ZAZZAFAR KAUNA 161-180

196 9 7
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*161-170*

Kallon Baby take har ta iso wajen su ta zauna sai sakin murmushi take kallon Zulaihat tayi tana cewa.."nasa fa lecturer din ya shigo fa." Girgiza mata kai kawai Zulaihat tayi tana murmushi itama Baby murmushin tayi mata tana cewa. "Alhamdullahi Allah na gode maka da hadani da masoyi nagartaice wanda ya iya soyayya." Har zata cigaba da maganar lecturer din da suke zaman jira ya shigo yana bata hakuri akan b'ata masu lokaci da ya dan yi...cigaba da yi masu abunda ya tarasu yayi da yake a busy yake bai wani jama ba ya kama gabanshi,bayan ya tafi kowa ya tashi dan yaje ya huta saboda sun gaji yau sun sha lecture...Koda suka fito su ukku sai labari suke ba ma kamar Baby da tafi kowa zuba a cikin su kuma ba labarin da take basu sai na Najeeb da irin ansar da yayi mata da kuma yanda ya nuna mata kulawa da kuma nuna ya anshi soyayyarta hannun biyu shi a shirye yake da ya aure ta dan bai san wasa da b'ata lokaci.

Cigaba da gaya masu tayi abun da yace mata da kuma irin kulawar da yake nuna mata zai mata idan har ya aureta sai a lokacin Zulaihat ta kalleta tana cewa.

"Bai ce maki yana da mata ba.?"

D'aga mata kai tayi tana cewa.."A'a ni bai wani gayaman yana da mata ba,Kuma fa sai da na tambaye shi ko yana da mata." Furzar da iskan bakinta mai zafi tayi tana jin wani irin rad'adi a zuciyarta,daurewa tayi tana sakin murmushin dole tana cewa..."da kika tambaye shi ko yana da mata mai yace maki.?" Dan shuru Baby tayi sai kuma tace mata.."ce man yayi shi bai da mata bai tab'a aure ba,amman Sis Zulaihat ko dai kin san shi ne.?" Girgiza kai tayi da sauri tana cewa.."ko d'aya ni ban san shi fine tun da bai da mata ai sai a fara shiri musha biki ko.?" Murmushi Baby tayi tana bude motarta tace.."in shaa Allah sooon za'a fara maganar auren ai tun da dai a shirye yake kamar yanda nima nike a shirye."

D'aga mata kawai hannu Zulaihat tayi tana mai yake mata baki har ta bar wajen sauke ajiyar zuciya tayi tana kallon Zubaida tace..."yanzun zaku tafi gida.?" D'aga Kai Zubaida tayi tana cewa.."maybe ban sani ba gaskiya sai na je zan ji fatan dai bamu zaki bi ba?" Dan turo baki kawai tayi tana cewa.."Byee sai mun had'e gida." Daga haka suka rabu ita ta nufi office din Najeeb Zubaida kuma ta nufi office din Moha ita ma.

Dan nocking tayi tana tura office din ta shiga zaune ta tadda shi yana shan tea,samun waje tayi ta zauna tana dan kallon shi ta gefen ido,jikinta sanyi yayi sosai da ya nuna bai son da shigowarta ba a office din,shan tea din shi kawai yake yana wani sakin murmushi yana danna waya ,take ranta ya bata da Baby da yake charting dan yanda yake sakin wanann murmushin to tabbas ba a banza ba kalaman soyayya ne Baby take gaya mashi zafafa shiyasa yake wani murmushi.

Kauda kan ta gefe tayi tana turo baki gaba sai wani motsi take da baki daga gani maganar zuci take, girgiza kai kawai yayi yana tashi ya had'a komai nashi yayi gaba bai ce mata komai ba...tashi tayi ta bi bayan shi tana jin kamar ta anshe wayar ta yarda k'asa ta taitaketa ta Kuma yi ma sim din pieces taga ta karshe.

Tsaki tayi a k'asan zuciyarta tana cewa a hankali.."ko kyaun soyayyarma bata yi mashi ji bar shi ita kuma wawiya sai wani rawar kafa take duk sai nayi maganinku soon sai na raba wanann soyayyar banzar naga ta karshe."....Shiga tayi gaban mota tana wani hura hanci sai wani yauki take da yakuna sai kace danyar kubewa,duk yana sane da reaction din ta shi dariya ma take bashi,har suka iso gida ba wanda yayi ma wani magana yana parking ta fito ta shigewarta gida dan ta gaji sosai ga kanta da yake mata ciwo ga kuma yar yunwa yunwa da take ji,room dinta kawai ta shige ta fad'a wanka dan wani irin zafi take ji mai shiga jiki.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now