ZAZZAFAR KAUNA 111-120

155 6 3
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*111-120*

"JIDDA.!" A tsorace yake maganar mai da kallon shi wajen mahaifinshi yayi da ya kwafe shi da ido,maido kallon shi wajen Jiddarh yayi yana Kara tabbatar da yes itace fa,yaushe ta dawo? Mai hakan ke nufi? Ta gaya ma iyayenta gaskiyar abunda ya faru kenan,wata uwar zufa ce ta keto mashi tun daga kan shi har zuwa kafafun shi..kirma ce ya fara yi yana girgiza kai can kuma ya nufa hanyar fita da sauri har ya bude kofar fita Alhaji Bala yace.
"Karka sake ka fita daga cikin dakin nan Ahmad maza dawo."
Da baya baya Ahmad ya dawo yana girgiza ma Jidda kai rayuwarshi ba abunda ya tsana kamar mutuncin shi ya zube a idon iyayenshi da kuma matar shi da yake bala'in so da kauna,yasan tabbas asirinshi ya tonu karshen zamanshi da ita yazo karshe yanda take da kishin bala'i and kuma shi ba zai iya rayuwa babu matar shi ba.

Zama yayi yana maida kan shi k'asa saboda da wani wawan kallo da Dad ya wurga mashi suna had'a ido, lokacin sanyi ne dan dukansu jikinsu kayan sanyi ne amman duk sanyin da ake shatatawa bai hana zufar da ke jikin Ahmad diga ba...yama rasa mai zaiyi jin Baba yayi gyaran murya yana kallon Jidda yace.

"Jidda."

D'ago kanta tayi tana kallon Baba sai kuma ta maida kanta k'asa tana share hawayenta...can kuma tace.."Na'am." Alamu yayi mata da ta share hawayenta d'aga kai tayi tana share hawayen sanann Baba yace.

"Gaya ma Alhaji Bala abun da kika gaya mana da Ahmad yayi maki,ban ce ki boye mashi Komai ba."

D'aga Kai tayi ta fara gaya mashi irin cin kashin da Ahmad yayi mata cikin kuka take gaya masu ,ita da zasu biye mata da sun bar tambayar ta dan bata son ana dawo mata da wannan abu a rayuwarta tabone dai yayi mata kuma ta bar shi ga Allah dan shine kawai zai saka mata.

Cikin karma da hajijiya Alhaji Bala Mato ya shako Ahmad yana wanka mashi maruka,can ya fashe da wani kuka yana nuna shi da yatsa magana yana son yayi amamn ya k'asa...can sai ya zube k'asa yana aman jini da gudu Ahmad yayo kan shi yana rushewa da kuka yana cewa.

"Innalillahi wa'innalaihirajiun! Baba! Baba! Baba! Na shiga uku na lalace wayyo Allah Baba dan Allah ka tashi karka mutu ka barni cikin masifa wallahi tsotsayine ba hali na bane."
Wajen Alhaji Bala su Baba sukayi suna d'aga Ahmad daga saman shi suka yi waje da shi... direct asibiti akayi da shi dan bashi taimakon gaugawa.

★★

*ABUJA 🥀*

Yau da wuri ta shirya bata yarda ta b'ata mashi lokaci ba saboda tana tsoron karda yayi mata irin na jiya yaje ya kasheta a banza yayi ma Umma asara..daman ta lura abunda yake fata kenan yaga bayanta kuma ta Allah ba tashi ba dan ta riga shi fadin Allah.

Yau ma dai ta shafa poder sai dai bata shafa ma bakinta komai ba kuma doguwar rigar material ta saka ta saka hijab dinta ta fito ta zauna parlo tana jiran fitowarshi...yana sane yaki fitowa dan shima sai ya rama b'ata lokacin da tayi mashi jiya,zaune yake saman gadon shi yana duba wasu file da Moha ya turo mashi jiya na makaranta.

Yana sane da 10 gareta kuma Moha ne zai daukesu kuma yasan Moha bai da sauki shima idan har ta makara hanata shigowa class din shi zai yi ba ruwan shi da wata sanaiya,tun da aikin shi yake kuma zai yi komai ne tsakani ga Allah.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)On viuen les histories. Descobreix ara