ZAZZAFAR KAUNA 101-110

228 9 2
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*101-110*

Murmushi yayi yana ajiye waya ya kalli su Mama yace.."Baba ne muka gama waya da shi fa." Zaro Ido Jidda tayi zuciyar sai bugawa take da sauri da sauri dan wani irin tsorone ya dirar mata jin Yaya Muhd yace da Baba yayi waya..ita kuwa Mama Murmushi tayi tana cewa.."Mai ya ce maka.?" "Tambayar kuna ina yayi sai na gaya mashi kuna nan gidana shine yace ga shi nan zuwa."
Murmushi kawai Mama tayi bata ce komai ba,daman tasan zaizo dan ba zai iya jurar rashinta ba a gidan bugun da Kari ma tasan yanda yake son Kulu ba zai tab'a korarta ba daman dai dokin zuciya ya hau har yayi abun da yayi din a jiyan.

Ita dai Jidda bata sake saka koda tea ba a bakinta tun da taji Baba zai shigo,tana cikin tunanin yanda zata kaya idan kuma yazo ko dan mai zaizo?ko zuwa zaiyi ya koreta tun da dai yace baya bukatarta... Humaid ne ya bata waya yana cewa.."Yaya Kulu ga Yaya Meenat nan zaku yi magana."

Ansar wayar tayi tana kangata a kunne sai kuma ta share hawaye tana cewa.."missing uh too Meenat,ya gidanki fatan kina cikin koshin lafiya.?" Daga bangaren Meenat ta d'aga mata kai tana cewa.."Lafiya lau Yaya Kulu,nagode ma Allah da kika dawo garemu Yaya Kulu yanzun nan zamu taho gidan Yaya din nida Abba Kulu."

Hawaye ta share tana cewa.."shikenan Meenat sai kunzo inason naga Kulu takwarata Allah yayi mata albarka." Da Amin Meenat ta ansa tana kashe wayar tana mika ma Humaid waya ,Yaya Teemarh ta shigo tana cewa..."Ina Kulun take, Alhamdullahi Alhamdullahi Allah mun gode maka Kulu kina Ina." Haka ta shigo tana cewa ko sallama bata yi ba.

Tashi Jidda tana rungume Teemarh sai suka rushe da kuka su dukansu sai da sukayi mai isarsu sanann suka yi shuru kallonta Teemarh tayi tana cewa.."Allah sarki Kulu ashe da rabon mu kara ganawa,mun sha kuka har mun gode Allah..nema iya nema munyi maki Jidda Allah dai bai qaddara zamu ganki ba har mun fidda rai oooo Allah maji rokan bawa Kinga kin dawo Allah mungode maka."

Share mata hawayen Jiddah tayi tana cewa.."Nima kuna raina a Koda yaushe Yaya Teemarh kullun cikin mafarkinku nike Ina kuma yi maku fatan alkhari da gamawa da duniya lafiya Alhamdullahi tun da na samaiku cikin koshin lafiya ."

Zama sukayi suka fara fira tana basu labarin zamanta a Ukraine da haduwarta da AK,komai dai bata manta ba sai da su Meenat sukayi kuka dan Yaya Teemarh bata dade da shigowa ba itama Meenat ta shigo...godiya Mama ta dunga yi ma Ammie tana jinjina mata ita da mijinta dan kuwa tabbas su din mutanen kirki ne halinsu mai kyau ne kuma abun koyi ne.

Dan kuwa duk wanda ya taimaka ma dan'uwanshi shima bai san ya tashi qaddarar zata kasance ba sai yaga shima an taimaka mashi kamar yanda ya taimaka maka ma wani,shiyasa ake son mutun ya yawaita taimako ko dan goben shi

★★

*ABUJA 🥀*

Sai wajajen karfe biyar na maraice ya gama duk abunda yake yi dan har meeting sai da yaje a senate bayan ta fito daga lecture din da zai yi ,bayan ya gama taitara komai nashi ya shiga rest room din da ke cikin office din shi.

Kwance ya ganta tana bacci ta turo baki ga dukan alamu tana cikin jaraba baccin yayi awon gaba da ita,girgiza kai yayi ya tsaya yana kallonta yana mamakin Karfin halinta, dole ma yace karfin hali in ba karfin hali ba ta dauko halin da ba nata ba ta daura ma kanta...shi har tsoronta yake yanzun dan ma yana dakewa bai nuna mata ,amman har tsoro yake su hadu ta fara zazzaga mashi jarabar nan tata,ita ko ciwon kai ma bata tsoro balle kuma azo da ciwon baki.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now