RABI'ATU

891 39 2
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
      *RABI'ATU*



STORY&WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*



(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






Follow me on wattpad @ Billylosh1



     *MOMMAH AUNTY SIS💕*




*IN DEDICATED TO MY CHARMING SIS AMEENERH GIDADO MRS.KHAN❣*


6⃣

8:00pm

      Kafin ta k'arasa Zarah ta kw'alayar da tafashashshen ruwan zafin a jikin ta  tsabagen yunwar da ke damunta tayi tunani abinci ne, wani rikitaccen ihu ta saki, Rabi'a tsayawa tayi tana kallon ta ba tare da tayi yunk'urin d'auk'eta a cikin ruwan ba,

   

    Duk fatar jikin ta ta yi rud'u-rud'u ta tashi, tahowa tayi da gudu tana zama Zarah ta fadi k'asa sumammiya d'aukan ta tayi ta fara jijjiga ta cikin kid'ima da d'imauta ta rasa abin yi gashi ya d'uru ruwa sun kukkumbura, tana tattab'a jikin ta ba tare da ta lura cewa tana kwailaye mata fatar data k'one ba wani rikitaccen ihu ta saki saboda tsoro wayar ta ta janyo tana k'ok'arin kiran driver, tunawa tayi batada number hakan yasa ta kinkimeta ta fita da ita compound sai ga Sani driver yana k'ok'arin shigowa saboda kiran da Alh yayi mishi cewa yazo ya duba su Rabi'a lafia bata answering call, ganinta da yayi da y'a a hannu babu  ko hijabi a jikin ta yasa shi yin gudu yazo inda take ya ce,


     " Haj lafia mey ya samet..... Kafin ya k'arasa magana yayi arba da jikin Zarah da yake compound din cike yake da fitilu na alfarma haske ya gauraye ko'ina,ba shiri ya kunna mota  basu ts'aya a ko ina ba sai ABDULRA'UF SPECIALIST HOSPITAL juyowa yayi ya ce "Haj mun iso", "ina ne nan kuma" "asibitin Alh. ne ay"  dallah c'an kaini AKTH mey zanyi anan gurin mtseeew"  "toh Haj ayi hakuri"  haka ya k'ara juya motar zuwa Aminu Kano suna zuwa Emergency aka wuce dasu ba tare da sun ts'aya tambayar ta abinda ya faru ba saboda yanda jikin ta yayi muni suka shiga da ita, wuri ta samu ta zauna a k'asa, malam sani kuwa yana gani an shiga da ita ya fito farfajiyar asibitin ya kira Alh. nan yake sanar masa abinda ya samu Zarah " garin yayi hakan ta faru" malam sani ya ce " wlh Alh ban sani lokacin da kace in zo inga ko lafia shine na tarar da ita a haka suna shirin fita ynz dai muna asibiti"  " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shine abinda Dr. Yake iya furtawa, "toh wani Dr. Kuka samu  bari in kira inji tukunnan" malam sani harda hawaye yake saboda tausayin Zarah da mahaifinta  "ya ce Alh ay ba asibitin ka muka je ba wlh har mun shiga ciki ta ce batason asibitin wai sai dai muje AKTH" shiru Dr. Yayi nadan wani lokaci sannan ya ce "bakomai Duk abinda ake ciki ka sanar dani" "toh Alh." Kashe wayar yayi ya kwanta yana fitar da hawaye masu zafi.

      Bangaren Rabi'a kuwa wayar ta ce a hannun ta tana karatu bata damu ta kira Dr. Ba ballantana ma ta sanar dashi halin da ake ciki ba a haukanta ay tunda ta kawo ta asibiti shikenan zata warke, malam sani ne yazo ya same ta sai dariya ta keyi,wasu hawaye ne suka zubo mishi d'aurewa yayi ya ce " Hajiya na sanar da Alh." d'ago wa tayi ta kalle shi ta ce  " toh waya saka ka"   "a'a dama shi ya ce in zo inga abinda ke faruwa saboda ya kira baki dauka ba shiyasa amma ayimin afuwa"  "toh naji jeka kawai "  "toh hajiya mey za'a kawo muku naga ko hijabi baki d'auko ba. Eh mu tafi kawai dan na fara jin barci tsayawa yayi yana kallon ikon Allah  ya ce  "Haj haka zaki tafi ki bar Zarah ita kadai"  "Eh  ay ba komai".






BILKISU ARDO CE❤





❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now