ZAZZAFAR KAUNA 121-130

203 9 4
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*121-130*

Bayan kowa ya fito daga kotun ana shirin tafiya da Ahmad ya kalli dan sanda da ya rike shi yana hawaye yace."Officer dan Allah Ina son kayi man alfarma d'aya kafin a tafi dani prison please." Tsaki Officer din ta buga yana buga mashi harara dan wani irin haushin Ahmad yake ji,dan shi ba haka yaso hukuncin ya kasance ba. yaso ace kotun musulci a ka Kai shi yanda yayi Zina da aure a kan shi a yanke mashi hukuncin kisa ai an rage mugun iri,dan barin mai hali irin na Ahmad a doron k'asa masifa ne babba.
Cigaba da jan shi officer din yayi babu ko tausayi cikin kuka Ahmad ya k'ara cewa.."Dan Allah officer kayi hakuri kayi man wanann alfarmar officer." Dakata Officer yayi jin yanda yake kuka sai yaji ya dan bashi tausayi kadan,tsayawa yayi yana kallonshi fuskarshi babu annuri a cikinta yace.

"Maiye alfarmar.?"

Sauke numfashi Ahmad yayi yana share hawayen shi yace. "So nike ka bani dama zan yi magana da Jidda." Wani kallo Officer ya watsa mashi yana jan tsaki yayi gaba,gani yake sam Ahmad bai da kunya ma har yana da idon da zai iya had'a ido da Jidda,yarinyar da yaci mutunci ya wulakanta babu Imani babu tausayi tabbas mutun mugun dutse...dan tirjewa Ahmad yayi yana cewa.."Dan Allah yallabai kayi hakuri ka barni Ina son nayi mata magana kuma maganar tana da mahinmamci sosai a wajena har da wajen ta ma."

Dakata kawai officer yayi bai ce komai ba,sai kuma ya tafi da shi wajen Jiddarh yana kallon shi yace.."5mn na baka." D'aga kai yayi yana cewa."Nagode sosai." Mai da kallonshi wajen Beauter yayi sai kawai ya fashe da kuka yana girgiza kai kuka kawai yake can kuma ya dan dakata da kukan da yake yana hade hannayenshi waje d'aya yana kallonta yace.

"Ban san da wani baki zan nemi gafararki Jidda,tabbas ban canci ki yafe man ba dan na cuceki na zalinceki Ina neman afuwarki ki yafe man tabbas nine mafarin komai na biye ma rudin shedan kuma na biye ma zuciya da kuma kishinki da nike da naga kin ki bani dama kin ba wani har kuna yawo duk inda kuka gadama tare kuna irin soyayyar da na bukaci muyi dake kika ki bani dama ,dalilin da yasa har nayi maki haka dan na huce takaici na huce daga hushina,gani nike abunda zan maki Kenan da zan huci daga hushina sai da nayi maki abun ya damaini ki yafe man."

Ko kallon shi Jidda batayi ba dan bata son ganin shi balle kuma taji amon maganarshi,kaf duniya bata wanda ta tsana sama ga Ahmad to daga shi sai Haidar dan wa'annan mutane biyu bata jin zata tab'a yafe masu dan ko wane da irin rawar da ya taka wajen ganin bayan tata rayuwar.

Ganin bata da niyar yi mashi magana officer ya kad'a kan shi ya shigar da shi a cikin motar police,kaf wajen babu wani nashi dan ba wanda ya hallaci shari'ar...tabbas yasan duniya ta juya mashi baya ace a kawo shi kuto ba wanda yazo nashi balle ma har suyi bankwana da nashi ko su Nana ba'a zo da su kotun ba balle har ya gansu ya dan ji sauki yace ya ga jinin shi.

Bayan sun dawo gida nan suka zauna suna mai da yanda akayi nan Dad ke gaya masu tun da har an gama komai to su gobe zasu koma gida saboda sun baro aiki a campany..ba haka su Baba suka so ba,dan sun so suyi masu Koda sati biyu ne ko kuma d'aya,amman tunda har sun kawo uzurinsu na sun baro aiki ba yanda zasuyi ai suna da uzuri.
Sallah ce ta tada su mazan suka tafi massalaci su kuma matan suka shiga dan yin sallah,bayan sun gama sallah Jidda da Meenat suka shiga kitchen suka girka masu abinci dan tun breakfast ba wanda ya k'ara cin abinci.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now