ZAZZAFAR KAUNA 11_20

297 16 1
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*11-20*

Shirin dawowa kasarsu ta haihuwa Beauter suke dan har ta saki gidan da take haya a Ukraine ta taitara duk kayanta a cikin trollys ta maido a gidan su AK ba abunda ta manta bata kwashe ba bama kamar kananun kayanta da kuma kayan gyaran jiki sai da ta kwashe komai...motarta kuma a kasuwa ta sakata ta saida kayanta ta sa kudinta a account duk da tana jin zatayi kewar kasar Ukraine dan ta saba da rayuwar Kyiv sosai rayuwace ta yanci ba ruwan wani da wani kowa hidimar gabanshi kawai yake.

Amman kuma yanzun hankalinta kwacokam ya dawo gida nigeria bama kamar gusau ji take kamar ta rintse idonta ta bude ta ganta tsindun a cikin gusau ...gusau din ma a cikin gidansu parlon Mama da sai yanzun take jin wani kewar parlon tana adfdaba mata,sai yanzun take jin kewar dramar gidansu da comedy din su Yaya Bash,daman shi Yaya Bash yana da saukin rai kuma akwai shi da zuciya mai zafin tsiya bai daukar shashanci amman yana wasa da yara.

Saukowa daga saman bene tayi tana cewa.."Sorry Beb tashi mu tafi." Kureta yayi da ido yana Kara jin tsoron Allah a zuciyarshi ya kuma Kara yarda babu abun bautawa da gaskiya sai Allah,kuma ba wanda ya isa yayi hallita sai Allah tabbas Allah yayi hallita a wajen Beauter...Allah ya azurtata da kyau wanda ko ita yana jin bata san ta da shi ba komai nata mai kyau ne gata wata irin colar ce Allah yayi mata wanda da wuya a samu mai kalar fatar da suka Kai goma a duniya dan fatar ba baka bace amman brown skin ce mai shike da kuma daukar ido.

Hura mashi iskan bakinta tayi tana girgiza shi tace.

"Beb."

Turo baki tayi tana yarfa hannu cikin shagwabar ta da ta zamai mata jiki tace.."mu tafi kaga muna cinye time fa." Murmushin shi mai tsada ya sakar mata yana shafa gefen fuskarta da yatsunshi guda biyu yace.

"I love you Partner."

Lumshe Ido kawai tayi tana jan hancinshi a hankali tace.. "Are the best Beb!Oya let go."

Jan hannunshi tayi suka fita daga parlon da kanta ta bude mashi motar ta saka shi sannan ta fiddo key din motar a aljihunshi ta shiga driver seat tayi worming din motar tana dannna horn gateman ya bude mata kofar ta fisgi mota suka dauki hanyar.

Waka ta kunna ta can kasar tana maida volume din k'asa dan a hankali sound din wakar yake fitowa tana kadai Kai tana dan bin wakar a hankali dan tana son wakar sosai and tana son wakar mawakin daman dan yana sakin sabuwa take download dinta...duk da ita ba ma'abociyar jin waka bace ace ma game ce to ba daga baya ba a wajen tasan ita boss ce indai kan game ce.

Kallonta yayi yana cewa.

"Partner gobe kamar yanzun mun dauki hanya."

Murmushi tayi tana kanne mashi ido d'aya tace.."Yeah." Sai kuma ta dan waigo tana kallonshi tace.." Kai din na mussaman ne Abdulkadir kayi man abunda har na mutu ba zan tab'a yi mantawa dakai ba and Kai ne silar fitowa ta d'aga kazamar rayuwa..rayuwa irin ta dabbobi dan mutun mai hankali da tunani ba zai tab'a yin rayuwa irin tawa ba,dan duk wanda zai ta had'a jikinshi da mutane barkatai sai marar hankali wanda bai san ciwon kanshi ba,ban taba ji da son jin nima inason nayi aure tun bayan barina gida sai da Allah ya hadani da kai, kaine farinciki rayuwata kuma kaine hasken rayuwata ka rike wannan."

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now