RABI'ATU

696 27 0
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤


® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

Follow me on wattpad @ Billylosh1





*THIS AMAZING PAGE IS FOR YOU #FANS I KNOW YOU WILL LIKE IT MORETHAN ANY PAGE, THANKS FOR THE SUPPORT*
LUV YHU GUYS BOHOT BOHOT❤😜



   *AUNTY SIS💞*

   *ANEELURV YOUR PAGE THANKS FOR ZA SUPPORT*❤

1⃣6⃣➡1⃣8⃣


  

   Malam Habu kallon ta yayi yace " ashe lek'en asiri kika zo dole Hajiya ta ce kar abarki ki k'ara shigowa, murmushin k'arfin hali Dr. Halima tayi tace " malam Habu kenan ka kalle ni daky'au ka fad'amin dame nayi kama?"  Mamaki ne ya bayyana akan fuskar Malam Habu yace " toh Baiwar Allah har sunana kika sani? " 

    Ajiyar zuciya tayi tace "d'azu da nazo fita naji Rabi'a ta kiraka da sunan" ,
   "oh tohtoh yanzu naji batu amma da harna tsorata,toh amma meyasa kike son sanin wad'annan abubuwan? Ke da bai shafe ki ba" Ta nisa tace  "Dan Allah karka min wannan tambayar, ka taimaka ka fad'amin kuma wad'annan tambayoyin ni kuwa suka shafa " "toh ay baiwar Allah kinzo da babbar magana, amma babu komai abu na farko dai mijinta yau kimanin shekara 2yrs kenan baya k'asar nan, kuma babu wani d'an uwansa da suka tab'a zuwa, Zarah kuma ita kadai ce y'arta kuma maigidan bayanan lokacin data haife ta kuma baizo ba.

    Kuma iya kacin zamana agidan nan babu wanda ya tab'a zuwa gidannan sai wata mata da zatakai kimanin shekaru 50 naji Hajiya tana ce mata Inna kuma a k'auyen *NAMORA*take".

     "Shikenan abunda nasani akan gidan nan". Gwauron numfashi ya ja sannan yace " kuma abinda yasa na fad'a miki shine nakusa barin gidan saboda babu albashi ga iyali kuma mai gidan bai tab'a zuwa ba tunda ya tafi" ajiyar zuciya tayi na tausayin Zarah daya k'aru a cikin zuciyarta tace " ko zan samu address din gidan innar tata a can k'auyen?" Wallahi babu amma yanzun nan Hajiya ta ayka mota guda na kayan abinci akai ma innar ta, yanzun nan wlh"  cikin zumud'i tace " ko zan samu number driver?",  shiru yayi  sannan yace "ina zuwa bari na kirashi dan inada number sa" , " cikin jin dadi tace "nagode".

   Shiga cikin d'akinsa yayi ya ciro wayarsa ya fito sannan ya kara wayar akunne sa yace " Assalamu Alaikum gambo kayi nisa ne?" Daga d'ayan b'angare naji yace " a'a wallahi Habu ganinan motar tayi faci" murmushi Dr. Halima tayi dayake tanajin abunda suke fad'a sannan tace " ka tambaye shi yana hanyar ina? Sai naje mu had'u "  malam Habu ya cigaba da cewa "Dama bak'uwar Hajiya ce takeson zuwa can gurin innar shiyasa Hajiya tace in kiraka in fad'a maka saboda ku tafi tare"(yayi masa k'arya dan yasan in ba haka ba bazai yarda ba), "toh ba matsala, ina titin *kwantiya* wajen masu gyaran motoci" "toh shikenan " nan ya katse wayar ya juyo ya kalleta tare da sanar da ita inda zata sameshi godiya tayi tare da bud'e *TOMMY GURL*bag d'inta ta ciro wrapper na 500 ta mik'a mishi kallon ta yayi tare da k'arb'a yana gode mata yace "rabon dana rik'e kud'i masu yawan wannan tun kafin Alhaji yayi tafiya"  "bakomai malam Habu nagode sosai"  "nima nagode Hajiya".

    Shiga motar ta tayi ta sameshi a titin *kwantiya* wurin masu gyaran mota dama ita yake jira tana zuwa suka wuce tana binsa a baya har k'auyen *NAMORA*


      Suna tsayawa, Gambo ya kirawo yaran unguwa suka tayashi shigar da kayan amma Dr. Halima ko fitowa batayi a mota ba har aka gama shigar da  kayan da suka cika tsakar gidan sannan Inna ta basu kyautar dubu daya, Gambo shirun da yaga Dr. Halima bata fito ba shiyasa ya tinkaro motar, tana ganinshi ya nufota tayi saurin fitowa tace " toh nagode Allah ya tsare hanya tare da mik'a masa dubu biyar 5k sannan ta wuce zuwa cikin gidan.

     Sallama tayi inna ta amsa mata sannan ta shiga cikin gidan. Taburma ta shimfid'a mata ta zauna ta kawo mata ruwa a kw'anon  samera sannan ta zauna jiki na b'ari taga mai kud'i, gaisawa sukayi sanann Inna tace " Ban gane ki ba baiwar Allah".

  Dr. Halima da ta rasa me zatace mata  tayi shiru sannan tace  " sunana  Fa'iza daga hukumar kula da iyali nake" (ta mata k'arya domin tasamu amsoshin da take buk'ata),  inna tace " tototo nagane dama harda wata hukumar kula da iyali kenan? Toh ina sauraronki" Dr. Halima tayi gyaran murya sannan tace "akan Rabi'atu ne" gaban ta ne ya fad'i amma sai ta dake tace " mey y'ata tayi miki kuma?"  "Kwantar da hankalinki Inna,inason in miki wasu 'yan  tambayoyi ne"  "toh ina sauraron ki" Dr. Halima ta gyara zama tace shin Rabi'atu ita ta haifi Zarah?" Inna da ta gano inda maganar ta dosa tace ni y'ata Rabi'a bata taba haihuwa  ba kuma bansan wata Zarah ba saidai kwanaki da naje na dubota take bani labarin cewa ta tsinci wata 'ya a hanya ba lafia ta kaita asibiti,kinsan Rabi'a akwai son yara ga tausayi" Dr. Halima da ta kura mata ido taga sai zufa take irin na marasa gaskiya tace "toh Inna ba matsala ni zan koma" bawai dan ta yarda da kalaman Innar ba tace" sai anjima"  "toh Malama Fa'iza sai anjima" tashi tayi ta nufi harya fita har k'ofar gida ta raka ta sannan ta juyo, tana isa mota sai ta tuna da mukullin motar ta akan taburma nan ta juya domin ta dauko.

    Tana shiga taji Inna tana waya       

     "kina jina Rabi'a karki kuskura ki yarda Zarah ta dawo gurin ki kuma ki cigaba da abinda nake koyarda ke  kinsan dai baki da kamata kaf duniyar nan dan yanzu wata tazomin gida" tare da bata labarin yanda sukayi da Dr. Halima, ta dora da cewa " idan aka tursasa sai kin karbeta toh ki karbeta zan kawo miki magani gobe da zataci ta mutu kinsan dai mai nake nufi ko toh", Dr. Halima da ta daskare a tsaye ta rasa mai za tace,  kafin Inna ta juyo da sauri Dr. Halima ta tare ta da sallama abunka da mara gaskiya da sauri ta cire wayar daga kunnenta ta boye a bayanta.

   Dr. Halima tace "kinga mukullin motar ashe anan na barshi" inna ta duburburce tace " Amma yanzu kika shigo dai ko?" " Eh " tace mata kawai tare da daukar keys dinta ta fita cike da tsanar Rabi'a da mahaifiyar ta,  driving take amma zuciyar ta na k'una sauka tayi daga kan titi tayi parking tare da kifa kanta akan sitiyerin motar saboda yanda takejin zafi acikin ranta.

  Phone d'inta ne ya fara ringing takai idonta kai sunan "Abdoulmalik" ta gani hakan ya tabbatar mata da cewa akwai matsala d'agawa tayi cikin sanyi murya nan Abdoulmalik yake shaida mata cewa tunda suka baro asibiti Divya ba lafia, cikin karfin halin tace  ganinan zuwa.
    Tada motar tayi sannan ta hau titi 40min ya kaita har kofar AKTH shiga tayi ba tare da ta d'ad'e ba ta fito rike da wasu files ta shiga mota ta wuce gidanta ta shiga direct d'akinta ta fad'a toilet tayi wanka ta d'auro Alwala ta tada sallar magrib da ya wuce ta ta d'aura da isha'i tayi addu'oin ta as usual sannan ta shirya ta sauka k'asa saboda rashin ganin Zarah, a goye ta ganta a bayan baba delu , tace"har ta tashi kenan baba?" "ay wlh hajiya tayi barci sosae, kuma tana tashi na bata abinci shine na goyata"  karb'ar ta tayi sannan ta fice zuwa gidan su Divya.

  Tana parking ta dauki Zarah tare da files din data dauko a asibiti sannan ta shiga cikin gidan.

   Masu aiki ne suka yi musu iso har cikin,parlour sannan  ta d'auki waya ta kira Abdoulmalik ta sanar dashi ta shigo gidan,ba'a d'auki wasu mintoci ba sai gasu sun  fito rik'e  da hannun juna har suka iso cikin parlour , ganin Divya yasa Zarah ta rink'a mik'a hannun tana cewa ma.. amaa.. ah acikin gw'arancin ta, da sauri Divya ta k'arasa kusa da ita ta d'auke ta tana mata dariya. Mamaki Abdoulmalik yayi ganin yanda Divya ta ware sai wasa takewa Zarah suna ta dariya, Dr. Halima ce tayi gyaran murya tace ku zauna zamuyi magana.

   Zama sukayi tareda tattara hankulan su guri d'aya, files din ta d'auko tare da  mik'awa Divya tace "you have to sign this papers" kallonta Divya ta tsaya yi tace " ok" ita a tunanin ta akan matsalar tace takoyi signing sannan Dr. Halima tace "as  from today Zarah  is your daughter, yeah Zarah Abdoulmalik".

  Abdoulmalik da ya zama d'an kallo yace "Dr. Halima i don't understand?" Divya kuwa mik'ewa tayi tsaye tace "do you really mean what you said? ".............





BILKISU ARDO CE❤



❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now