ZAZZAFAR KAUNA 61-70

171 5 5
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan audio su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*61-70*

"Zulaihat." Murmushi ya saki yana girgiza kai sai kuma ya mike tsaye yana kashe komai ya shige room,wanka yayi ya kwanta yana tunanin duniya yana tunanin yanda komai ya chanza ya juye...komai ya juye ya chanza ya zaman mamaki da kuma al'ajabi har yau har gobe yana mamakin yanda ta sauya ta chanza hali yana mamakin yanda har yarinyar ta iya kallon kwayar idonshi tana gaya mashi maganar da ta ga dama ta zo bakinta.

Juyi yayi yana cewa a hankali.."yaushe kika sauya kika zama haka Zulaihat?yaushe kika koyi rashin kunya? wata irin tsana ce kike man?tabbas zaki soni kuma zaki kaunace ke da kanki zaki kawo man jikinki da kanki zaki bukace ni wannan alkwarine.

Shafa lips din shi yayi sai kuma ya tashi yaje gaban mirror yana kallon yanda lips din yayi ja,saboda taunar da yasha murmushi yayi kawai yana koma wa ya kwanta ya lublube da blanket yana tunanin duniya bacci yayi gaba shi.

*WASHE GARI*

Koda ya tashi bai wani kalli ko inda room dinta yake ba,daman yana da lecture yau 8 ganin yanda lip din shi bai karasa hucewa ba yasa ya kira captain yace yayi holding din lecture din sai 12 ya gaya ma su.

Yana zaune yana shan tea Moha ya kira shi waya dauka yayi yana cewa.."Ya dai.?" Tsaki Moha yayi yana cewa.."Yanda akayi dan rainin hankali,Kai fa matsalarka kenan." Lumshe Ido yayi yana furzar da iska ya ajiye cup din yace.."Kai ne ke da matsala wallahi daga tambayarka lafiya sai ka hau ni da masifa sai ka saka man ciwon kai ina zamana."

Yanda yake maganar a hankali kamar bai wani lafiya Moha yace.."Najeeb are you okay.?" D'aga mashi kai yayi kamar yana gabanshi yace..Yeah." girgiza kai Moha yayi yana cewa.."Sure.?"again d'aga mashi kai yayi yana cewa ."sure."

Dan shuru Moha yayi yana nazarin shi sai kuma can yace.."daman na kiraka akan komawar su Darling school banji kace komai ba har yanzun." Tsaki yayi yana cewa.."wacece kuma Darling.?" Shima Moha tsakin yayi yana cewa.."Dallah can Malan ban sani ba,ban san wulakanci fa Kai daman haka kake wallahi ba'a maganar arziki da kai,wa zan ce ma Darling duk duniyar nan ban da Matata."

Tsaki Najeeb yayi yana cewa.."Sannu tamtabara uwar aure,da anyi magana sai kace mata mata sai kace Kai d'aya ne kake da aure a duniyar nan kafa ishe ni ahtoh."

Dariya Moha ya fashe da ita yana cewa.."Taya ba zan yi maganar Matata ba,bayan ita ke sama man natsuwa sann..."Moha." Ya katse Moha yana furzar da iska dan daman kan shi yana mashi ciwo a hankali ya bude baki yayi kamar ana mashi dole yace .

"Duka yaushe akayi resume din school din da har zasu fara zuwa,and kuma naga ai bama a fara yi masu lectures din ba ko?su bari sai Monday a samu drive yana kai su."

Zaro Ido waje Moha yayi yana cewa.."wani Drive zamu ba matanmu yana dauka sai kace babu zuciya a jikinmu?kalle mana mata fah zai kama yi and har magana nasan sai sun yi ko da sau d'aya ne,ni kuma hakan ba zan laminta ba gaskiya."

Shuru Moha yayi yana cigaba da cewa.."Amman idan zaka iya kai sai ka sama ma Zulaihat drive nidai kam da kaina zan dunga daukar kayana Ina kaiwa, kuma Ina dawowa da kayana hankalina kwance haba Ina ma zan iya."
Furzar da iska yayi yana jan tsaki yace.."naji sai kayi yanda kaga ya dace,wa zaka nuna ma kishi Malan zaka wani kama cika ma mutane baki."

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now