RABI'ATU

497 18 1
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1






*AUNTY SIS💞*














3⃣4⃣➡3⃣5⃣











       Ran litinin da safe aka sallami Abdoulra'uf, da k'warin shi yayi parking ya fito nan maigadi yake sanar dashi cewa jiya Baffansa yazo tare da matarsa,mamaki sosae ne shimfid'e akan fuskar Abdoul nan ya barshi ya wuce yanata tunanin taya sukasan gidanshi kuma mai ya kawosu da wannan tunanin ya  shigo parlour amma abinda hancin sa yaji masa ne yasashi dakatawa  idanuwansa suka sauka akan Inna da ke shimfid'e akan 3seater white leather seat k'afafuwanta duk faso ga datti gefe guda kuma Rabi'a ce zaune akan centre table tana sosa kanta k'wark'wata na bin jikinta, cikin zafin rai yace

   "Kai you're very stupid, waya kawo ku gidana wannan wani irin hauka ne, ke mahaukaciya sauka akan abinan ko in b'abb'allaki" tare da nuna Rabi'a a firgice ta sauka tana b'uya  a bayan Inna saboda tsoronsa da takeji.
    Inna ce ta mik'e tace
  "Haba yaro ai kayi tambaya kaji ko, toh tunda bakayi ba ni bari na fad'a maka Matar ka  na kawo maka"

   "Matata" Abdoul ya maimaita

  "Ras kaji da kunnen ka, gata nan ran juma'a aka d'aura auren ni kaga tafiya ta dama abinda yasa na zauna saboda karta zauna ita kadai ne toh kuwa tunda ka dawo shikenan".
   Ta mike ta zari mayafinta tace wa Rabi'a "yi nayi bari na bari kinji ko 'yar lele na Allah ya miki albarka ki kula da mijinki duk abinda yasaki kiyi zan d'inga zuwa duba ki karki damu"

  Nan ta fice tabar Abdoulra'uf rike da kansa da yake ta faman sarawa ya wuce d'akin shi ya k'wanta yana rike da kanshi yana addu'oi can anjima yaji k'aran fashewar abu kafin ya mik'e yaji wani k'arar da gudu ya sauka a gado ya fito sai cin karo yayi da Rabi'atu rike da guntun glass a hannun ta k'asa kuwa centre table ne ya tarwatse,
 
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wai dama baki tafi ba uban mai kika tsaya yi agidan kuma wa yace ki tab'a min kaya "?

Rabi'atu tace

    "Dan Allah kayi hakuri bazan k'ara ba wallahi kuma abin ne yamin kyau shiyasa na d'auka zan kai shi d'akina"

  Ya maimaita "D'akinki? Lallai bakida hankali gidan ubanki ne dazakice d'akinki, dalla can fita ki barmin gida "

  Rabi'atu k'walla ya cika ido tace " dan Allah kayi hakuri bansan hanya ba kuma Inna tacemin gidanane kuma kai mijina ne"

  Dasauri Abdoulra'uf ya biyota inda take ya hankad'ata k'ofar fita kenan sai ta fad'i akan k'afar Baffa Bala dake k'okarin shigowa ya dakatar da Abdoulra'uf dake tunkaro ta yace

   " Inka kuskura ka k'ara taku d'aya sai na maka rashin mutunci"
Jin  maganar Baffa Bala ne yasa Rabi'atu d'agowa tana k'okarin buya a bayan shi yace "Dallah can k'azamar banza matsa kiban waje, kai kuma Abdoul ka bud'e kunnuwanka da kyau ka saurareni kaji,Rabi'atu matarka ce nina aura maka ita kuma kasan cewa baka da wani uban bayan ni saboda haka karka kuskura ka kashe musu 'ya dan baza abarka ba, kuma idan na k'ara ganin k'afarka agidana wallahi sai na daure ka in kunne yaji jiki ya tsira"

  Yana gama magana ya juya har zai fita sai ya juyo yace "ke kuma karki kuskura ki bar gidannan in kuwa kika fito toh wlh ba gidana ba daga ke har Uwar taki"

    Abdoulra'uf zaman dirshe yayi agurin yana ta dirzar kuka mai t'suma zuciya, Rabi'atu kuwa ihu ta ringayi tana kuka harta shiga d'akinta ta barshi a durk'ushe a wajen.








*BILKISU ARDO❤*





❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now