RABI'ATU

3.9K 123 4
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
      *RABI'ATU*




STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤


® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



Follow me on wattpad @ Billylosh1






*THE WHOLE BOOK IS YOURS MOMMAH (AUNTY SIS💕)*



Kuyi min uzuri am too busy these days daz why kuka jini shiru dan naga k'orafin ku e.g Sis meenah, Maman Abra, kuna da yawa ba sai na lissafo ku ba you know yourselfs.......... Ban manta dake ba fa'iza gashinan😜


Dedicated to you *Fai'za musa bunu*












4⃣

        Tunda Rabi'a  ta zauna a seat din  Divya take kallonta daga sama har k'asa saboda idan aka ce maka Rabi'a na da tab'in kwa'kwalwa baza ka mu'sa ba tare da kallon ikon Allah.

        Ita kuwa Rabi'a ko ajikin ta bata ko kalli inda Divya take ba har ta gama sauraron Rai Dangin Goro,  malam yana fita ta tashi ta nufi hajiya da kudin ta, ciro kud'in tayi tare da mik'a mata ta ce "irga ki gani sun c'ika" da sauri hajiya ta amsa tana fara'a ta k'irga kud'i, sun cika cifcif d'agowa tayi tare da cewa "Rabi'atu kud'i daidai wlh y'ar albarka kin cika alk'awari" "toh ay dole ne in cika alk'awari tunda na d'auki kayanki" hajiya ta k'ara godiya sannan Rabi'a ta koma seat d'in ta ta zauna.

     

     Zarah ce ta tashi daga barcin da take yi ta zauna tana mitsika ido duk kw'ansa da k'yar yake bud'uwa "mamaah" sunan da  zarah take kiran Rabi'a kenan da gw'aran cin ta,  juyowa tayi tana kallon ta tace " kai zarah wai har kin tashi,ke baza ki bar ni na huta ba kwata-kwata sai jarabar tsiya yanzu sai ki ce yunwa kikeji salan ki tsotse ne mtseeeew" sa hannu tayi ta dauko ta da hannu daya wani irin kuka mai sauti zarah ta saki harda shid'ewa, idanuwa Rabi'a ta fito dasu saboda tsananin rud'ewa da tayi ta rasa mai zatayi gashi bata san abinda ke faruwa da ita ba saboda yanda zarah take yin kuka,juyowa yan'ajin sukayi Divya ce ta karbe ta ta soma rarrashinta  amma ina kukan sai k'aruwa yake yi ahaka Divya ta fara dudduba jikin ta tana neman abinda ya same ta.

     Tana duba hannun ta taga ya kumbura suntum "innalillahi wa'inna ila'ihir raji'un"shine abinda Divya ta ambata a bakin ta sai hawayen da suka ringa zubo mata saboda tausayin zarah da taji, Rabi'a ce ta tashi tana cewa "mai ya same ta" tare da zazzaro idanuwa waje a lokacin da ta yi tozali da kumburarren hannun zarah ga kukan da takeyi, Divya kuma sai addu'oi take tofa mata amma ina gashi bataso a tab'a mata hannun ko kad'an a haka headmaster ya shigo ya samesu Divya ce tayi k'arfin hali ta sanar dashi abinda ke faruwa, Rabi'a kuwa ta sake baki da ido tana kallon ikon Allah....

   Kw'atance gidan wani tsoho mai gy'aran targad'e da karaya yayi musu akusa da makaranta basu b'ata lokaci ba suka nufi gidan domin sanin abinda ya same ta, suna shiga suka tarar babu mutane a gurin hakan ya basu damar shiga ciki , samun guri sukayi suka zauna har lokacin Zarah na hannun Divya ..........


    mats'owa yayi yana Tambayar mai ya faru, sosa k'eya Rabi'a ta fara yi da mitmit da ido sannan ta ce "eh wlh dama d'aukanta nazo yi jiya sai na fizgo ta da hannu daya" Divya da sauri ta d'ago kai tana sauraron abin al'ajabi da sakarci irin na Rabi'a, malamin bai ce uffan ba ya rike hannun ya fara tofin tare da jajjan hannu kukan Zarah ne ya k'aru.......




BILKISU ARDO CE❤





❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now