RABI'ATU

1.7K 71 18
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1






*AUNTY SIS💞*














3⃣5⃣➡3⃣6⃣



    Saida yayi kuka mai isarsa sannan ya mik'e ya shiga d'aki ya kwanta. A b'angaren Rabi'a ma haka tunda ta shiga bata fito ba ga wata irin yunwa da take nuk'urk'usarta a d'aki suka wuni har dare dak'yar barci ya d'auke ta.

   Abdoulra'uf yanda yaga rana haka yaga dare wuraren k'arfe biyu na dare yayi alwala yayi nafila raka'a hudu yayi addu'oi ya idar ya nannade sallayar ya hau kan gado ya kwanta, ji yayi ranshi yayi fari kamar baida damuwa ya kwanta ya rufe jikinshi da bedcover.k'arfe biyar ya farka yayi alwala ya nufi masallaci yana dawowa ya kwanta tun kafin rana ta  fito. Rabi'a sai barcin ta takeyi ba tareda tayi sallah ba , Abdoulra'uf duk da AC dake aiki a d'akin bai hanashi yin zufa ba duk ya gama jik'ewa saboda mafarkin da yakeyi Mamy shi tana

cewa"  Abdoul kaji tsoron Allah daya halicceka karka tauyema k'aramar yarinya hakkinta nasan cewa baka sonta kuma bada san ranka  hakan ya faru ba amma karkayi abinda Allah zaiyi fushi dakai kasani cewa hakkinta yana kanka karka wulak'anta ta Dan Allah Abdoul karkayi abinda Allah bayaso Allah ya sanya alkhairi azamanku ka cigaba da.  *ADDU'OI, AZKAR DA KARATUN AL-QUR'AN* komai yayi zafi maganinsa Allah. Fuskarsa hawayene sharkaf akwance a d'an firgice ya tashi yana salati maganganun mamy ne ke masa yawa akai sai yaji duk bai kyauta ba haka ya mike ya fito zuwa d'akin Rabi'a ya sameta ta bararraje tana bacci harda yawun bacci yanata zuba ga d'akin sai warin balaga yakeyi haka ya daure ya tasheta dakyar ta tashi

Yace " ke kinyi sallah? ko kinsan k'arfe 10am tayi ? Cuno baki tayi saboda ya katse mata barci, jin tayi mishi shiru ne yasa

yace " tashi kiyi sallah kin makara " sannan ya juya ya barta a tsakiyar gado. yana fita ta d'aura daga inda ta tsaya ta cigaba da barci.

   Yana  fita yayi kitchen ya kunna kettle  ya bud'e frigde ya d'auko slice bread ya saka a toaster ya juya ya fasa 3Eggs yayi pinching salt kad'an ya saka yayi scramble egg ya juye a plate ya cire toast bread d'in ya dauki mug ya had'a green coffee ya zauna a dining yayi breakfast ya gama ya d'auraye plates d'in sannan ya wuce bedroom d'insa ya fad'a toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin farar shirts da white cobalt jeans ya taje gashinsa yayi spraying *juicy couture* da *kokoriko*, ya d'auki wayarsa da car keys ya fito yana baza k'amshi, mota ya shiga direct asibitin sa ya wuce domin ganin kammaluwar aikin yana isa ya tarar da Kabiru d'an k'wangila  yana shirin shiga mota ganin Abdoulra'uf ne yasashi t'sayawa suka gaisa suna tattaunawa akan aikin tare da zazzagayawa ko'ina a cikin asibitin , sai around 1pm sanan suka fito compound.

   Abdoulra'uf yace " Kabir inason ka nemamin house maids guda biyu mata amma nafison yare banason bahaushiya yau ko gobe"
 
Kabir ya nisa yace "don't worry sir in Sha Allah zankawosu zuwa anjima sai ka fad'amin unguwar dazan kaisu "

Abdoulra'uf yace" karka damu basaika kawosu ba in ka samosu give me a call i will pick them"

  Nan sukayi sallama Kabir dai abin mamaki yake bashi yanda Abdoulra'uf bayason kowa yasan a ina yake da wannan tunanin ya shiga mota Abdoulra'uf gida ya wuce direct yashiga d'aki yayi wanka yayi alwala ya fito masallaci, Rabi'atu kuwa tunda ya tasheta ta koma saida barcin ya isheta sannan ta tashi tana Neman abincin ci ta rasa yazatayi fitowa tayi ta samu mai gadi tana tambayarsa a ina ake siyarda abinci yayi mata k'watance zuwa kasuwar bakin titi ta fito tana ta tafiya ba dan ta gane k'watancen ba sai yawo takeyi daga wannan titin zuwa wancan har aka fara kiraye-kirayen sallar azahar, gashi hanya ta b'ace mata..





*BILKISU ARDO CE❤*








❤💕❤💕❤💕❤

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 01, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RABI'ATUWhere stories live. Discover now