RABI'ATU

818 41 2
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY&WRITTEN BY BILLYLOSH❤




® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*



(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_



#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



Follow me on wattpad @ Billylosh1

_*ʍվ Տհօղɑ ƒօɾ վօմ ҍҽӀօѵҽժ ՏíՏ ʍɾՏ.յɑʍíӀ*_


       *AUNTY SIS💞*
   

Yau dai nayi answering calls ba adadi ga comments duk akan *Rabi'atu* gaskiya am so happy you guys should keep encouraging me lurv you bohot bohot.
      much luv my fans.❣



8⃣


      "Wannan ai Zarah ce" Dr. Halima ta ce "kinsanta ne?" "Eh ay ita ce nake baki labari d'azu" Dr. Halima sake baki da ido tayi tana kallon Zarah sannan ta ce "Divya kina nufin wannan ita ce Zarah da kike bani labari d'azu?"

        Divya da kuka ya ci k'arfin ta kasa ma gana ta yi nan DR. Halima ta d'inga rarrashinta har ta ts'agaita da kuka sannan ta dubata ta ce " ina ganin zata kwana biyu a asibitin saboda jikin ta yayi stabilising yanzu sai munjira mahaifiyarta tazo tukunna, Divya take it easy mana ki bar kuka".

     Divya ta d'ago fuskarta da ta kumbura tayi ja saboda kuka ta ce "wlh Dr. Halima har cikin jini na nakejin Zarah bazan iya tafiya in barta anan ba kuma acikin wannan halin ba please ki barni anan har Rabi'a tazo" Dr. Halima da tunda Divya ta fara magana takejin tausayin ta ta ce "ba komai Divya ay dama ana neman mai zama da ita gashi ko kudi basu biya ba ballantana maganin da zata sha " bakomai Dr. Zan biya dukka"

      Smiling Dr. Tayi sannan ta ce " Allah ya saka maki da mafificin alkhairi" "Ameen" kawai ta iya furtawa  sannan ta juya tana kallon Zarah tare da shafa kanta tana to'fa mata addu'oi.

      Malam sani jiki a sabule ya shiga mota ya koma asibitin yau ma haka ya gama zaman sa ba tare da an bari ya shiga ganin mara lafiyan ba ya dawo gida. Yana isowa gida sai ga kiran Alhaji. amsawa yayi ba tare da yasan abinda zai fad'a mishi ba, suka gaisa cikin mutunci da mutuntawa ya k'ara da cewa " ya jikin Zarah?" "Da sauk'i Alh." "Amma mai yasa Rabi'a bata daukar waya?"  "Eh toh gaskiya Alh. bana ce ba ko bata kusa da wayar ne kila, ay in sha Allah zata warware muna nan tare ay za'ayi komai daya kamata ayi kamar kana nan", "dadi sosae Dr.Abduol yaji sannan sukayi sallama tare ta katse call din duk  da hankalinsa ba'a kwance yake ba amma maganar Malam sani ta cire mai kokwanto.

  Rabi'a tana shiga aji kowa ya ringa mata ya mai jiki a yatsine take amsawa har ta isa mazaunin ta.

    Safeeena ce ta juyo ta ce " Rabi'a ina Zarah naga yau baki zo da ita ba" kamar baza ta amsa ba ta ce "Eh banzo da ita ba " da Safeena taga ba mutunci sai ta juya tayi shiru.

    Ana tashi kuwa gida ta wuce tana shiga ta tarar da Inna Rakiya(mahaifiyarta) da gudu ta fad'a jikin ta tana washe hakora ta ce "Inna ke ce" "kinji ki da shirme bagani ba kuwa" "sannu da zuwa" "Inna ta ce yawwa yar'albarka kawo min ruwa" tashi tayi ta dauko mata bottle water ta kw'ankw'ade  dukka sannan ta dire robar ta ce "ina Zarah ne naga ban ganta ba" sosae k'eya tayi sannan ta ce tana Asibiti" Inna ta maimaita "Asibiti" "Uhm bata da lafia ne ta k'one da ruwan zafi"Inna ta ce  "ke  kuma kina gida?" "Eh mana Inna" gud'a Inna tayi sannan ta jawo Rabi'a ta ce yar'albarka daidai kenan dama ba k'aunar ganin ta nakeyi ba ki bar ta. ma a asibiti karki sake komawa ji yanda ta gama zuke ki duk kin gama ramewa" "Rabi'a tayi cha'rab ta ce dama ay ba komawa zanyi ba wlh dan ni na tsani yarinyar har bana fata uban ta ya dawo kilan ma Zarah ta mutu ", "Allah ya sa "in ji Inna.





BILKISU ARDO CE❤



❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now