ZAZZAFAR KAUNA 241-250

243 4 4
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXp

*Wannan page sadaurkarwa ne ga duk wani masoyina da wanda na sani da wanda ban sani ba ku sani inajin dadin yanda kuka nuna ma kauna wajen karanta DA'IMAN ABADAN bansan da wani baki zan maku bayanin dadin da nike ji ba.*

*241-250*

Zaune ya taddata a parlon tana tsakular indomien ko ci bata yi ba,zama yayi yana maidota saman cinyarshi ya kalleta cikin so da kauna yace.."Kalbi." D'agowa tayi tana kallonshi can kuma ta sakar mashi murmushi tana lefewa jikinshi,kara tight dinta yayi a jikinshi yana dan shafata a hankali yace.."ya naga baki ci indomie din ba.?" Shuru tayi sai kuma ta turo baki tana cewa.."ji nayi ta fice man a rai Hubby."

Kallon indomie din yayi sai kuma ya d'agota a hankali yana cewa.."daure kice please kinga bakiyi dinner ba." Dan turo baki tayi tana girgiza mashi Kai tace. "A'a Hubby ko kallonta ban son nayi tada man zuciya take sosai."

Kallon yanda indomie tayi kyau a Ido kawai yake Ina ga ta shiga a baki ya testing dinta zai kasance?amman ita tace wai ma tada mata zuciya take murmushi yayi yana shafa lafaifen cikinta da ba za'a akwai ajiya a cikin shi ba,kissing din cikin yayi yana cewa..."Babyn Hubby mai yake bukatar ci?Dan ba zan barku ku kwana da yunwa ba."

Shafa kan shi tayi tana cewa.."Dan wake Hubby da manja da yajin tafarnuwa a yanka albasa da su kwai harda cabbage ma." Galala yayi yana kallonta shi Ina zai samo mata wani danwake cikin daren nan?karfe sha biyu fa na dare kuma ga irin garin da suke bai san a ina zai samo wani danwake ba..kwabe fuska yayi yana cewa.."Kalbi danwake fa kika ce.?" D'aga mashi Kai tayi tana cewa.."Eh Hubby idan banci ba ji nike kamar na mutu."

Rufe mata baki yayi yana girgiza kai yace.." ba zaki mutu ba,karda ki sake cewa haka kina son zuciyata ta buga.?" Girgiza mashi Kai kawai tayi cigaba da cewa.."kin san kece komai nawa kice rayuwata ba zan iya yin komai ba idan baki dan kinbi kin mallake lungu da sako kice sarauniyar zuciyata Ina sonki ina Kaunarki Kalbi take care bari naje na samo maki and da danwaken sai kuma mai.?"

Dan shuru tayi sai kuma tace.."Zobo amman na gidan Ammie wanda nasha dazun yana man dadi Hubby ka taho man da shi." Zaro Ido yayi waje yana cewa.."ranki ya dad'e Gimbiyata bari naje Allah yasa basu kwanta ba..koma sun kwanta na tadasu dan ba zan yarda ki kwanta ban baki wanann zobo ba I love you Kalbi."

A hankali tace.."I love you more Hubby please kayi sauri yunwa nike ji sosai." Daukarta yayi ya kaita room yace ta bashi minti goma yanzun zai dawo. Sai da ya k'ara kissing din ta sanann ya bar gidan,wasu eatry ya shiga wanda yake da assure din samun dan wake amman duk bai samu ba sun k'ara haka ya kama yawo a cikin garin Abuja har Allah yasa ya samo danwake a wani eatry shima ba wani mai yawa bane sosai.

Agogo ya kalla yaga har d'aya na dare ya kusa kuma yasan tana can tana jiranshi tin da tana son cin danwaken kuma tana jin yunwa cikin daren ya kira Khalid yace yaje ya dauko mashi zobo a apartment din Ammie ya kawo mashi yana kofar gida.

Kafin ya iso gidan har Khalid ya dauko yana dan jiran shi bayan sun gaisa ya anshi zobo ya nufo gida cikin wuta² dan bai san yunwa ta kamata ita da abunda ke cikin cikinta..yana shigowa ya tadda Moha tsaye yana magana da gateman bayan yayi parking ya fiddo da order din da yayi da kuma zobo ya mika ma Moha hannu yana cewa.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now