RABI'ATU

719 30 5
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1




*AUNTY SIS💞*




2⃣8⃣➡3⃣0⃣



     "Ciki"?

Rabi'a tace "ciki likita, anya kuwa"?

Inna ce ta gwabje mata baki tace  " sakaryar banza kawai tashi mu tafi"

Mik'ewa tayi jiki babu kwari suka karbi takardar suka fito, Inna ta juyo tace mata " Dan ubanki zaki sanar dani a ina kika samo cikin sati biyu"  Rabi'a tace "walla...... Bata k'arasa ba taji saukar wani rikitaccen mari a fuskarta har sau uku. Abinda ko duka inna bata taba mata ba ballantana mari ta rike kumatunta tana dirzar kuka mai cin rai, ita bama cikin ke sata kuka ba marin da Inna tayi mata ne ya sata kuka.

   Adaidaita suka hau suka Rabi'a bata daina kuka ba aranta tana tunanin a ina ta samu ciki? Waye ya mata ciki? Yaushe? Tambayoyi ta ringa jerowa zuciyarta amma bata da amsoshin su.
       ahaka suka nufi wani asibitin amma result d'aya yake nunawa wato 2weeks pregnant, sai da suka zagaya asibitoci shida suna tarar da result d'aya alokacin ana kiraye-kirayen sallar magrib sannan suka wuce gida..




   Abdoulra'uf har ya gaji da jiranta bata dawo yana kwance a d'akin shi ya fara  tunanin rayuwar shi ta baya................

30yrs⏮


    Yaro d'an shekara tak'was 8yrs na gani a bakin k'ofar parlour yace "Assalamu Alaikum" shiru ya k'arayin sallama amma shiru kakeji hakan yasa ya bud'e labulan parlour ya shiga amma ga mamakin sa sai yaga Baffa Bala  da matarsa Baba Baraka ta hard'e k'afa d'aya kan d'aya, t'sugunnawa yayi har k'asa ya gaishe su  ko kallonsa basuyi ba ballantana su amsa masa yace

    "Baffa yunwa nakeji a sammin Abinci inci tun gayan  tuwon jiya har yanzu da dare yayi bansa komai a baki na ba dan Allah ko wani guntun tuwo ne abani in ci"

    Baba Baraka ce ta d'amk'o wuyar rigarsa ta sharara masa mari ta k'ara sharara masa wani ta rik'e kansa ta buga a jikin bango har sai da ya daina gani saboda azabar da yasha ya fad'i k'asa yana kuka yace "Baffa ka cice ni zan mutu Baffa abinci kawai na rok'a"  gyaran murya BaffaBala yayi sannan yace

    " Abdoulra'uf  wallahi zanci ubanka da wannan shegen iyayin naka toh uban waye zai baka abincin, ay masu gata suke cin abinci kaikuwa da baka da iyaye sai dai ka kwana da yunwa kuma bari kaji shinkafa da tuwo sunfi k'arfin ka saidai dawa da gero ko k'anzon tuwo yafi karfin ka shegen yaro mai idon mayu kawai, tashi ka bani guri ko in taka maka ruwan ciki"

  Haka ya tashi ya tafi, harya fita Baba Baraka ta mike tace " kai mai idon mayu zo nan"

   juyowa yayi yazo gabanta ya t'sugunna

   tace "wanki kaya zan baka da bargo kanaji na" 

  "Eh"

Wucewa tayi d'aki ta kwaso kayan dayawa wanda tasan cewa sarai bazai iya wanke wa ba sannan ta bashi bargo ,

RABI'ATUWhere stories live. Discover now