RABI'ATU

561 28 2
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
      *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BT BILLYLOSH❤




® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


Follow me on wattpad @ Billylosh1


_*AUNTY ZARAH MY DAZZLING AXLAND THIS PAGE GOES TO YOU*_


    *AUNTY SIS💞*

2⃣0⃣➡2⃣2⃣






      Duk hankalin ta atashe take magana, Son please karka tafi ka barni you're my life....kafin Divya tayi magana taga Dr. Halima ta zame k'asa ta zauna, Everyone is in shock saboda basu san mey ya faru ba kawai sunji tana ambaton Abdoulfatah my son, nan Divya take tuno ranar da Dr. Halima take bata labari akan tilon d'anta wato Abdoulfatah, tanaji dashi kamar tsoka  daya a miya he's 22yrs akullum idan suka had'u sai tayi hiranshi.

   Matsowa tayi kusa da Dr. Halima da k'yar ta tashe ta suka koma cikin parlour ta zauna akan kujera, ruwa Divya ta tashi ta kawo mata  tasha sannan take maida musu abinda aka sanar da ita. Tana gama magana ta tashi da niyyar komawa gida,da k'yar ta yarda Abdoulmalik ya maidata gida tare da cewar gobe za'a maida mata motar ta.

    Yana dawowa gida direct sama ya nufa zuwa d'akin shi domin yasan Divya tana can, amma sai yaga wayam, rufo k'ofar yayi ya nufi d'akin ta gani yayi an kashe wutar d'akin  sai Dim light amma hakan bai hana bayyanar t'saruwar dakin ba da aka k'awata shi da komai fari, glass ne zagaye da bangon dakin iska tana kad'a curtains din balcony da ta manta bata rufe glass din gurin ba, farin chandler ne sak'ale a d'akin wanda ya k'ara k'ayatar da  d'akin.

     Shiga yayi da sallama yaji shiru, sai ya kunna lights, to  his surprise sai yaga Divya kwance ita da Zarah suna barci cikin kwanciyar hankali, sake baki yayi yana kallon su, matsowa yayi bakin gadon yace " Divya! Bude ido tayi ahankali suka sauka akan fuskar shi, Divya tun yanzu zaki fara nuna wariya ko?, baki tab'a kwanciya barci ba ba tare dani a kusa dake ba". Lumshe manyan idanuwanta tayi sannan ta saki murmushi mai k'ara mata kyau,  ta shag'wabe fuska   tace " tun yanzu har ka fara jealous akan Zarah ko? Tunda mukayi aure 9yrs kenan kullum tare muke kwana, amma dan yau zan kwana da baby darling d'ina shine kake b'ata face ?" Hade fuska yayi ya tsuke baki yace " yanzu bayan kin bata matsayin shimfid'a ta hakan bai isa ba harda sunana kike kiranta?" murmushin k'arfin hali tayi saboda barcin dake k'anta tace " Habiby barci nakeji fa please lets talk tomorrow morning kaji, ka kwanta a gefen baby Zarah" 

       "A gefen Zarah fa kika ce," " Uhmmm" tace mishi. Marairaicewa yayi yace "please my Queen ki dawo tsakiya sai ki saka Zarah agefe please why! Kinsan am already addicted to you i can't sleep well, taya kikeson inyi barci ba tare da kin kwantar da kanki akan kirji na b........ Ba  tareda ya k'arasa fadar abinda ke ranshi ba  dariya ta kubuce mata tana rufe bakin ta. "Dariya ma  kikemin Divya? Ba laifinki bane ki cigaba tashi yayi har yaje kofa sannan ya juyo yace "Toh zan samu atayani wanka?" Tausayi taji ya bata saboda basu saba hakan ba kuma tunda take bata tab'a kwana a dakin taba kullum sai dai agyara shi kamar sabo haka yake kullum.

    Duba Zarah tayi taga har yanzu barci takeyi ta shafa kanta ta k'ara rufe ta sannan ta kunna mata mp3 tasa mata karatun. yace "baki bani amsa ba" dariya tayi tace " how can i refuse my hubby" tahowa yayi inda take tsaya ya dauke ta in a bridal style ya kashe wutan d'akin ya rufe kofar .

      Bai ajiyeta a ko'ina ba sai kan gadon shi yana murmushi.......




    Dr. Halima tunda ta koma gida bata runtsa ba rokon Allah take,Allah yasa Abdoulfatah bai samu bad injuries ba, duk yanda bacci yake b'arawo baiyi gigin daukar ta ba yanda taga rana haka taga dare.

     Sai karfe 2am Abdoulmalik ya bar Divya ta dawo dakin ta dan baza tabar Zarah ta kwana ita kad'ai ba, saida ta fara barci sannan taji shigowar shi tace "Habiby yadai?" "Uhm nakasa barci ni kadai ne so shiyasa na dawo nan, a ina zan kwanta ? "  Tace "kwanta gefen Zarah" "please Divya"  "ok kwanta nan" cikin farin ciki ya kwanta.....

     Gari na wayewa around 7:30am  Dr. Halima  ta shirya akwatinta ta fito, d'aya daga cikin motocin gidan tasa driver ya d'auke ta zuwa gidan su Divya dukda tasan by this time suna barci. Shiga tayi cikin main parlour da sallama, masu aiki ne kawai suke aikin su Zama tayi tare da ciro wayarta dan kiran su.

    Divya tunda tayi sallah bata koma barci ba daukar iPad d'inta  tayi tana ma Zarah ordering kayan sawa masu tsada  da kayan wasa, kaya ba kad'an tayi ordering ba. Har ta gama ta mike sai ta tuno drama jiya dasu kayi akan Zarah, k'ara d'aukar  iPad din tayi sannan tayi mata ordering Charlotte crib grey colour(free mattress & pillow) which is 190k sannan tayi murmushi ta ajiye.

    Shiga tayi toilet tayi wanka ta shirya cikin maroon colour doguwar riga wanda yasha golden stones simple makeup tayi ta saka hula golden sannan ta sauka zuwa kitchen ta shirya musu breakfast : *SULTAN CHIPS, WINGS TANDORI CHICKEN, RICE & COCONUT PAP, CARROT & BEETROOT SMOTHIE*, bayan ta jera su akan dining ne ta koma daki ta tarar Zarah ta tashi amma tana kwance hakan yasa ta dauke ta tace " morning Habibty" dariya Zarah tayi kamar mai fahimtar magana, bandaki ta wuce da ita ta shiga mata wanka tana mata wak'ar:

     *this is the way i  take my bath ,take my bathx2 this is the way i take my bath early in the morning*.

    Tana gama mata wanka tayi mata brush. Wani daki naga sun shiga wanda aka k'awata shi da akayan alatu na morewar karamin yaro dakin Aqua blue ne da touches of baby pink wani wardrobe Divya ta bude wanda yake cike da kayan toddler children. Zab'o mata golden gown tayi mai hade da head band ta saka mata ta wuce shoerag ta dauko mata maroon daidai k'afarta kamar an g'wada  mata tana gama shirya ta ta hada mata oat ta bata ta shanye sannan taje ta tashi Abdoulmalik ya shiga wanka.

  Dr. Halima ta kafa wayar a kunne a lokacin da ta fara ringing har ta katse ba'a dauka ba lokacin da take kokarin dialing na biyu ne ta hango su suna sakkowa gwanin ban sha'awa Divya na rike da Zarah Abdoulmalik na rike da hannun Queen dinsa cikin fara'a da kwanciyar hankali suke sakkowa kana ganinsu kasan suna matuk'ar son junan su, ko lura da parlour basu yi ba suna kallon junan su har suka iso cikin parlour. Dr. Halima wacce tun suna sakkowa take kallon su cikin tsananin kauna tace "morning beautiful couples" d'ago kai sukayi atare suka kalleta tare da sakar mata murmushi.







BILKISU ARDO CE❤



❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum