RABI'ATU

482 21 1
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1




*AUNTY SIS💞*




2⃣6⃣➡2⃣8⃣



   Dafe kanshi yayi saboda yanda yake sara mishi yace

    "Wai mai yake faruwa ne? Shin akwai rai da yake living in dis mess? "

   Fitowa yayi da sauri a compound yaga malam Habu tare da malam sani sunyi jugum-jugum k'arasowa yayi har inda suke yace

  "Shin yaushe rabon Rabi'atu da gidan nan? Kuma wa yake kwana aciki? Ina masu aikin gidan nan? Ina watering man ?"

   Tambayoyi ya ringa jero musu aykuwa malam Habu an tab'o inda yake masa k'aik'ayi yace

  "Yallabai kayimin afuwa,amma tun watan da kasa k'afa kabar k'asar nan Hajiya ta kori masu aikin share-share da yi mata girki ba tare da ta biyasu  albashin su ba, wasu ma da kuka suka tafi."

    "masu aikin nan farfajiya kuma rashin albashi ne yasa suka tafi, nima abinda yasa zan tafi kenan babu abinci babu albashi sai dai na fita k'asan Layin nan alwai gidan wani commander da ake bada sadaka nake karbowa ko kuma malam sani ya kawomin daga gidanshi toh yallabai kasan halin rayuwa shima ba k'arfi gareshi ba kuma shima baya samun albashi toh wataran ma haka zamu kwan da yunwa ga kuma iyali , kayi hakuri yallabai bana fada bane dan na had'a ka da iyalinka amma iya kacin gaskiyar kenan ".

    Abdoulra'uf da tunda ya fara jawabi idanunsa suka rine sukayi ja zuciyarsa nayi masa rad'adi yace

   "Kuna nufin Rabi'a tana cikin gidan nan haka kamar bola?"

     "Eh yallabai yanzu ma ta tafi islamiyya ne bata dad'e da fita ba."

wayarsa ya ciro yayi dialing wata number da ya rubuta Mr.funitures,bayan sun gaisa ne yake ce masa ya kawo masa funitures na parlour da duk wani tarkace irin nasa everything iri daya. 

    "Please kuma yanzu nakeso akawomin"

    Yace "ok sir within 30mins in Sha Allah" 

    "OK thank you"


Tare da kat'se wayar ya umar ce su dasu biyosa ciki. Daukar kayansa sukayi tare da binshi ya nuna musu hanyar upstairs suka wuce dashi ciki, suna ajiyewa suka sakko suka tarar Abdoulra'uf ya fara firfitar da kayan waje  zagewa sukayi suma suka  fara aiki komai na parlour aka fitar dashi ko tsinke basu bari ba sannan suka koma d'akinta nan ma basubar komai ba toilet ne basu tab'a ba sannan suka share parlour Abdoulra'uf yasa key ya rufe dakin ya bude na kusa dashi wanda komai na buk'ata akwai komai aciki sannan yasa aka kawo masa masu aiki mata guda uku basu dad'e ba suka iso aka barsu da shara da mooping.

     Kofar kitchen ta baya suka bude aka fitarda duk abinda Rabi'a ta tab'a amfani dashi da gas cooker aka bar wad'anda suke cikin kwalayensu kofar store dake mak'ale a kitchen din suka  bude k'yenk'yeso da kwari ne suka musu sallama, beraye kuwa ba'a magana duk sun gama b'ubb'ula buhunhunan abincin madarar g'wang'wani  duk sunyi expired milo kuwa duk ya d'ank'are acikin g'wag'wani yayi bak'i haka aka ringa fitarwa Abdoulra'uf sai da ya zubarda hawayen bak'in ciki.

      suka kimtsa koina agidan sai ga motar kayan ta iso, komai su dasuka kawo kayan su suka jera su parlour ya dawo kamar yanda yake a'da. Gida ya gyaru dan har upstairs saida aka gyara dama tunda ya tafi ba'a taba gyarawa ba.

   Wanka ya shiga yayi ya shirya sannan ya fito nan malam sani yake

   Cewa "toh yallabai ya za'ayi da wad'annan kayan?"

    "Eh a nemo mota ta fita dasu, kayan sawanta kuma ku duba sababbin sai ku d'auka in kunaso amma dan Allah sababbin kawai dan sauran bazasu sawu ba ak'ona su"

    "Ak'ona kuma yallabai, ay bak'yau albazaranci ko?  ina laifin akai gidan wanki a wanke a goge sai a kyautar".

   "Murmushin k'arfin hali yayi sannan yace hakane, toh ayi hakan kasamo mota ga dubu d'ari nan kakai kayan wanki da guga  kace su wanke kayan sau biyar sai ka biyasu, ka nemo motar da zasu fita da kujerun da gadon"

"toh yallabai godiya muke Allah ya saka da alkhairi Allah ya k'ara arzik'i."

     "Ameen" yace a tak'aice

Harya juya zai koma ciki yace

    "Uhm nikan karfe nawa take dawowa ne?"

    Cikin girmamawa Malam Sani yace

     "Karfe 11am"

   Maimaitawa Abdoul yayi "11am"?

   "Eh yallabai"

"Toh malam sani yanzu ay karfe biyu na rana, ko ka manta bakaje ka dauko taba ne?"

  Shafa kai yayi  yace

  "Ay bani nake d'auko ta ba"

Changin fuskar da ya gani a wajen Abdoul ne yasa ya cigaba da cewa

   "Kayi hakuri yallabai ba laifi nane ba wallahi ita ta jamin kunne da cewa kar in kuskure inji d'auko ta ballantana in kaita ban tab'a ba saboda bataso kaji dalilina, kuma bata tab'a kaiwa haka bata dawo ba".

   Juyawa yayi ba tareda yace komai ba ya hau sama d'akinshi dan har yanzu gidan wari yake mishi.



  Rabi'a tunda taje makaranta take kwance ko Rai dangin goro yau ba'a saurara ba saboda zazzabin daya rufe ta, haka ta ciro wayarta ta kira Inna take sanar mata bata da lafia tace gatanan zuwa tana kashe wayar ta ta shirya ta taho cikin garin kano, islamiyyarsu Rabi'a tazo ta jira aka tashe su sannan tafito da k'yar take tafiya bata gani da k'yau har ta iso gurin Inna.

Inna na ganinta ta rik'e ta jikin ta yayi rau-rau da zafi, suka dauki hanyar asibiti suna zuwa likita ya dubata ta fadi abinda ke damunta yace

    "Toh Rabi'a kinada aure?"

    "Eh" tace masa

Likita yace "Toh ga test kuje kuyi yanzu sai ki kawomin result"

Karb'a sukayi suka nufi lab aka d'iba jinin ta after some mins aka basu result suka koma office din likita suka mik'a mishi result ya karba ya karanta sannan ya rufe yana murmushi  yace

    "Congratulations Rabi'atu you're expecting a baby two weeks pregnant. Ina nufin kina d'auke da ciki na sati biyu"

      😨ciki?????????





Ni kuwa billylosh nace "Wayaga su Rabi'a da ciki ank'i Zarah gashi an samu wani.....






*BILKISU ARDO CE❤*






❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now