ZAZZAFAR KAUNA 221-230

187 6 3
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://whatsapp.com/channel/0029Va9zjzE84OmE1ogwXn2I

*221-230*

A hankali ya daura bakinshi saman wuyanta yana kissing din ta da kuma sinsinata yana shakar kamshinta.. lumshe ido yayi yana budewa a hankali ya waigo da ita suna kallon juna ido cikin Ido,kallon zan mutu idan bake suke ma juna kwayar idonsu kawai zaka kalla ka gane sunyi nisa a kogin son juna..sun dade suna aika ma juna sakonni ta cikin idanu sannan ya k'ara hug dinta tight very tight yana cewa a hankali.."gaya man sunan turarukan nan naki Kalbi? please ki gaya man Ina kika samosu Kai ni wajen da kika saya na ba wanda ya sayar maki dashi kyauta..ki yarda dani ina bala'in son wannan kamshin naki yeah I love it so much Kalbi."

Kwantar da kanta tayi tana cewa cikin saukin sonshi da kaunarshi tace.."Hubby Kai ne sirrin komai nawa,ki sani komai nike yi dan kai nike yi shi domin kuwa ka gama zama bango a rayuwata Kaine jigon rayuwar Zulaihat sai da kai Zulaihat take gane komai sai da kai Zulaihat take sanin dadin duniya..kamar yanda kamshinka yake saka ni natsuwa da wani sauke marar musaltuwa Hubby Ina kaunarka."

Kallon juna suka dan yi suna sakar ma juna murmushi can kuma suka fara kissing mouth to mouth kamar zasu cinye junansu haka suka koma..daga tsaye suke tsotsar bakin juna suna shafa ko wani sako na jikinshi sun dad'e a haka sanann ya shureta bai direta ko Ina ba sai saman gado..dakyal ya lalubo switch ya kashe hasken dakin suna lulu duniyar da idan suka shigeta mantawa suke da a Ina suke..dan dukansu zakewa suke suna nuna ma juna babu wani bayan kai,suna mallaka ma juna zuciya da kuma rayuwa ma baki d'aya suna jinsu a wata duniya sun lula sun tafe haka suke ji.

Washe gari bayan sun tashi tare sukayi wanka suka shirya suka samu abunda suka saka ma cikinsu duka k'ara yin shirin tafiya school Kuma yau Zulaihat zata fara exams din ta final year..ba karamin kyau sukayi ba kallo d'aya zaka yi masu ka gane suna cikin kwanciyar hankali da kuma natsuwa,kallo d'aya zaka yi masu kace wa'annan masoyane kuma sun dace da junansu.

Yanda suke nuna ma juna taitali da kulawa a gaban kowa zai Kara burgeka ya baka sha'awa..zama da masoyi yafi komai dadi amman idan akayi dace da masoyi nagartaice na gari wanda zai dauki damuwar matarshi tashi ce haka itama matar,wanda zasu zauna zaman amana ba cuta ba cin mutunci to tabbas su Najeeb sun Kai duk inda kake tunani har ma sun wuce a fagen so da kaunar da suke ma junansu.

Dan kuwa sun sauke duk wani girman kai da son girman tsiya duk babu su yanzun a tare da su kuma babu yar'ramuwa sun bude sabon shafin rayuwa dan rayuwa suke gudanarwa mai cike da salo mai tsayawa a zuci da kuma bargewa...kuma tana bashi girman shi tana respected din shi sosai bama kamar inda suna makaranta baka tab'a cewa sun san juna idan har suna class.

Daman ba kowa yasan suna da alaqa ba sai Zubaida da Baby shiyasa ba ruwansu da wani sa idon students..yanda yake tambaya ya tada wanda ya gadama haka yake tadata mudun Allah ya qaddara sai an tadata..kuma zata tashi ta bada ansa cikin natsuwa da kamun kai daman ba da kowa take harka ba a school din daga Zubaida sai Baby.

Su ukku suke komai nasu daman Baby tayi aurenta ta auri saurayinta Kamal suna shan soyayyarsu suma kamar ba gobe..idan suna son su sha dariya sai su tuno baya suna jan Zulaihat irin rayuwar da sukayi a baya ita da Najeeb kamar ba su ba sai dai tayi dariya.

Cikin sati biyu suka gama exams Allah yayi ya yarda Zulaihat ta gama degree kamar wasa shi Najeeb har mamaki ma yake gani yake kamar a mafarki duka duka yaushe taje hundred level gashi har ta gama..bayan sun dawo gida sai tsale take tana rawa gabanshi duk murnar gamawarce yana zaune sai kallonta yake yana murmushi dan ba karamin kyau rawar take mata ba.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now