tana tura marfin motar da karfi,duk da yaji yanda ta kulle motar kamar yak'i amman bai ko waigo ba balle ya nuna yasan tana yi,fuuuuu haka take tafiyar sai wani hade fuska take kamar yanda shima yake hadewa bude kofar yayi yana shiga bakinshi dauke da sallama.

Har zata shiga yayi sauri ya riketa yana zabga mata harara da kallon banza yana cewa.." idan kika kuskura kika shigar man gida bakiyi addu'a ba sai nayi ball dake a cikin daren nan stupid marar wayau."

Fisge hannunta tayi daga rikon da yayi mata tana tsayawa tayi addu'a sannan ta shiga ko sallama batayi  a fili ba ,sai dai a zuciyarta tayi ko tsayawa kallon tsaruwar parlon batayi ba ta nufi wani room tana murdewa ta shigewarta ta na bango kofar...Tsaye yayi yana kallon kofar da ta shiga can yayi tsaki tana kwafa yace.

"Zan yi maganin wanann rashin kunyar taki soon useless."

Tsaki yayi yana kulle kofar gidan yaje ya ajiye mata leda a bakin kofar da ta shiga ko nocking baiyi ba balle yace fito ki dauki leda, ya juyo ya hayewarshi sama ya samu dakin da yasan nashi ne ya shiga.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now