ZAZZAFAR KAUNA 41-50

203 6 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*41-50*

"Kee!Kee!Kee!." Wata zufa ce ta keto mashi har diga yaji yana yi tsabar hirgita kar dai ace yarinyar nan mutuwa tayi?take hawaye suka cika mashi ido..dan bai shirya rasa ta ba dan yanzun,ya zaiyi da rayuwarshi idan babu ita a kusa dashi?bayan itace farincikin shi itace rayuwarshi itace hasken idanunwanshi itace komai nashi..bai jin zai iya kallon wata mace da sunan so,hawaye zirr suka tsiyayo a fuskarshi yana mai k'ara girgizata yana cewa.

"Inalillahi wa'innalaihirajiun na shiga uku Zulaihatu."

Kuka ya rushe da shi a wajen yana daura kan shi a samanta can kuma ya k'ara d'agowa yana bubugata da sauri yana cewa.

"Wake up please Myluv i'cant do without you."

Rintse idonshi yayi jin zuciyar shi tana neman tarwatsewa ya ma rasa mai zaiyi ya kasa gane komai idanunshi sun kulle hankalinshi ya gushe daga jikinshi,bai yi k'asa a gwiwa ba ya sake yin kanta yana girgiza ta kamar wani zautaice yace.

"Maiyasa zaki yi man haka? maiyasa zaki tafi ki barni a lokacin da nike bukatarki?maiyasa kika k'asa gane irin so da kaunar da nike maki?maiyasa zakiyi man wanann yankar kaunar Zulaihatu?kece farinciki kice rayuwata,zuciyata ba zata iya jurar rashinki ba Zulaihatu farincikina komaina kece garkuwarsu Zulaihat rashinki babban bala'i ne a rayuwata ba zan iya ba Allah ka taimakeni."

Yabi ya rude bai ma san mai yake furtawa ba,kawai dai ya daura kanshi a samanta yana kuka yana subbatu dan ya gama zama wani zautaice ya dumauce surutu kawai yake yana amaye irin so da kaunar da yake mata.

Tun da ya shigo taji shigowarshi lamo tayi dan bata san ganin shi sam,sanmatarta yayi tana kokarin tashi ta koma room dinta kafin ya shigo sai kuma taji shigowarshi.

Sai kawai ta koma tayi kwanciyarta tana jan tsaki dan ba haka taso ba,ganin yanda yake tab'a hanyoyin da zai gane tana numfashi ko bata yi,sai kawai ta dauke numfashin nata dan taga ya zaiyi shin murna zaiyi ta mutu ko kuwa.?

Yanda yake kuka yake subbatu da yan surutai kamar wani sabon kaimu...tun tana danne dariyar da take karda ta fito fili har ta kasa jin yace .

"Shikenan tawa tazo karshe Allah nima ka dauki raina ba zan iya rayuwa babu wanann baiwar taka ba..dan itace rayuwata na bani ni Najeeb mutuwa nima kizo ki daukeni."

Kuka ya rushe da shi har da zukar majina kamar wani karamin yaro,bata san da ta tashi zauna ba tana nuna shi da hannu ta rushe da wata uwar dariya har rike ciki take tsabar dariya har da hawaye dan muguta..wani dadi take ji ta sashi kuka kamar yanda shima ya sata,ko bakomai ai ta rage zafin targade mata kafa da yayi ko nan ta tsaya itama taci riba,balle kuma akwai next plan dan sai ta aiwata abunda tayi niyar aiwata a kan shi idan ta ida samun sauki.

Stop yayi yana kallonta ga fuskarshi jaga-jaga da hawaye idanuwa sunyi ja jajir kamar wata gauta haka idanun suka koma...tashi zaune tayi tana dariya bai san lokacin da yayi murmushi ba yana share hawayen shi da bayan hannunshi yayo kanta.

Tashi tayi da gudu ta bar mashi parlorn tana shiga room dinta ta kulle dakin tana mai shigewa toilet dan yin wanka ,tana wanka tana murmushi dan abun yayi mata dadi da ta saka Dr Najeeb kuka murmushi ta Kara saki tana cewa.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now