ZAZZAFAR KAUNA 201-210

215 9 6
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*201-210*

"Wallahi ba inda zaka je,ko kafar gida ba zaka fita ba balle har ka fita wani waje." shuru tayi tana kama kuhu sai wani girgiza zawa take, murmushi yayi yana kallon yanda take wani hura hanci sai kace idan ya gadamar fitar tana iya hanashi murmushi ya sakar mata yana k'ara gyara zaman hular kan shi yace.."Amman wasa kike ko.?" Banza tayi da shi bata ce mashi komai ba,Shima bai sake kallonta ba ya nufi hanyar fita hankalin shi kwance..kukan Kura tayi tana tsale ta haye saman shi tana makalkaleshi gami ta zagaye hannayenta a wuya shi tana daura bakinta dai dai satin kunnenshi ta sakar mashi wani softkiss  tana cewa a hankali.

"Ba wasa nike ba,ba inda zaka dan kai nawa ne ni d'aya nace nan nike da fada a zuciyarka,ya kake son nayi maka ne wai Mr Man.?" K'ara sakar mashi da wani kiss din tayi tana dan tsotsar kunnen kadan tace. "Tell me please mai zan maka wanda zaka gane ka gama da zuciyar Zulaihatu?gayaman ya zanyi ka gane ba zan iya rayuwa babu Kai ba?Kaine rayuwata Kaine wanda nike so kuma nike kauna, believe me ba zan iya rayuwa ba babu Kai da Kai nike son rayuwa har *DA'IMAN ABADAN* I love you I love you very very much Hubby."

Kuka ta fashe mashi da shi tana cewa.."I can't ba zan tab'a barin ba ba zan iya ganin kana tare da wata ka yarda da ni zan iya mutuwa mudun har hakan ta kasance so da kaunar da nike maka ya wuce duk yanda zan gaya maka su dan Allah ka hukuntani ta ko wace hanya amman banda kula mata ba zan juri wanann hukuncin ba."

Zagayo da ita yayi gabanshi yana mai share mata hawayen fuskarta kamar yanda shima hawayen ne a saman fuskar ta shi..bai san ya zai misalta farincikin da yake ciki a yau ba,baki ba zai iya furtawa ba ganin taki barin kukan kamar yanda yake bukata ya nufi da ita saman kujara yana mai had'a bakinsu waje d'aya yana mata wata irin tsotsa .

Yanda yake kissing dinta kadai zai tabbatar maka da irin son da yake mata ba karami bane yana sonta yana kaunarta tun bai san sonta yake ba har ya gano ita ce dai lifepartner din shi,tuni ya yarda da ba zai tab'a moruwa ba idan har bata a kusa da shi...ya yarda dace itace Apple of his life ya yarda ya yarda  da shi so ba ruwanshi da Kai waye ba ruwanshi da wanann bai tab'a tunanin zai yi ma dallibar tashi irin son da yake mata ba.

Yana dad'e yana tsotsar bakinta sai da ya tabbatar da tayi shuru ya d'ago kanta yana mai hade kansu waje d'aya suna shakar numfashin juna sosai murmushi ya sakar mata yana cewa a hankali kamar yana ra'da yace..." I really love you Kalbi." Dan shuru yayi yana mai cigaba da cewa..."Zulaihatu ba zan taba iya had'a soyyyarki da wata ba,dan nasan ko na had'a ba zan tab'a yin adalci ba a tsakaninku,dan sonki a jinina yake,Ina sonki tun ganin farko da nayi maki lokacin kuna level one kunzo wuce kina kuka ke da Zulaihat."

Shuru yayi yana jan hancinta kadan ya cigaba da cewa.."a lokacin ban san sonki nike ba nasa dai kawai tausayi ne duba da duk ganin da zan maki cikin kuka nike ganinki..kullun ina mamakinki sosai yanda kike kuka kika maida kuka abokinki baki da abun yi sai kuka,ni kuma wanann yawan kukan naki na banza sai na fara jin haushinki na kuma sama raina sai nayi maganin kukan nan naki."

Kallonshi kawai take sai kuma ta weaving face din shi tana cewa.."ya kuma kayi shuru?ya akayi ka san sunana?kuma ya akayi kasan gidanmu.?" Kama hannun yayi yana murzawa a hankali yana cewa.."Ina kallon beautiful face din Matata kuma hasken idaniya I love you da sonki zan bar duniya." Dan shuru yayi yana cigaba da cewa.."lokacin dai Ina sane da duk wani motsi naki a school ban manta captain dinku na tambaya sunanki ya gaya man full name dinki a ranar na haddace sunan a kaina...ina sane na kadaki course din na."

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now