ZAZZAFAR KAUNA 151-160

182 14 14
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*151-160*

Tura office din Moha yayi yana shiga da sallama a bakin shi, d'agowa yayi yana ansa sallamar sai kuma ya ajiye pen din hannun shi yana kallon Moha,bayan Moha ya samu waje ya zauna suka fara gaisawa sai da suka gama gaisawa sannan Moha ya fara cewa..."Munyi magana da wannan yarinyar fa Najeeb." Murmushi Dr yayi yana cewa.."Gud ya kuka yi da ita.?" Gyara zama sosai Moha yayi yana kallon shi ya cigaba da cewa.
"Komai ya tafi normal yanda ya dace na kuma tsara sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba."
"Wani hanzarin kenan.?"
"Maganar waya ba da ita zaka dunga pretending din waya ba bcox kar da a shiga hak'in yarinyar kamar yanda kace tun farko shiyasa nayi tunani bayan na koma gida sai na yanke wani plan din."

Kallon karin bayani yayi mashi,kuma Moha ya gaya mashi duk yanda sukayi da Baby ba abunda ya manta bai gaya mashi ba, cigaba da cewa yayi..."kasan dawa yanzun Kai zaka dunga pretending din.?" Girgiza mashi Kai kawai Najeeb yayi yana murmushi,shi abun dariya ma yake bashi kuma Moha tausayi yake bashi kamar yanda yake tausayin kan shi,yasan wacece Zulaihat kuma yasan taurin kanta da yar'banzar zuciyarta kamar ta kafiran farko.

Shi yasan sam yarinyar ba son shi take ba kamar yanda ta ambata ,daga zuciya har baki haka maganar take bata son shi ta fito kuma yaga tsintsar gaskiyarta a cikin kwayar idonta..tabbas yana fatan sun sansanta sunyi rayuwa irin ta kowa sun nuna ma junansu so su taitala junansu su tairairayin juna su nuna ma juna zazzafar kauna...amman taya?yaji ya kuma yarda yana da laifi tun farko shine bai jata a jiki ba bai nuna mata taitali ba balle kuma so da kauna,ya dauka to yana son ta ba shi chain yana son ta bashi dama ta karshe ya nuna mata irin son da yake mata.

Yana son ta bashi Koda wata d'aya ne tal ya nuna mata matsayinta da girman da take da shi a zuciyarshi,yana son ta bashi dama ya bude mata zuciyarshi taga gidan da ta gina a cikin zuciyarshi ba tare da ita ta sani ba,shima  kasan shi bai sani na bai fargaba sai dai kawai yaji ginine wanda ba zai tab'a iya rushewa ba.

Tabbas yasan zata kaunace shi zata so shi zata riritashi,amman idan ta daure ta bashi chain na wata d'aya wata d'ayan ma yayi yawa shi sati d'aya ma is okay,amman idan zata daina yi mashi tsiwa da rashin kunya sune bai jin zai iya dauka a matsayin shi na mijinta ta dunga kallon idon shi ba kunya ba tsoro ta gaya mashi magana.

Abunda kuma ba zai dauka ba idan har tace zata cigaba da wannan bed behevoir din nata ba zasu tab'a shiryawa ba,ba zasu tab'a zama inuwa d'aya da ita ba,zaman su ba zai tab'a daurewa ba kuma ba dan bai sonta ba ,a'a dan rashin kunyar ne kawai zai rabasu shi dai ba zama zaiyi yai ta bugunta ba,balle ma da iliminta da hankalinta ba zata tsaya ta saki jiki ya kama wani bugunta kamar wata jakka..tabbas yasan ba zata yarda ba maganin ayi karda a fara. numfashi yayi yana ce ma Moha.

"Da wa zan dunga yin wayar."?

Dan shuru Moha yayi sai kuma yayi murmushi yana cewa.."Da Seemarh." Kallon baka da hankali Najeeb yayi  ma Moha sai kuma can yayi tsaki yana girgiza kai yana mamakin yanda komai za'ayi da Moha ba'a gamawa sai ya kawo shirme da hauka kamar wani yaro,shi gashi dai kamar ya fara hankali amman idan yayi wani abun sai kaji kamar ka tashi  kamashi Kai ta Mari ko kaji saukin takaicin da ya kunzuga maka,tsaki yayi a karo na ba adadi yana hararar Moha yace.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now