ZAZZAFAR KAUNA 21-30

222 6 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*21-30*

Karfe goman dare jirginsu ya sauka a Aminu kano airport,bayan yan lokacin passenger suka fara fitowa,a hankali take taka matakalar benen jirgin ta na ida saukowa a filin jirgin ta lumshe Ido tana sauke ajiyar zuciya,shakar iskan wajen tayi tana furzarwa a hankali ta bude idonta a hankali ta sauke a saman fuskar AK da yake tsaye tana sakar mata da murmushi,itama murmushin ta sakar mashi tana cewa.

"Yau gani a kano."

D'aga mata kai yayi yana kamo hannunta a hankali yace.."Yaushe rabonki da taka kafarki a wannan wajen.?" Langwabar da kai tayi tana wasa da yatsan hannunshi tace.."four years back."

Jan hancinta kawai yayi suka bi bayan su Ammie dan har an gama zuba kayansu a booth suka shiga mota  su ka dauki hanyar GRA,Dan a nasarawa zasu kwana washe gari sun dauki hanyar jigawa saboda yanzun dare yayi ga kuma matsalar tsoro da ake fuskanta balle su doshi hanyar dutse a cikin dare.

Koda suka isa gida masu gadin gidan suka kwashe kayan suka shigar masu da shi ko zama basu yi ba kowa ya shigewarshi dakinshi dan watsawa saboda gajiyar da suka kwaso...Koda ta shiga room din Ammie tace ta shiga need ta tadda dakin sai kace ana rayuwa a cikinshi komai gyare yake a cikin dakin,ga dakin yayi masifar bala'in kyau komai na cikin dakin milk ne ba karamin kyau dakin yayi ba,bayan ta gama k'arema dakin kallo ta fada toilet tayi wanka ta dauro alwallah bayan ta fito ta shafa cream ta shirya cikin doguwar rigar bacci ta zura hijab tayi sallah sannan ta fashe turare ta kwanta dan bacci ne fal a idonta ga kuma yar yunwa tana jin amman baccin ya danne yunwar.

Bayan sun fito parlo suka zauna a dining zasu ci abinci, Jidda suka tsaya yi shuru bata fito ba,5mn Ammie taga tayi ba taga Jidda ta fito ba,  ganin  bata fito ba sai ta tashi ta shiga taga ko lafiya.

Tsaye Ammie tayi tana kallonta sai kuma ta saki murmushi tana karasawa a jikin gadon ta zauna,tana kallon yanda take bacci duk gashi ya rufe mata ido bacci take cikin kwanciyar hankali dan a hankali take fitar da numfashi take wani murmushi Ammie tayi tana yaye mata gashin da ya rufe mata fuska tana Kara gyara mata kwanciyarta a hankali tace.

"Allah yayi maki albarka."

Kashe mata hasken dakin tayi ta kuma tofe ta da addu'a tana fitowa ta dawo wajensu kallon Dad tayi tana cewa.."Ashe bacci take." Murmushi Dad yayi yana cewa. "Ina ruwan Hauwa'u,ai dole ayi bacci angaji sosai balle ita ba sabawa tayi da tafiya mai tsawo irin wannan ba." Murmushi AK yayi yana cewa.."Gaskiya kam Dad dan tunda taje Ukraine bata sake matsawa ba kullun dai tana cikin rabon da ta hau jirgi wai shekara hudu kenan."
Zaro Ido Ammie tayi tana dariya tace .

"Kaiiii Luv Anya kuwa babu sheri a maganar nan taka.?" Kwabe baki yayi yana saka tsokar nama a bakinshi a hankali yake taunawa kamar ana mashi dole dan shi a duniya ba abunda yake mashi wahala kamar tauna abinci..ba abincin bane bai son ci ba A'a kawai dai taunashi yake mashi wahala shiyasa sai ya hakura Koda yana jin yunwa sai yasha milk ko kuma yogurt.

Sai da ya hadeye sannan ya kalli Dad yace.."Dad kaga Ammie ko?bayan ita ta gaya man da kanta kuma sai Ammie tace haka." Dariya Dad yayi yana cewa.."rabu da ita naga alamun so take su hademana kai su nuna mana banbanci." Kwabe fuska kawai ya Kara yi yana turo baki murmushi kawai Ammie tayi tana cigaba da cin abincinta tayi kamar bata san suna yi ba.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now