ZAZZAFAR KAUNA 71-80

238 11 4
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*71-80*

"Dallah can Malama maza koma inda kika fito ki chanza dressing din ki." Kallon kanta ta dunga yi daga sama har k'asa sai kuma ta kalli gefe da gefe ko zata hango makusar shigar tata da yake cewa wai ta chanza....ganin bata ga aibun shigar ba ta mai da kallonta kanshi tana cewa.."Mai kuma wannan shigar tayi da har zaka wani ce na chanza ta.?" Cikin rashin kunya da fitsara tayi mashi maganar.

Kwafe ta yayi da ido kawai bace mata komai ba,sai ma mamakin karfin halinta da rashin kunyarta yake da kuma rashin tsoron Allah,in ba rashin tsoron Allah ba maiye ace tana matar aure ta dauki wannan gayun na kece raini ta kuma fita,bayan inda zata akwai maza mazan da ba maharramanta ba, tabbas ya yarda bata da hankali.

Ganin yanda yayi banza da ita ya kuma dauke kai ya maida ga tv sai ranta ya b'aci sosai wato  ga mahaukaciya tai ta yi ko? Ko kuma karya uwar haushi tai tayi,kwafa kawai tayi ta juya fuuuu ta shiga room din ta tsaki yayi yana bin ta da kallo yana cewa

"Stupid."

Can sai gata ta fito ta daura ma kayan hijab har kasa sai wani kumbure fuska take tazo gaban shi ta tsaya kam..sai da  ya mula ya sha iska ya d'ago yana kallonta daga k'asa har sama tsaki yayi yana cewa.

"Ai da saura."

Turo baki tayi tana Kara kallon jikinta ganin hijab ce to mai ye kuma sauran,nan ma fuuuu ta Kara juya ta shiga room ba'a dad'e ba ta fito sai wani kumburi take kamar yeast.

Kashe kallon yayi yana kallon fuskar yanda take turmuke sai wani busar kamshi take ganin ta wanke fuskar ba sauran kwaliya ko digo a sama ga kuma hijab da ta saka har kasa sai yaji dan dama dama duk da dai da son samune to ba inda zataje balle har wani gardin kwato ya kalle mashi mata.

Tashi yayi yana yin gaba bai ce mata komai ba..bin bayanshi tayi sai kumbura take tana hawa shiga mota yayi yana worming din motar yana kallonta..ganin bata da niyar shiga ya dannan ma gateman horn yana niyar ficewarshi ganin da gaske yake tafiya zai yi ya barta ya ta bude bayan mota ta shige sai wani cin magani take.

Ko kallonta bai yi ba ya danna hancin motarshi ya ficewarshi daga gida ,yanda yake ba motar wuta sai kayi tunanin garin baki d'aya zasu bari,dan ba d'aga ma motar yake ba wuta yake bata dan so yake kafin 30mn ta ida tayi mashi a cikin school.

Tsoroce take dan ba abunda take tsoro a rayuwarta sama da tsawa sai kuma gudun mota,tana tsoron aita falla gudu da ita a cikin mota kamar rai din biyu ne ba d'aya ba , shiyasa bata cika hud'a da mota ba..ta gwanmace ta hau naped itama naped din bata yarda aita falla gudu da ita ba dan hankalinta baya kwanciya har sai taga ta sauka sanann.

Ganin gudun ba mai karewa bane, ta rintse idon ta har bata san adadi ba haka ma salati tayi shi yafi cikin kwando wani taka burki da yayi yana yin reserve duk a lokaci guda bata san lokacin da tayi tsale ba ta koma gaban mota tana makurewa waje d'aya.

Hawayene kawai taji suna zubo mata sai kuma addu'a da ta kamayi tana Allah Allah taga sun isa makarantar saboda a rude take sai taga makarantar tayi mata nisa sosai.

Babu inda baya karma a jikinta tsabar tsoro,lura da situation din da take ciki da yayi sai ya kara ma motar wuta dan yaji dadi da yaga ta firgice daman ta Kai shi makura ta Kai shi karshe dan rashin kunyarta ta isheshi over and over ma.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now