ZAZZAFAR KAUNA 141-150

199 9 14
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*141-150*

Driving yake yana dan satar kallonta a kai a Kai,so yake yayi mata magana amman yana tsoro saboda ba ta bashi fuskar da har zai iya yi mata magana ba,har mamakin yanda yake tsoronta yake ganin idan har bai yi da gaske ba to ba zai tab'a iya yi mata maganar da yake son yi mata ba kuwa...daurewa yayi yana dan gyaran murya ya kira sunanta,bata ansa ba kuma bata kalle shi ba,sake kiranta yayi a karo na biyu nan ma shuru tayi mashi dan kallonta yayi yana cewa.
"Jidda."
D'agowa tayi tana mashi wani kallo tace.."lafiya dai ko.?" Murmushi yayi yana cewa.."lafiya ba lau ba Jidda." Dan shuru yayi sai ya cigaba da cewa."ki taimakeni dan Allah Jidda." Dan karamin tsaki tayi yanda ba zai ji ba,ita fa surutun da ta guda kenan shiyasa taki biyo shi bata son naci da kunata,shi kuma nacin tsiya gare shi sai kace wani maye turo baki kawai tayi tana k'ara maida kanta gefe bata ce mashi komai ba.

Furzar da iskan bakinshi yayi yana mai cigaba da cewa.."ya kamata ace kin gane irin son da nike maki Kulu,ya kamata ace kin tausayama kuma kin yantani,kin maida komai ba komai mun cigaba da soyayyarmu kamar da,dan nasan yanda nike sonki kema haka kike sona please Jidda wallahi na hukuntu iya hukuntuwa ki duba man I beg please SP."

Girgiza kai kawai tayi sai kawai tayi murmushi har yau har gobe tasan babu son shi ko digo a cikin zuciyarta,da dai kam tabbas ta so shi tayi mashi son da ashe shi ba irin shi yake mata ba,tayi mashi so iyakacin gaskiyar ta a da tana jin tabbas idan har babu shi ba zata iya rayuwa ba kamar yanda shima yake nuna mata ashe duk karya ce yaudara ce,ba sonta yake ba jikinta yake so yana wani depend da wai kishi.kishin bazan har da wofi mutun da yakita lokacin da take bukatar shi.

Wani irin kuka da hakuri ne ba ta bashi ba a lokacin,babu hakurin da ba bashi ba har cewa tayi ya aureta zata za mai mashi baiwa yar aiki ya auro wata,ita dai kawai aurenta take bukatar yayi dan kawai tana son ko ganinshi tayi taji dadi,amman yace shi bai son ganinta baya bukata sam and shi maganar gaskiya ba zai iya auren karuwa ba,abunda ya dunga ce mata kenan maganarsu ta karshe da shi wanda itace sanadin barin gidansu ce mata yayi.

Shi ko ya aureta yana iya kashe ta saboda tsanar da yake jin yayi mata and yana nadamar saninta da yayi har yayi soyayya da ita karda ta sake kiranshi idan har kuwa ta kuskura ta k'ara Kiran shi sai ya kira Baba yace ya jama mata kunne ta bar Kiran shi idan kuma shi ke sata zai gaya mashi yama daina dan shi ba zai auri karuwa yar iska ba.
Wannan maganar da ya gasa mata yasa taji komai ya fice mata a rai bata son komai bata bukatar komai da kowa a rayuwarta zata je inda ba wanda ya santa tayi rayuwarta ba wanda yasanta balle har ya ce mata karuwa.

Sauke numfashi tayi tana cewa..."Yaya Haidar tun wuri kasan yanda zakayi ka fita daga rayuwata Ina ganin girmanka da mutuncinka ni da kake gani nan cikakkiyar karuwa ce mai lasisi kuwa kuma ba mutunci gare ni ba tsaf zan wankeka tas and ka manta da bakinka kace baka iya auren karuwa?to yanzun mai zakayi da karuwa yar'iska mai bin saurayi tana watan ni a wajen shi.?"

Har ya bude baki zai yi magana ta d'aga mashi hannu ta cigaba da cewa.."dakata man Haidar dan Allah bari kaji fa nifa nan wallahi ba zan tab'a aurenka ba da na aureka na gwanmace na Kara shiga duniya a karo na biyu kaji ma na gama maka,kuma wai ba kayi aure ba?to kaje kaji da matarka nima ka barni naje da wanda yasan mutuncina da martabata and ka barni na auri maisona tsakani ga Allah ba dan wani kyauna ba ko kuma surar jiki yana sona ne saboda da Allah dan haka kaji tun dare bai maka ba kasan nayi karda ka sake yi man maganar wani na soka har yanzun akwai sona zuciyarka."

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now