RABI'ATU

513 20 0
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1






*AUNTY SIS💞*





_*KUYIMIN UZURI FANS WLH BANDA LAFIYA NE SOSAE SHIYASA BAKWA JINA KWANA DA YAWA YANZU MA KUYI HAKURI SABODA BAZA KU DINGA JINA FREQUENTLY BA AMMA ZAN DAGE NA DINGA BAKU UPDATE KO DA BA KULLUM BA NE...... NEED YOUR DU'A*_❤





3⃣2⃣➡3⃣3⃣






         Kwatakwata am not comfortable saboda irin yanda Baba Baraka tasani agaba tana ta kallona, ina ta neman hanyar da zan bar parlour sai naji wayana yana ringing nan na ciro wayar naga Rasheed khan ne yake kirana na amsa tare da mik'ewa na fita waje muka gaisa sannan yayi hanging up nan na samu na kira number *kabiru dan kwangila* wanda shi nabawa kwangilar gina asibiti na cikin fara'a muka gaisa yaji dad'i da yaji na dawo Nigeria tare da tabbatar mishi da cewa gobe zanje inga aikin da ake ciki.

   Baba Baraka gajiya tayi da jiran Abdoulra'uf ya dawo hakan yasa ta haura sama tana k'unk'uni . Bai kwana agidan ba ya wuce sabon gidan shi dake *kwairanga road* yana shiga ya ajiye trolley dinshi ya nufi toilet yayi wanka ya dauro alwala ya saka jallabiyya ya shimfid'a sallaya yayi shafa'i da wutri yayi addu'oi  sannan ya tashi ya maida kayan sa cikin wardrobe ya kashe lamp ya kwanta, asubar fari yayi alwala yayi sallah wuraren 9am ya nufi gidan Baffa Bala wanda tun karfe 7am bakwai na safe Baba Baraka taje d'akin shi amma tana zuwa taga wayam gurin mai gadi taje tana tambayarshi Abdoulra'uf nan yake shaida mata cewa bai kwana gida ba, ta hana kanta sukuni tana tsaye a jikin window ta hango wata farar mota kirar *Mercedes Benz 2015*  ta danno kai cikin gidan tasha tin tic tayi parking nan ya bude ya fito yana sanye da farar shirts round neck an rubuta *LION* a jiki ya daura dilem akai tare da black jeans k'afarsa sanya da flat  takalmi hannun sa rike da wayarsa ya rufe motar yana takun k'asaita Baba Baraka harda hadiyar yawu saboda yanda Abdoulra'uf ya birge ta yake kuma bata sha'awa ya shiga da sallama ta amsa mishi ya gaisheta ta amsa tasa Inna ta kawo masa breakfast ya ci sai ga Baffa Bala ya shigo suka gaisa yana amsawa a dak'ire yace

" a ina ka kwana Abdoul?"

Abdoulra'uf ya ajiye spoon din ya d'ago yace

" Baffa a cikin sabobbin gidaje na ne na kwairanga road can na tafi ".

  Baba baraka ta maimaita "gidaje"?

Shiru yayi yana cin abincin sa yana gamawa ya tashi ya fita ya nufi d'akinsa na bayan gidan ya d'auko akwati ya dawo parlour har yanzu suna zaune sunyi jugum-jugum ya zauna ya bude akwatin ya ciro kayan gefe guda dukka ya ajiye a gefen Baffa Bala ya ce. "wannan tsarabarka ce Baffa" sauran na akwatin kuma ya mik'awa Baba Baraka sannan ya musu sallama ya fice ko godiya basuyi ba sunyi tagumi suna tunanin wannan wani irin yaro ne.

  Yana fita ya zarce site wurin aikin asibitin shi wanda alokacin an gama komai painting wasu duwatsu na decoration akeyi  yana isowa yayi parking  ya shiga ciki "what a lovely place" ya furta yayin da yake shiga asibiti ne dan daidai mai hawa uku side uku hawa tara kenan ya had'u sosai yasha glasses ta waje irin ginin turawa yasa akayi  saboda asibitin *ARTEMIS* na india ya birgeshi  in ka shiga ciki k'aton fili ne sai guest seats  gefe guda kuma hanya ce dazata shigar dakai cikin asibitin.


Yayi admiring ginin dan baiyi tunanin za su iyayin shi haka ba. Ya gama zagaya ko'ina at last  ya shiga office d'insa Wow! White&orange  ne komai na ciki k'aton parlour ne in ka shiga ga table dinsa mai S shape da kujera d'ayan site d'in  kuwa fararan kujeru ne da centre table sai mini fridge a right side bangon kuwa sun sha deco shi kanshi Abdoulra'uf yayi admiring wajen duk da irin asibitocin da yake gani a abroad.

    Inna ce ta shigo da k'ullin kayanta a hannu suka gaisa da Baba Baraka sannan ta shaida mata cewa zata k'auyen namora saida ta gama yat'sine yat'sine ta sannan ta d'aga kai ta kalleta tace jeki kwana daya na baki, dukda ba haka Inna taso ba haka ta tashi ta tafi, washe gari kuwa da sanyin safiya ta dawo saboda aikin gida, ta kwankwasa maigadi ya bude mata  tashigo  sai ga Rabi'a biye da ita fuska fal jan baki da kwalli an zane fuska  an saka wata yaloluwar atamfa riga daban zani daban ga d'ammarar da tayi a k'ugunta jikinta yayi fururu saboda rashin shafa  mai k'afarta kuwa sanye yake da silifas kore duk k'asan su ya sud'e sun tsinke an d'auresu da farar leda ana jansu haka gata da aukin dariya hak'waranta jajaye zur dasu babu k'yau gani, ga tulin kaya akanta sai faman Sosa kai take tana sosawa in ta fito da hannun sai kaga kwarkwata haka zakaga sunata sakkowa a wuyanta ga wani irin wari da takeyi . *#RABI'ATU KENAN@21yrs* suna wucewa mai gadi ya tofar da yawo yace wannan kuma fa   kamar wacce aka d'auko daga garin gab'a -gab'a. suna shiga suka wuce d'akin kwanansu suka ajiye k'ullin kayansu sannan  suka shiga kitchen shirya breakfast suka gama komai suka kint'sa gidan suka fara sharar bayan gidan Rabi'a kuwa cewa tayi ta gaji baza ta iya ba, Baba Baraka ta sakko domin shiga kitchen taga ko'ina a gyare abinci an kai ga dining hakan yasa tayi murmushi ta koma saida suka gama shiryawa sannan suka fito sukayi breakfast Baffa Bala ya fita tayi mishi rakiya ta koma parlour tana jiran zuwan Abdoulra'uf tana zaune a gurin sai ga Inna ta shigo ta kitchen ita da Rabi'a suka samu guri suka zauna suka gaisa tunda taga Rabi'a ta d'aure fuska take tambayar Inna wannan yarinyar fa, Inna tace

"hajiya kiyi hakuri  ban sanar dake ba kafin na d'auko ta Rabi'a ce 'ya ta mai gari ne yace bazata cigaba da zama ba saboda tace batason d'anshi shine na taho da ita ta tayani aiki",
    Shiru Baba  Baraka tayi sannan ta amsa mata tare da bawa Rabi'a irin ayyukan da zata d'inga yi .


     Yana gamawa ya wuce shopping mall ya siya abinda yake buk'ata ya koma gida.

    Watan sa d'aya da dawowa Baba Baraka ta fara nuna maitarta a fili na sha'awar Abdoulra'uf, yana bud'e k'ofar shiga parlour Baba Baraka  Rabi'a tazo fitowa mistakely ta watsa mishi miyar dake hannunta ajikin farar shad'dar dake jikin shi , sandarewa yayi saboda yanda miyar ta k'ona shi saboda zafinta.

  Ihu ta t'sandara mai sauti sai ga Baba Baraka da  inna sun fito domin ganin abinda ke faruwa.





*BILKISU ARDO*❤






❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now